← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 208 OF 313

Sashe 208

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru Abba yayi yana ta kallon Usman, can ya ɗan yi murmushi yace "Did you say this to anybody? I mean did u discuss it to anyone?" Usman ya girgiza masa kai without looking at him, Abba ya sauke ajiyar zuciya, bayan few seconds yace "Not even her?" Usman yace "Eh" Abba na gyada kai yace "Gaskiya nayi farin ciki da wannan batun Usman, i am so happy about it, and this is what i wished for few months back, but...." Usman ya daga kai ya kalli Abba, calmly Abba yace "I want u to let ur intentions be known to her before anything...." Usman ya girgiza kai da sauri yace "Abba kawai ba sae nayi hakan ba, kawai dai..." Sai kuma yayi shiru, Abba yace "You have to Usman, kwanaki i wasn't willing to give her an alternative cause tunanina hakan kadae ne mafita gare mu da ita baki daya, and i understand you too then da kayi declining... But yanzu i don't think i will do anything without her consent, say ur mind to her, go on a courtship with her...." Kallon Abba kawai yake baya ko kifta ido, Abba jinjina masa kai giving him assurance yace "Ko nan da sati daya ne in dai da consent dinta you gat my back son" Usman bai iya yace komai ba ya sauke kansa, Abba dai sae kallonsa yake, bude kofar parlon aka yi Mayraah ta shigo da sallama, Abba ne kawai ke kallonta, Usman kam bai daga kai ba, har ta karaso ta zauna gefensa tana kallonsa tace "Yaya na gama mu tafi gida" Abba yace "Nan din ba gida bane?" Ta kallesa ta ɗan yi murmushin karfin hali tace "Abba ae ban ce ma Ammi zamu kwana ba shi yasa" Abba ya gyada kai yace "Toh in kin ce mata sai ki zo kiyi weekend a nan din" Mayraah dai bata ce komai ba ta mike tana kallon Usman tace "Yaya Ammi fa tace kar dare yayi sosai" Sai a sannan ya daga kai ya kalleta yace "To ba yanzu zan tafi ba" Ta marairaice tana kallonsa, mikewa Abba yayi yace "Naga ko karfe tara bai karasa ba ai Mimi, so there is still time, bari inje inyi sallah" Fita yayi daga parlon, Mayraah ta zauna kusa da shi kamar zata yi kuka tace "Yaya pls kaga dai Ammi bata san za mu zo nan ba ko, kuma ce min kayi wajen Maleeha fa za mu je, ni dai ka tashi mu tafi gida don Allah" jin yayi shiru ta ɓata fuska tace "Ka ji mana yaya" Sai a sannan ya juya ya kalleta yace "Nan din daji ne?" Ta turo baki ta koma ta jingina jikin kujera tana kallonsa fuskarta a daure, har bayan minti sha biyar bai ce mata ba, ita ma bata ce masa ba a parlon, lkci lkci take turo baki duk yana lura da ita, can ya mike tsaye, tana ganin haka ita ma ta tashi, ya kalleta yace "Ke a nan fa za ki kwana" Ko rufe baki bai yi ba tace "Wallahi bazan kwana ba" Tana fadin haka ta nufi kofa yace "Kar ki fita" Dawowa tayi tana kallonsa kiris ya rage ta fashe da kuka, ya koma ya zauna kan kujera, a hankali yace "Now tell me, me yasa baza ki kwana nan ba?" Ta zauna kasa daga gefensa tace "Kawai wajen Ammi zan tafi" Jin bai ce komai ba ta daga kai suka hada ido, tace "Pls mu tafi yaya" Hajiya Amina ce ta shigo parlon tana kallon sauran abincin da ba a taɓa ba tace "Ka ci abincin kuwa barrister?" Yace "Eh na ci, za mu tafi ne" Hajiya Amina tace "Ina ce ai a nan Mayraah zata kwana" Usman yace "Bata zo da shirin kwana ba" Hajiya Amina tace "Toh shikenan, ko weekend ne sai ta zo" Mayraah ta sauke wani ajiyar zuciyar relieve sanda taga sun bar gidan. Sai da suka yi nisa sosai ta kallesa tace "Yaya baza mu siya ma Ammi Apples da watermelon ba?" Yace "Ok za ki siya mata?" Tayi er dariya tace "I am not together with my Atm?" Ya ɗan kalleta yace "Nawa za a ara maki?" Ta langwabar da kai tace "Like 10k" Yace "Ohk" gun da ake siyar da fruits yayi parking ta juya ta kallesa tana jiran ya bata kudin taje ta siyo, bude motar yayi ya sauka ta bi sa da kallo, bayan wasu mintuna ya dawo ya ajiye mata ledan kan kafarta yace "15k, sai ki biya yaushe?" Dariya tayi tace "Muna isa gida" Yace "Alright" Suna isa gida bayan yayi parking ta bude motar ta sauka ta jira shi ma ya sauka, bayan ya rufe motar ya jingina jiki folding his arms yace "Mun iso gida" Bata san sanda ta fashe da dariya ba tace "Yaya ko ciki fa bamu shiga ba" Yace "Toh" Daga haka ya nufi cikin gidan, ta bi bayansa tana murmushi, suna shiga parlor Maheer kadai ne zaune yana danna wayarsa, sau daya Usman ya kallesa ya wuce sama, Mayraah na ganin Maheer ta nufi kujeran da yake ta