← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 266 OF 313

Sashe 266

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

looking at Musharraf yayi kasa da murya yace "Now tell me, are you still interested in getting married to her" Musharraf ya daga kai ya kallesa, sai kuma ya ajiye book din hannunsa yace "Who?" MD ya jinginar da kansa da kujera yayi kasa da murya yace "The Girl" Musharraf ya sauke idonsa yace "Why the question?" MD ya kallesa yace "I will make sure...." Shiru yayi ta dalilin wayarsa dake vibrate, ya dauka yana kallon screen din, ganin Ceo ce ke kiransa ya daga ya kai kunne, bata taɓa spending din night a asibitin ba a iya saninsa sai gashi yau har karfe sha biyu da rabi na dare bata tafi gida ba, bayan yaji abinda tace a wayar a hankali yace "Ohk Ma'am" Daga haka ya mike ya nufi kofa Musharraf ya bi sa da kallo har ya fita. MD na isa office dinta ya sameta zaune kan 3 sitter ta lulluba da karamin duvet kamar me jin sanyi tana jiransa, tun da ya shigo yake kallonta ganin yanayinta ya dawo kamar mara lafiya, da ladabi yace "Are you really okay Ma'am, is anything the matter?" Kujera ta nuna masa alamar ya zauna without looking at him, ba musu ya zauna yana kallonta, bayan few seconds ta sauke idonta kasa cikin sanyin murya tace "Tambaya nake son maka Aliyu" Yace "Ohk Ma ina ji" Calmly tace "What did you know about Mary Ann" Ya sauke idonsa kasa, ya ma rasa ko mamakin tambayar nata yayi ko akasin haka, duk da ya jima yana mamakin dalilin da yasa ta sake haka da Mayraah har aka je da ita UK kuma ta sauketa gidanta bayan yasan tana da trust issues, wanda a duk ma'aikatan asibitin nata shi kadai yasan gidanta both UK, Abuja, and Lagos, bayan few seconds ya dago kansa yace "Ma'am ni ban santa ba, ban taɓa ganinta ba sai a asibitin nan, sai dai a yau i was also shock bayan da naga Mamina da Younger brother dina sun zo dubata all the way from kano, and i get to know that fiancee din brother na ce ita da na ce maki an fasa aurensu kwanaki" Ceo dai kallonsa kawai take, can tace "Brother din ka kuma?" MD ya sauke ido a hankali yace "Nima sai yau na sani" Ceo na kara wrapping din duvet din jikinta tace "Ko zan iya sanin me yasa aka fasa auren?" MD ya ɗan yi shiru, a ransa yaji bai kamata ya tona ma Mayraah asiri ba, this is supposed to be her secret in this hospital, yana jin ko Dr Khalil bai san wacece ita ba from the look of things, and bai kamata ya ce ma Ceo ai ita din ba a san asalinta ba, CEO ta dafa shoulder dinsa a hankali tace "Akwai wani abu da zaka boye min ne Aliyu? Talk to me kar ka ji komai" MD ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, ya san dai ko ya gaya ma Ceo wacece Mayraah yanda yaga take jinta a ranta ba raguwa zai yi ba, lumshe ido yayi ya bude bayan ya gama nazarin yanda zai sanar ma Ceo wacece Mayraah ba tare da yayi tarnishing image dinta ba, Murya can kasa yace "Uncles dina sun gano foster parent kawai gareta...." CEO dake ta kallonsa babu ko kiftawa ta sauke idonta ta dalilin hawayen da ya ciko mata, shi dai MD kallonta kawai yake, ta jawo tissue kan table din gabanta tana goge hawayen da yaki tsaya mata, MD yayi karfin halin cewa "Are you alright Ma?" Da kyar tana ci gaba da goge hawayen dake ta zuba idonta cikin breaking voice tace "Kasan me Aliyu?" Ya girgiza kai yana kallonta, cike da karfin hali tace "Ina son za mu je gidana yanzu, i want to show you something" Yace "Ok Ma'am" Mikewa tayi ta wuce Bedroom dinta ya bi ta da kallo, wondering why she is crying tun dazu, he is just confuse at this point, ba a dau lokaci ba ta fito sanye da kayanta, ko wayoyinta da jaka bata dauka ba ta nufi kofa, ya bi bayanta suka fita daga office din.
Chapter 266 · 0% Book details