← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 228 OF 313

Sashe 228

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ja Ammi da zance, su ne har kusan karfe shidda a gidan, Ummi ma tuni ta shigo dakin Inna ta zauna suna hiran gaba daya, magana daya biyu sai innan ta Gwale Ummi, Ummi dai ko bin ta kanta bata yi, a haka dai Ammi ta samu suka lallaba suka bar gidan inna na cewa tana nan zuwa zata sa Khalil ya kai ta, bayan sun kama hanya Mayraah na kallon Ammi tace "Kamar Mama Ladi ko Ammi" Dariya Ammi tayi tace "Wannan ai ta so ta fi mama Ladi, gaskiya Ummin na hakuri da ita..." Mayraah tace "Ai kam Ummi ba ruwanta bata biyeta" Washegari ko da Mayraah taje aiki su Khalil basu dawo Lagos ba wai sai Tuesday, hankalinta kwance tayi aikinta a asibitin babu wanda ya takura ta, a ranta ta dinga fatan da ma kar su dawo da MD din nan, a rikesa a branch dinsu na can Lagos din ace an masa transfer. Da daddare Mayraah na shirin kwanciya kiran Maheer ya shigo wayarta, dauka tayi ta zauna gefen gado sannan ta daga, bayan sun gaisa, a hankali tace "Was it successful yaya?" Yace "Nop Mimi, wai sai nan da wata uku" Lokaci daya jikin Mayraah yayi sanyi, for kusan 4 days yake ta kokarin ganin ya samu transfer din zuwa Abuja, har Abba sai da yayi intervening a issue din, duk hope dinta yau idan ya kirata zai ce an maidosa Abuja, jin bata ce komai ba yayi kasa da murya yace "Kin yi shiru" a hankali tace "To me zan ce?" Yayi murmushi yace "Ki ce min congratulations" Ta buda ido tace "Wai anyi Transferring dinka?" Yace "Yes Mimi" Ba karamin farin ciki Mayraah tayi ba, har sallan dare sai da tayi a yan kwanakin nan duk don ya samu transfer din sai gashi kuma ya samu, yace "But Abba ne fa yasan yanda ya bi aka yi Transferring dina, it won't have been possible idan ba don shi ba" Mayraah tace "Maa sha Allah, congratulations yayana i am so happy with this news, yanzu yaushe zaka yi resuming aiki a nan?" Yace "Sai monday next week, but in sha Allah zuwa friday zan dawo Abujan" Tace "Toh Allah ya kai mu yayana" Tana son tambayarsa ko da Haseenahn za su taho amma dai tayi shiru bata yi tambayar ba, yace "Bari in kira Ammi in gaya mata, i told u first before her" Mayraah na murmushi tace "To yaya, bye" Maheer na kiran Ammi bayan ita ma tayi farin ciki tace "To yanzu ya za kayi da yarinyar nan?" Yace "Kawai ta tafi gidansu" Ammi tace "Aa babu wannan zancen Maheer, babu yanda muka iya haka zaka taho da ita nan, the chalet here is almost 2 times bigger than the one u are inside now, hakuri za kayi ku taho tare" Maheer yayi shiru don bai yi expecting Ammi zata ce haka ba, Cikin kwantar da murya tace "I understand you dear, amma kayi hakuri na ɗan lokaci ne, bazan taɓa goyon bayan ka ci gaba da zama da Haseenah ba yanzun ma kai ma kasan akwai dalili ne" Shi dai bai ce komai ba, don gaba daya mood dinsa har ya baci. Ranan Wednesday Mayraah na shiga asibiti da safe bayan ta dubo wata patient a wani ward tana dawowa reception sai ga Dr Khalil ya shigo, tana hango wanda suka shigo tare kawai tayi saurin juya masu baya pretending bata gansu ba, da haka ta nufi wani ward da sauri ta shige ciki kamar zata je dubo wani patient, duk MD na kallonta, nurse din wajen ta gaishesu da ladabi, har MD din ya fara tafiya toward step sai kuma ya dawo ya cire glasses dinsa yana kallon nurse din da kyau yace "Anyi cleaning office dina yau?" Nurse din ta mike da ladabi tace "Yes sir, ai kullum sai cleaner din ya yi cleaning office din sannan ya maida ma secretary spare key... He does that every day ko baka nan" Yace "Fine, i need my library shelf carefully dusted and cleaned to my satisfaction today, Da muka shigo ai kamar ba ke kadai bace a nan" Ta gyada kai da sauri tace "Eh ni da nurse Ilham ce, amma ta shiga ward 3 zata dubo patient" Yace "Good, look for her ki gaya mata abinda nace don ita zata yi aikin ba wani ba, or you just tell her to meet me in my office immediately" Nurse din tace "Okay sir" shi dai Dr