← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 192 OF 313

Sashe 192

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cewa "Daga wannan tarin fa wani ake zare ran, wallahi ba ruwana Badiyyah ta zo ta tafi kar in rasa yayata" kwance Mama Ladi ta tarar da Badiyyah shame shame a kasa kamar mara galihu, ko bin ta kanta bata yi ba tana toshe hanci ta bude inda kayanta suke ta dinga kwaso su tana zubawa cikin akwatin da ta bude, Badiyyah sai bin ta take da ido tana sauke numfashi a hankali, tun shekaranjiya babu me bi ta kanta a gidan sai Ammi dake ajiye mata kunu a bakin kofar dakinta tayi tafiyarta, ji take kamar mutuwa kawai zata yi, komai ya dena mata dadi a rayuwar, Mama Ladi na gama cusa kayan cikin akwati tana kallonta tace "Tashi ki fita a samar maki adaidaita sahu ki tafi can gun dangin ubanki su yi jinya, mu ba yan iska bane duk ta sunna aka same mu, don haka baza mu yi jinyan cikin shege ba Allah ya tambayemu" Badiyyah ta mike zaune da kyar tashin hankali karara a kan jemammen fuskarta tace "Mama Ladi wallahi basa so na, ko a baya ba jin dadin zaman can garin nake ba don Allah ki rufa min asiri Mama Ladi" Mama Ladi bata sake sauraronta ba ta fito parlor da akwatinta, Ammi na tsaye tana kallon Hajja dake kuka hade da tari ta dage a fitar mata da Badiyyah daga gidan, Mama Ladi tace "To ni dai bani da karfin dagota Ammi ki je ki fito da ita ga akwatin nata na fito da shi, ko shatar adaidaita sahu ne sai a dauko mu biyasa ya kai ta har Bichi" Sai ga Badiyyah ta shigo parlon da rarrafe ta fashe da kuka tace "Don girman Allah Hajja ki ce ma Mama Ladi a bar ni nan bazan iya zaman Bichi ba basa sona ke ma kin sani" Wani rikicewa Hajja tayi ganin Badiyyah ta dinga tari da karfi tana nuna alamar a fitar mata da ita, Dole haka Ammi ta fita da Badiyyah compound don Hajja ta dena ganinta, Mama Ladi ta dauki akwatin Badiyyah ta bi su da shi, Badiyyah ta rike kafar Ammi tana kuka sosai tace "Don Allah Ammi kema kinsan bani da inda zan je, basa sona a Bichi, don Allah ku yi min rai Ammi" Ammi dai na tsaye ta kasa cewa komai, Mama Ladi na ajiye masu akwatin ta koma gun er uwarta Hajja tace "An fitar da ita yanzu za a daura ta a mota ya kai ta Bichin don Allah ki kwantar da hankalinki yaya" Hajja dake ta sauke numfashi da kyar Aunty Mariya na durkushe gabanta ta rike hannayenta biyu, cikin sarkewar murya tace "Mariya ki kai ni wajen yahanasu kawai" Aunty Mariya ta kwantar da murya tace "Hajja yamma yayi mu kama hanyar kaduna yanzu, ki yi hakuri gobe da sassafe sai mu tafi in Allah ya yarda" Mama Ladi ta zauna gefenta tace "Tafiyar yamma babu dadi yaya, gobe da asuba har ni sai mu je Kadunan in hankalinki zai kwanta da haka, idan ya so idan nayi kwana biyu sai in bar ki tare da yahanasun ni in dawo" Kai kawai Hajja ke gyada masu tana sauke numfashi, Ammi dai an bar ta tsaye da Badiyyah da akwatinta a tsakar gida ta rasa yanda zata yi, Aunty Mariya ta kira da wayarta dake hannunta, ba a dau lokaci ba Aunty Mariya ta fito tsakar gidan, ko kallon Badiyyah dake kwance ƙasan compound din tana rusa kuka bata yi ba ta karasa gun Ammi da ta koma gefe tana jiranta, Ammi na kallon Aunty Mariya cike da damuwa tace "Yanzu ya za mu yi Mariya?" Aunty Mariya tace "Ya za mu yi me Ammi?" Ammi tace "To ina za a kai yarinyar nan yanzu?" A takaice Aunty Mariya tace "Aa, ba dangin ubanta na Bichi ba, ko kin manta ne Ammi" nan da nan hawaye ya cika idon Ammi tace "Kar ki manta Mariya yau ace Rukayya na da rai...." Kasa ci gaba tayi saboda kukan da ya taho mata, Aunty Mariya dai tayi shiru nan da nan ita ma hawaye ya cika idonta, cikin rawan murya Ammi tace "Hannunka baya rubewa ka yanke ka yar, ko mun ki ko mun so Badiyyah ta mu ce, er uwar mu ta jini ce ta haifeta gashi bata doron kasa yau ga halin da er ta ke ciki, kuma Allah ya gani mun yi bakin kokarinmu kan Badiyyah, i tried my best Mariya, my children tried their best also, ke za a ce ba a garin kike ba, Amma Allah yasan kokarin da nayi kan Badiyyah" kasa ci gaba Ammi tayi, Aunty Mariya ta goge hawayen idonta tace "Yanzu ya za mu yi yaya?" Ammi na hawaye tace "Wallahi ban sani ba, kin ga tace bata son ganinta ni kuma yanzu ba ɗa bane a gidana, i don't have that power anymore, ban san ko Mahmud zai amince Badiyyah ta koma can ba" Aunty Mariya ta sauke ajiyar zuciya tace "Ni kuma kin san family house nake, bazan dau Badiyyah da ciki in fara kai