zauna kasa ta ajiye ledan hannunta tana kallonsa tace "Ina yini yaya" Yace "Ina ku ka je?" Ta buda ido tace "Yaya ce min fa yayi wajen budurwarsa zai je shine ya kai ni Miller road, ashe wajen Abba zai je" Maheer ya maida dubansa kan waya yace "Ohk" Tace "Yaya ka ara min 15k cash pls" ya kalleta yace "Me za ki yi da 15k?" Tana murmushi tace "Just borrow me pls" Yace "Sai ki maida yaushe" Dariya ne ya taho mata tace "Gobe da safe" Yace "Ohk, mu je in baki" yana fadin haka ya mike, tashi tayi ita ma ganin ya nufi kofar fita tace "Aa yaya zan jira a nan ka kawo min pls" Ya juya yana kallonta yace "Why?" Shiru tayi bata ce komai ba, ya karasa kusa da ita, still looking at her yace "Why?" Ta sauke ajiyar zuciya tace "I am not going there because of ur wife" Yace "Do not call her my wife again Mimi, Haseenah is not my wife" Ita dai bata ce komai ba, yace "Mu je" a hankali ta fara tafiya tana biye da shi a baya, sai da suka iso chalet din tace "Amma bazan shiga ba, i will wait outside Yaya" Tana fadin haka ta tsaya dai dai stairs din chalet din, shi ma bai yi forcing dinta ta shiga ba, yana bude kofa Haseenah dake zaune kan kujera tana waya ta katse wayar tana goge hawayen idonta tana kallonsa, ko kallonta bai yi ba ya bar kofar a bude ya wuce daki, kamshin turaren da ta dinga ji na shigowa parlon ya sa ta mike ta taho bakin kofa don jikinta ya bata da mutum a wajen, tana ganin Mayraah bata bari sun hada ido ba ta koma inda take ta zauna, ba a dau lokaci ba Maheer ya fito da cash din a hannu, ya mika ma Mayraah ta amsa tace "Thank you Yaya" Shi dai bai ce mata komai ba yana kallonta, ta juya ta sauka daga chalet din ta koma main building din gidan da sauri, ledan fruits din ta dauko sai da ta fara zuwa dakin Usman tayi knocking ya bude kofar ganinta ya koma ciki ya zauna, ta bi bayansa tana murmushi tace "Ga kudin" Amsa yayi ya ajiye gefensa, ta juya ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita. Washegari Mayraah na idar da sallan asuba bayan ta gama azkar ta shiga dakin da Badiyyah take, zaune ta sameta kasa, Mayraah ta zauna tana kallonta tace "Ya jikin?" Badiyyah ta gyada mata kai, Mayraah tace "In kawo maki kunun ko shayi" Badiyyah tace "Ko wanne" Mikewa Mayraah tayi ta fita, Bangaren Ammi ta fara tafiya don ta gaisheta, tana shiga ta tadda Mama Ladi na minshari kan darduman da tayi sallah, dakin Ammi ta karasa tayi sallama, Ammi ta amsa mata, ta shiga dakin... Maheer na zaune gefen Ammi, ita kuma tana zaune kan darduma, Mayraah ta duka kusa da Ammi ta gaisheta, Ammi tace "Kin tashi lafiya" Mayraah tace "Alhmdlh" Kallon Maheer dake kallonta tayi tace "Ina kwana yaya" Yace "Lafiya lau" Mikewa tayi tace "Zan dawo Ammi" Daga haka ta nufi kofa Ammi ta bi ta da kallo har ta fita, sai kuma ta kalli Maheer a hankali tace "We will continue later Maheer" Bai bari sun hada ido ba yace "Ohk" daga haka ya mike ya fita daga dakin. The next day friday Mayraah na dakin Badiyyah da yamma Mama Ladi ta shigo, Mama Ladi tayi tagumi daga tsayen da take tace "Naga abinda ya isheni ni Ladiyo, Wato ke dai Mera baza ki ji shawaran da nake baki ba ko? Baki da aiki sai makale ma wannan mata kamar almajira, nace ki fita hanyarta kiyi ta kanki kin ki, me yasa kike cusa kanki a abinda bai shafeki bane? yarinyar da kowa yasan ba sonki take ba tun asali, yarinyar da saboda ita kiri kiri aka fasa aurenki da ɗan matsiyatan can, ko ke baki lura alhakinki ke bin ta ba? Ko wani me ciki za ki ganta fes fes gwanin sha'awa amma Badiyyah kamar sabuwar almajirar kana rod dake garin kaduna, ke ko don kar kije ki shaƙi wata cutar baza ki kama kanki daga zuwa inda Badiyyah take ba? To ni dai ba ruwana Mamuda na kiranki, yana can parlon Ammi yace ki je" Daga haka Mama Ladi ta fice daga dakin tana toshe hanci, Mayraah ta kalli Badiyyah da hawaye ya cika idonta, kasa ce mata komai tayi amma har cikin ranta bata son abinda Mama Ladi ke yi ma Badiyyah a gidan, abun yayi yawa, mikewa tayi ta fita daga dakin ta tafi bangaren Ammi, Abba na zaune parlorn Ammi, Ammi kuma na ta harkan gabanta, Mayraah ta zauna ta gaida Abba, Abba ya amsa yace "Anjima Usman zai kai ki can gidan Hajiya Amina kiyi weekend, mai aikinta bata nan" Sai a sannan Ammi ta juya ta kalli Abba, Mayraah dai ta kasa cewa komai tana kallon Abba, Abba yace "Sai ki dau kayan da za ki tafi da su" Ammi na kallon Abba cikin karfin hali tace
Chapter 208 · 0% Book details