Khalil na tsaye yana kallon MD da mamaki, Nurse din ta tafi da sauri inda Mayraah ta shiga don kai mata sakon MD, Dr Khalil ya bi bayan MD da ya nufi step yace "Dama nurse ta taɓa maka gyaran office Dr? We have more than enough cleaners in here" MD yace "Za a fara yau, kai baka ga duk ka sa yarinyar nan ta gama raina mu ba, wato tafi karfin ta tsaya ta gaishemu shine zata shige ward, to zata yi gyaran every nook and cranny na office dina yau kuwa, next time ma idan tayi repeating haka abinda zan yi mata kenan, silly girl" murmushi kawai Dr Khalil yake yana biye da shi a baya. Mayraah ta dinga kallon nurse din da ta kawo mata sakon MD tace "In same sa a office kuma? Allura fa zan ma patient din nan idan ta gama cin abinci" Nurse din tace "I will handle that, kawai ki tafi ya ce yana jiran ki" Mayraah ta fita daga ward din ta taɓe baki ta wuce sama, jiya da baya nan asibitin so conducive wallahi. Knocking din office din nasa tayi tana hade rai, har sai da ta kwankwasa sau uku sannan taji yace a shigo, ta bude kofar ta shiga, gaban table dinsa ta tafi ta tsaya bata bari ta kallesa ba tace "Good morning sir" Bai amsa gaisuwar ba ya nuna mata direction da shelf din Libraryn nasa yake yace "Take out all those textbooks and articles, dust and clean, finish with that first...." Mayraah ta dinga kallonsa taki cewa komai, ya daga kai ya kalleta yace "What are you still waiting for?" Juyawa tayi ta nufi shelf din da ya nuna mata fuskarta a daure, ya bi ta da ido, tana isa nan ta fara sauke textbooks din daya bayan daya tana ajiyesu kasa, sai da ta sauke many of the textbooks ta fara jin kamar dust a hancinta, still dai ta ci gaba da fiddo su, tana ajiye na hannunta taji tari ya taho mata, da sauri ta rufe hancinta da hannunta, kamar tayi triggering tarin sbda ƙuran dake hannun nata, ta durkusa nan kasa da sauri within few seconds she began gasping for breath, bai san sanda ya karasa inda take ba ya duka gabanta ya dago kanta da sauri yana kallonta yace "Are you Asthmatic?" Sai kuma ya janyeta daga wajen textbooks din ya zaunar da ita kan office chair dinsa trying to help her with first aid, amma numfashinta sai kokarin daukewa yake, lkci daya duk ya daburce a wajen kamar bai taɓa zama likita ba a rayuwarsa, gashi dai bayan pills da injections har inhaler akwai a show glass din magunguna dake office din but he was just lost ya kasa yi mata komai, dai dai nan Dr Balogun ya shigo office din, da sauri ya nufosu lkci daya kuma yake tambayar me ya sameta, yana fahimtar Asthma ne ya fara mata abinda ya kamata a wajen, cikin kankanin lokaci ya dauko pills a show glass ya bude ya dau bottle water dake kan table ya bata, with his help ta hadiyi pill din, they were there for almost 15 mins yana kokarin calming dinta har ta fara sauke numfashi a hankali, MD was just standing like a quack Dr a wajen with no help, Dr Balogun ya dinga mata sannu, bayan some minutes yace "Are you okay now?" Ta daga idanuwanta da suka kada, duk da azaban da kirjinta ke mata ta gyada masa kai, yace "Ok now duk ward din da kika ga babu kowa a nan sama kije ki kwanta, get some rest" Tayi karfin halin mikewa tsaye Dr Balogun ya bata hanya yana mata sannu, tana fara tafiya ta ji kanta na juya mata tayi baya zata fadi, kafin ta kai kasa MD yayi saurin riketa, Dr Balogun yace "Her Bp is low" kwantar da ita MD yayi kan examination bed dake office din nasa, Dr Balogun na kallonsa yace "Akwai coffee powder ayi making mata coffee ta sha?" MD ya dauko Tea cup dinsa yana wankewa sau daya ya kalli cikin cup din keenly, kafin yayi attempting sake komawa ya wanke Dr Balogun ya amshi cup din yace "I will do it..." Cikin mintuna kadan yayi making coffee a cup din ya mika masa yace "I have a patient in my office... I will be back idan na sallamesa yanzu" MD ya amshi Coffee din ya juya yana kallon Mayraah da idonta ke a rufe, Dr Balogun ya fita daga office din da sauri don dama tambaya ya shigo yayi masa....
Chapter 228 · 0% Book details