Sashe 135
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake.* [7/11, 8:55 PM] Khaleesat Haiydar💖: Hajiya Amina ta karasa cikin parlon ganin Mama Ladi sai bata zauna kan kujera ba ta zauna kasan carpet tana kallonta cikin ladabi tace "Ina kwana Mama" Mama Ladi dake ta kallonta daga sama har kasa ta kalli Aunty Mariya dake zaune kan kujera fuskarta babu yabo babu fallasa tana danna waya tace "Wacece wannan kuma kika bude ma kofa ta shigo mana Mariya?" Hajiya Amina ta ɗan yi murmushi tace "Sunana Amina Mama" Mama Ladi ta yamutsa fuska tace "Amina? Meye kuma Amina? Amina daga ina? Ko dai batan hanya kika yi? To ko dai korar Salibar aka yi aka canzo wata mai aikin Mariya?" Hajiya Amina ta kalli Aunty Mariya dake ta harkarta da waya tace "Ina kwanan mu" Sai a sannan Aunty Mariya ta dago kai a takaice tace "Lafiya lau" Mama Ladi tace "Kin san ta ne Mariya ta shigo mana kanta tsaye ko dai makota zata shiga tayi ɓatan kai? Ko Saliba aka canza" Aunty Mariya tayi pretending kamar an kirata a waya ta mike ta shige daki ta kulle kofar, dai dai nan aka Bude kofar parlon Usman ya shigo da sallama ya karaso ya zauna kan kujera yana kallon Hajiya Amina yace "Ina kwana" Hajiya Amina ta kallesa tace "Lafiya lau barrister" Daga haka ta kalli Mama Ladi dake ta kallonta daga sama har kasa kamar taga abun kyama ta mike tace "Mama bari in baku waje..." Daga haka ta nufi kofa ba tare da ta jira cewar Mama Ladi ba ta fita, Usman na kallon Mama Ladi da ta bi Hajiya Amina da kallo baki bude yace "Ina kwana Mama?" Mama Ladi ta dawo da kallonta kansa, sai kuma ta saki kuka ta rike kai tace "Yanzu Usman kai da nake ganin hankalinka ace har da kai a zuba ido ubanka ya dankara ma uwarka kishiya baka taka masa burki ba? Me zai yi da wata matar gashi da gandara gandaran samari a gida banda son rai da son zuciya irin nasa? Shekara kusan arba'in yana tare da uwarku bai mata kishiya ba sai yanzu kuma kuka yarda da hakan baku tada masa bori ba? Kuma don Allah a ina ya jajibo wannan mata haka sai uban mazaunai? Sannan saboda raini da duniyanci shegiyar sai ta biyo mu har nan daga shigowarmu ko minti daya ba mu yi ba? Ina ruwanmu da ita zata shigo nan idan ba munafurci ba? Ta ina Ammi zata fara kishi da wannan mata haka kamar karuwa, ko kai baka ga yanda take wani juye juye bane?" Usman dai ya mike zai fita Mama Ladi ta tashi da sauri tace mu je ka kira min uban naka, kace Mama Ladi daga karaye na sallama da shi. Duk yanda Aunty Mariya ta dinga kokarin kwantar ma da Ammi hankali tana bata baki Ammi bata saurareta ba don kamar dada tunzurata ma take, sai harhada komai na dakinta take waje daya tana kuka, daga karshe ma ce ma Aunty Mariyar tayi in ta sake mata wata magana zata mareta, hakan yasa Aunty Mariya ta ja gefe ta rasa kuma yanda zata yi ta tsaya duk jikinta a sanyaye, seriously Ammi ke hada sauran kayanta tana goge hawayen dake sauko mata. Mama Ladi na zaune parlon baki sai girgiza kafa take tana jiran taga ta inda Abba zai billo bayan ta aika Usman ya kira mata shi, bayan some minutes sai gashi ya iso chalet din ya shiga parlon da sallama ya zauna saman carpet ya gaisheta da ladabi, Mama Ladi ta fashe da kuka ta rike kai tace "Yanzu kai Mamuda shekaranku 40 da Ammi ba a taɓa jin kanku ba, ba a taɓa sulhunta ku balle a raba ku fada ba sai don wannan ɗan matsalar ya gitta tsakaninku sai ka mata sakayya da kishiya? kishiyar ma kamar daga Tafa ka aurota, Mamuda ka mance yanda Ammi ta zauna da kai kana matsiyacinka cin yau da kyar na gobe daban tsabar talauci, baka da ko kwandalan kanka alhalin masu kudi ne suka dinga sonta da aure taki amince masu ta makale maka kamar me bakin uwa? Ko dai ka mance yanda ta dinga kwana da yunwa ta yini da yunwa duk bamu sani ba tana ta rufa maka asiri a haka har ta haifa maka yaran nan cikin baƙar yunwa? Shine yanzu zaka saka mata da wannan tozarcin Mamuda?" Abba dake sauraronta yana kallon TV, ya ɗan yi murmushi ya girgiza kai yace "Baaba ban kara aure don in tozarta ta ba, na karo aure ne saboda babu yanda zan yi hakan shine kadai mafita a gareni da yarana, baaba a duk abubuwan nan da suka faru in za ayi alkalanci tsakani da Allah ke kanki kinsan na kauda kai nayi hakuri na kuma nuna komai ba komai bane...." Mama Ladi ta share hawayenta tace "Sarai nasan