Sashe 252
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
bin sa a baya yace "Pls Dr allow me to see her even if it's just for a minute, she is my sister, i am also a Medical Doctor...." Sai da ya fadi shi ma Medical Dr ne Dr Balogun dake tafiya ya juya ya kallesa ba tare da ya tsaya ba yace "A Medical Doctor?" Da sauri Maheer ya ciro ID card dinsa ya nuna masa yace "Yeah i am also a Dr Sir, here is my Identity card and place of work" Dr Balogun ya amshi ID card din nasa, ganin asibitin da yake aiki da field dinsa as a Medical Doctor ya tsaya yana kallonsa yace "Ohh really" Mayar masa da ID din yayi yace "Alright Dr, let me talk to our MD, yana cikin ICU din... I pray he allows u in" Maheer yace "I will appreciate that plss sir" Dr Balogun ya juya ya koma IC unit din ya shiga, MD na tsaye gaban Breathing machine din yana kallonsa monitoring each and every alarm it's making baya ko kiftawa as if his own life depends on that too, bai taɓa ba Machine din nan Value irin yau ba a kaf shekarunsa na aikin likitanci, juyawa yayi yana kallon Dr Balogun da ya shigo ICU din, Dr Balogun ya karasa gun sa da ladabi yace "Sir, dama akwai wani yayanta ne ke son a bashi izinin shigowa ya ganta, he is also a Medical Doctor a nan Abuja, a Surgeon" MD dake ta kallon Balogun ya dauke kai kawai don shi ko magana ma baya so, sai ga Dr Khalil ya shigo Unit din shi ma ya nufo MD, ya ɗan sauke nosemask dinsa yace "Sir, akwai yayanta shi ma likita ne, pls in ka bada Permission zai shigo ya ganta ya fita immediately...." Juyawa Dr Balogun yayi ya fita, a hankali MD yace "Meye amfanin shigowan Khalil? As u can see ba wani improvement for now, i think it's not necessary..." Yana fadin haka ya koma ya zauna don wani mugun ciwo kansa yake, Dr Khalil yayi kasa da murya yace "But MD ko yaya ne a bar ko mutum daya a yan uwanta su shigo, barin shi da yake likita, saboda rashin barin mahaifiyarta ta shigo yasa tayi collapsing dazu a reception jininta ya hau yanzu haka she is being admitted also, Abbanta ma ba a bashi daman shigowa ba he is so disturbed, don't forget MD Mayraah is between life and death...." MD ya katse sa da sauri ya mike yace "I don't understand?" Dr Khalil ya kwantar da murya da damuwa yace "We shouldn't deceive our self sir, But that is the reality don haka ka bar yayanta ya shigo since he is also our Colleague, bamu san me zai faru ba" Bai jira cewar MD da ya bi sa da kallo zuciyarsa na bugawa ba har ya fita, MD ya juya da sauri ya kalli Ventilator machine din da yayi making wani alarm, ya karasa kusa da Mayraah that is attached to medical devices and tubing ya duka da sauri, Gown Dr Khalil ya ba Maheer da nose mask with gloves sai takalman da zai shiga ciki da su, tun da ya shigo MD ke kallonsa, Maheer na tafiya a hankali ya karasa gun Mayraah ya kamo hannunta ya duka with breaky voice yace "Mimi, pls wake up Mimi...." MD dai kallonsa kawai yake, Maheer ya hade kansa da gadon yana rike da hannunta gam, MD could see the tears coming down from his eyes, sunkuyar da kai shi ma yayi, Kusan a tare MD da Maheer suka dago kai as a result of alarm din da machine din yayi, Maheer ya mike tsaye da sauri looking at the machine zuciyarsa na bugawa yace "Her pressure is dropping" Bayan sun yi kokarin saita BP din nata by administering her with vasopressin, MD ya kalli Maheer zai yi magana sai ga Ceo ta shigo ICU din, karara zaka ga tashin hankalin dake fuskarta direct ta nufi inda Mayraah take, Wani Dr Ba indiye da bature suka shigo ICU din su ma with another Dr duk suka yi kan Mayraah, Maheer ya sauke idonsa kasa a hankali ya juya ya fita daga IC unit din. Maheer na isa reception din asibitin sai ga Usman ya shigo da Aunty Mariya sai Hajja dake biye da su a baya, Aunty Mariya ta fashe da matsanancin kuka ta nufi Maheer da sauri ta kamo hannunsa tace "Maheer ta farfado ko tana ICU din har yanzu?" Maheer ya kasa ce mata komai, hakan yasa Hajja ma ta fashe da kuka, Usman ya nemi kujera a reception din ya zauna ya dafe kansa, juyawa Maheer yayi walking slowly ya tafi can far end of the reception ya zauna ya jinginar da kansa ya runtse ido zuciyarsa na bugawa da karfi, he just can't imagine loosing Mimi, kuka Aunty Mariya take kamar ranta zai fita Hajja na taya ta, bayan wani lokaci Hajja ta mike tana share idonta ta nufi Maheer tace "Ina Ammin take?" Maheer ya sauke idonsa yace "An kwantar da ita, ta samu bacci" Hajja ta zauna tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah ga mu gare ka, Allah ka tashi kafadun wannan baiwar taka" Suna ta zaune a reception din for almost 3 hours babu me cewa kowa komai, kowa kuma da tunanin dake ransa, Maheer ya ciro wayarsa dake ta vibrate tun dazu ya ki duba me kiran, don duk hankalinsa na kan wanda zai ga ya fito daga hanyar ICU amma shiru shiru har yanzu daga Ceo din har likitocin da suka zo, kallon screen din wayar yayi yaga number Mama Ladi, ya daga ya kai kunne yayi shiru, daga daya bangaren cikin daga murya Mama Ladi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, Maheer ga ni a garin Habuja tun dazu ban san inda zan je ba ina ta yawo a tasha" a hankali Maheer yace "Ki nemi me adaidaita sahu sai in gaya masa asibitin" Da sauri Mama Ladi tace "Tohh to" Katse wayar yayi ya ajiye gefensa ya dafe kansa, ba a dau lokaci ba sai ga kiran Mama Ladi Maheer ya gaya ma mai adaidaita sahun asibiti wanda sananne ne sosai, sannan ya katse wayar ya mayar aljihunsa ya mike tsaye, ya tafi can bakin ICU din ya zauna yana kallon kofar... Wani likita ne a ICU yayi saurin riko MD da yayi baya zai fadi, duk sauran likitocin suka juya kallonsa, Ceo tace "Ka je ka huta Aliyu, get some rest, by the grace of God we have hope" Da sauri yace "No Ma'am i am fine...." Dr Hamid ya dafa sa yace "You need rest MD, kuma baka samu ka ci komai ba and this is pass 12...." Bai jira cewarsa ba ya kama hannunsa za su fita daga ICU din MD da kansa ke juya masa bin sa kawai yake, sai da suka isa kofa ya sake juyawa ya kalli Mayraah da Toxicologist din ke bakin kokarinsu a kanta, suna fitowa daga Unit din Maheer ya mike da sauri yana kallonsu.