ta gidana ba ya zame min abun gori gun facalolina da dangin mijina" Ammi na gyada kai tace "Haka ne, kawai yanzu daukarta zan yi mu tafi gida sai in ga yanda za mu yi da Mamuda" Aunty Mariya tayi kasa da murya tace "In har ya nuna bai amince ba ko jayayya kar kiyi da shi Ammi, ki nemi izini kawai ki kai ta Bichi gobe, nima goben za mu tafi da Hajja kadunan tunda tace baxata zauna nan ba, ga Mama Ladi tace za ta bi mu" Ammi tace "Toh shikenan" Aunty Mariya ce ta fita ta samo masu adaidaita sahu, aka saka akwatin Badiyyah a ciki, Ammi ta daure fuska tana kallon Badiyyah dake kwance a kasa tace "Tashi ki fita" Da rarrafe Badiyyah ta karasa gate din ta lallaba ta shiga adaidaita sahun, Aunty Mariya tayi ma Ammi sallama tana tsaye har adaidaita sahun ya juya ya bar layin sannan ta koma cikin gida. Ammi na isa gida dab da magrib ta sauka ta ba me adaidaita sahun kudinsa sannan ta sauko da akwatin Badiyyah ba tare da ta bi ta kanta ba ta shiga cikin gidan, Badiyyah ta sauko da kyar tana biye da ita a baya tana maida numfashi, Ammi taga motar Abba a garage alamar yana nan, Haseenah ce ta fito daga Chalet sanye da Hijab bayan ta leko compound jin an bude gate taga Ammi ce, ta sauka kasa ta karasa gun Ammi tace "Ammi sannu da zuwa" Ko kallonta Ammi bata yi ba tace "Sannu" Zata amshi akwatin hannun Ammi, Ammi ta ki sake mata tace ta bar shi kawai, tun shekaranjiya Haseenah ke gidan bayan an sallameta daga asibiti kamar yanda Abba ya umarce Maheer ya kawo ta gidan don tana ma gidan Badiyyah tayi wannan tonan sililin a parlon Hajja, kamar ance Haseenah ta juya taga Badiyyah ta shigo compound wujiga wujiga duk ta rame tayi baki, nan da nan Haseenah ta hade rai ta kauda kai, Badiyyah dake fama da kanta ko bin ta kan Haseenah bata yi ba ta shige cikin gidan da sauri don kwanciya kawai take son yi ga amai da ke taso mata, Haseenah ta ɗan yi jim, sai kuma ta bi bayansu zuwa main building din gidan ita ma, a parlor ta tadda Badiyyah ta kwanta, Ammi kuma ta haura sama, Lokaci daya ta ga Badiyyah ta mike da gudu ta shige bandakin dake parlor tana kakarin amai, bude baki Haseenah tayi da mamaki bayan ta bi ta da kallo, a hankali tace "Amai kuma??" Can dai ta juya da sauri ta fita daga parlon ta koma Chalet din da take. Ammi tayi shiru tana kallon Abba a sanyaye don maganganu kawai yake cikin fada inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, har ya kai aya, can ta sauke kanta kasa cike da karfin hali tace "Shikenan Yallabai kayi hakuri... kayi hakuri, goben sai in kai ta Bichi idan Allah ya kai mu" A takaice Abba yace "Da dai ya fi don bazata zauna a gidana ba i stand my words" Daga haka ya mike ya shige Bedroom dinsa Ammi ta bi sa da kallo wasu hawaye na sauka idonta, duk ya canza kamar ba shi ba, Abba da ko ɗaga mata murya baya yi idan yana mata magana a baya, abu ko bai masa ba idan tace haka take so to haka nan zai yi don baya son bacin ranta kwata kwata amma yanzu duk babu wannan, duk hakan na neman zama tarihi daga yan watannin nan da suka shude, he is now a changed person, tunanin hakan ya kara breaking heart dinta sosai, ta mike ta fita daga parlonsa ta koma bangarenta ta ci kukanta ta gode Allah..... Mayraah na kwance dakinta bayan isha Karime ta shigo da sallama tace "Hajiya Ilham ga can kwan na soya maki a kitchen sai ki yanki bredin da zai isheki ki debi ruwan shayi a flask ki bar ma yallabai sauran, ni zan shiga gidan makociyarmu in duba jikin er ta ta kone a kafa, to duk yau ban shiga ba" Mayraah ta gyada mata kai tace "In zan ci zan je in dauka" Karime tace "Toh sai na dawo" Mayraah ta bi ta da kallo sae kuma tace "Amma ba dadewa za ki yi ba ko?" Karime ta juyo tace "Toh akwai dae wani pim din hausa da ake yi duk ranan juma'a, wani lokacin in Ummi ta shiga ta kwanta da wuri na kan je gidan in kalla, kinsan duk an rufe tashoshin gidan nan saboda yan biyun nan maxa da yarinyar nan Mimi da basu son maida hankali su yi karatu sai kallo, to yallabai duk ya rufe tasoshin ba a kallon finafinai a gidan nan, ke baki ga tun da kika zo sae dai ki ga an kamo tashan labarai ba" Mayraah tace "Yanzu dai kallo za ki je yi kenan" Karime ta kyalkyale da dariya tace "Baxan boye maki ba shi zan je inyi gaskiya, karfe goma ake gama pim din, ana gamawa zan dawo in sha Allah" Mayraah tace "Toh... Shikenan, sai kin dawo" Karime tace "Toh kar dai ki bar kwan ya sandare"
Chapter 192 · 0% Book details