wannan, don juya ka suka dinga yi kamar sun samu waina, su ce wannan su ce wancan kuma kana ta bin su babu musu har na so inji haushinka wallahi" Abba yace "Yauwa baaba, na bi su yanda suke so a lokacin nan don a zauna lafiya, duk yanda suka ce haka ake yi, a tsarinsu na karshe ne naga bazan iya ci gaba da goyon bayan zalunci ba, na kuma nuna ma ita Ammin bazan yarda da haka ba shine ta debi kayanta ba fada ba komai ta bar gidan nan, baaba fisabilillah akwai wanda Mayraah ta sani a duk duniyar nan bayan mu?" Mama Ladi ta gyara zama tace "Ina fa?? Yarinyar da ku kanku baku san asalinta ba balle ita da sai kwanan nan ma tasan ba ku ne iyayenta ba" Abba yace "Kinga da farko Ammi ta nuna Hajja tace bazata sake rikon Mayraah ba, na danne zuciyata na nuna ba komai tayi ma mahaifiyarta biyayya kawai, nace Mayraah ta koma gidan kanina wato ɗan yayan mahaifina shi ma iyalansa suna nan garin kano shine dai yake legas, Maheer ya nuna gidan yayi nisa daga makarantar ta sai dai ta zauna gidansa kawai, duk aka amince saboda dai Ammi ta samu kwanciyar hankali gun mahaifiyarta, wannan duk bai isa ba sai gashi sun billo da wata maganar wai bazata zauna gidan Maheer ba sannan nan din ma Ammin bazata riketa saboda son zuciya irin nasu da rashin binkicen asalin abinda ke faruwa, ina ake son yarinyar ta tafi fisabilillah ga jarabawarta na karshe zata zana? ban da ni me hakuri ne wa za ayi ma haka a zauna lafiya Baaba? Yarinyar da tun tana jaririyarta ake tare da ita yanzu da girmanta a billo mata da haka don ma tana da strong mind? Ina ake son in kai ta to?" Mama Ladi tayi kasa da murya tace "Ka ma yi kokari wallahi Mamuda don ba ko wani namiji bane zai dauki wannan iskancin ba zancen gaskiya, kuma Allah ya maka albarka yanda ka dinga bin duk abinda suka ce da farko kana ta kauda kai...." Abba yace "Auren nan kuma da nayi, nayi sa ne kawai saboda babu yanda zan yi, Baaba kema kinsan babu ta yanda za ayi kana tare da mace babu zagi ba cin mutunci ta tattara kayanta ta koma gidansu kuma mahaifiyarta na kallonta amma tayi shiru ta barta ta ci gaba da zama bata saka ta koma gidanta ba" Mama Ladi tace "Ita fa Hajja ka rufa ma kanka asiri ka daina sa ta a sabgar nan, don wllhi gobe ma nake son mu kai ta asibiti a duba mana kwakwalwarta don tsufan duk ya rikirkitar da ita abun dai ba kyau" Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Na ƙaro aure ne saboda bazai yiwu ace Mayraah na gidan nan babu babban mace dake saka mata ido ba, sannan yayyinta duk ba gidan suke ba a ko da yaushe, in ma suna gidan to yanzu duk sun san su ba muharraman juna bane.... Kin ga ai abinda zai yiwu shi ake yi" Mama Ladi tace "Kul, kar ka sake cewa ka karo aure saboda Mayraah ka kara goga mata baƙin fenti a shiga uku, me ya kai ka fadan haka? kai dai kawai kace ka karo aurenka saboda baza ka iya zama babu mace ba, kai ni ban ma yarda cewar saboda wannan ɗan matsalar ka tashi kaje kayi wannañ gantalallen auren ba Mamuda, dama can kana da bazawararka a boye kuna tadinku, kar ka raina min hankali kawai" Abba yayi murmushi yace "Ko daya, hada ni aka yi da ita ma" Mama Ladi tayi mitsi mitsi da ido tace "To Allah ya tsine ma koma wanene ya hadaka da ita" Shi dai Abba bai ce komai ba, Mama Ladi tace "Kuma yanzu ka tashi mu koma can bangaren Ammi da bakinka ka gaya mata ka kara aure, don babu rashin mutunci ace namiji ya dankara ma mace kishiya babu saninta, ko mata dari zaka aura baka da sama da Ammi kaji in gaya maka, maza tashi mu je ka bata hakuri sannan kasan inda zaka kai kishiyar don baza su zauna gida daya ba suna gogan kafada da katuwar matar da ka auro, ai na ganta wata sandan sandan kamar er Ghana" Abba dai kallonta kawai yake, ta mike tana gyara yafin gyalenta tace "Ka tashi mu tafi nace ko" Ya ɗan yi murmushi don bai son yi mata musu amma ba don yayi niyyar hakan ba ya mike ya bi bayanta suka koma main house zuwa bangaren Ammi, Mama Ladi ta bude kofar taga akwatunan Ammi an sake fito da su parlon, Mama Ladi ta rike haɓa tace "Ji shashasha...." Abba dai ya nemi kujera ya zauna babu yabo babu fallasa, Aunty Mariya ta leko daga dakin jin muryar Mama Ladi tana ganin Abba ta hade rai ta koma cikin dakin Ammi, Mama Ladi ta shiga dakin tana kallon Ammi dake kulle last box dinta tace "Fito fito, hada akwatuna ba