Sashe 172
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*MUNA MARABA DA KU, MUNA GARIN SOKOTO MUNA AIKE KOWANI GARI KOWACCE QASA CIKIN AMINCI* Washegari da safe Mayraah na zaune dakin da aka bata bayan tayi wanka amma ko leka parlorn gidan ta kasa yi, tun da Dr Khalil yace mata gidansu matarsa ne ya kawota jikinta yayi sanyi ta kasa samun nutsuwa har gari ya waye, Karime ce ta shigo dakin da sallama, Mayraah ta gaisheta Karime ta amsa da fara'a tace "Hajiya na kiran ki a parlor" Mayraah ta mike sanye da hijab dinta ta fita parlor, da ladabi ta gaida Ummi, Ummi ta amsa tace "Baza ki je aikin bane naga baki fito ba har takwas yanzu" Mayraah ta sunkuyar da kai tace "Zan je" Ummi tace "To ki shirya ki fito kiyi breakfast kafin nan driver ya dawo daga ajiye yara makaranta sai ya sauke ki asibitin" Mayraah tace "Toh Nagode" Daga haka ta mike ta koma dakin da ta fito, karfe takwas da rabi Mayraah ta sake fitowa parlor bayan ta shirya cikin uniform, tana fitowa Karime kadai ta tarar tana ta aikace aikace a parlon, Karime ta nuna mata dinning area tace "Ga kumallon naki can na kai maki" Mayraah ta mata godiya sannan ta karasa ta zauna, shayin ta hada, ta debi irish da kwai ta fara ci, ko bayan da ta gama breakfast din tana ta zaune parlor sai ga driver yana sallama bakin kofar parlor, Karime tace "Yauwa ga Dreban ya dawo, Hajiya ta shiga ciki ta kwanta tace ince maki Allah ya tsare" Mayraah ta mike tace "Toh nagode" Daki ta koma ta dauko handbag dinta da wayarta sai ledan scrub din ta sannan ta fito ta kara yi ma Karime sallama ta fita. Driver na ajiyeta bakin gate din asibitin ta sauka tace masa "Nagode" Yace "Allah ya tsare Hajiya" Daga haka ta shiga gate din asibitin. Kamar jiya yau ma haka Mayraah ta jigata a asibitin don daga shigowarta da safe wani Dr Balogun ya aika a kira ta zuwa theatre, ba kuma wani aiki tayi ba kawai surgical equipments suke kira by their names ita kuma babu bata lokaci take mika masu Instruments din, kuma ko sau daya bata yi mistake din ko daya ba, wani ma bata jira a tambaya take mika wa sanin function dinsa, 2 other senior nurses ne tare da likitoci biyu a theatre din giving them assistant, ba su suka fito theatre din ba sai bayan azahar, Dr Balogun na kallon Mayraah yace "Ur alma mater Madam?" Sosai gabanta ya fadi, sai ga wani Dr ya zo yana ma Dr Balogun din magana, sum sum ta bar wajen da sauri ta koma reception tana zare ido, Nurse Hafsat tace "Sai yanzu, sannun ku da aiki" Dai dai nan Wata nurse ta ajiye telephone din hannunta saman desk tana kallon Nurse Hafsat tace "Who is Nurse Ilham?" Nurse Hafsat ta nuna mata Mayraah, Nurse din ta kalli Mayraah ta sanar mata Dr Khalil na nemanta a office dinsa, Tun da Mayraah ta shigo asibitin basu hadu ba bata ma san ko ya zo ba ko bai zo ba, sai da tayi sallan azahar sannan ta tafi sama zuwa office dinsa, bayan ta shiga ta kulle masa kofa ta karasa har bakin table dinsa ta gaishesa, ya ajiye aikin da yake yi a laptop yayi mata izinin zama sannan ta zauna ta sake gaishesa ya amsa yace "You looked stressed, ai tunda kika bari Dr Balogun ya gano ki sai kinyi hakuri da shi, haka yake in dai ya lura nurse bata basa problem wajen aiki and she is composed kuma ta san abinda take shkkn duk zai yi aiki sai ya sa an nemo masa ita sai dai in bata duty ranan" Mayraah dai bata ce komai ba sai murmushi da tayi, yace "Nasan baki ci abinci ba ko?" Bai jira cewarta ba ya dau ledan takeaway ya mika mata, ganin bata amsa ba yace "Karbi mana" Ta sunkuyar da kanta tace "Bana son ina daura maka burden dina, i am suppose to get food my self ba wai ka siya min ba" Yace "Ki tambayi Nurse Hafsat in dai ban siya mata lunch ba to probably ban zo asibitin ba ko kuma bana duty ranan, i do this for most of the nurses, it's nothing a wajena" Mayraah ta amsa a hankali tace "To Nagode Allah ya saka da Alkhairi" Yace "Ameen, ya kika baro su Ummi" Mayraah ta kallesa da sauri, sai kuma tayi kasa da murya tace "Amma me yasa zaka kai ni gidan in-law dinka?" Yace "Bayan in-law nima mamata ce ai, bani da kamar ta a duniya...." Kallonsa kawai Mayraah take, yace "Ina da shekara biyar Mom dita ta rasu ta bar ni gun stepmom dina, i still remember vividly the maltreatment from my stepmom, yes it is still in my memory, duk abinda tace shi Dad dina yake yi ba shi da wani say may his soul rest in peace, dangin Mom dina sun so daukana a lkcn stepmom ta saka dad dina yaki amincewa su tafi dani, to cut everything short, Ummi that was our neighbor then ita ta daukeni ta kawo ni cikin nata yaran bayan tayi threatening stepmom dita zata kai ta kara kotu cause barrister ce, Babansu zainab ma haka, kowa na shakkar shiga sabgarsu a layin, even my dad couldn't confront her duk da gidan su Ummi was opposite to ours, few years later dad din nawa shi ma Allah ya masa rasuwa, Ummi and her husband are the reason i am who i am today, and after everything they gave me der daughters hand in marriage... though Zainab father is also late bayan aurenmu da shekara biyu..." A hankali Mayraah tace "Allah ya ji kansa, Allah ya ji kan iyayenka kai ma" Yace "Shi yasa naji tausayinki da kika ce min ur parent were late" Nan da nan hawaye ya cika idon Mayraah, yace "Ya ku ka yi da aunt dinki about inda zaki zauna saboda aikin?" A hankali Mayraah tace "Dama tace kayi min recommending area da zan iya samun wajen zama a nan since mu bamu san Abuja ba kai kuma a nan kake" Dr Khalil na kallonta yace "Ohk akwai kudin kama wajen da zaki zauna din kenan?" Ta gyada masa kai, yace "Meye Budget din ku?" Ta ɗan yi shiru, sai kuma tace "Ai ban san nawa bane ake renting waje a nan" Yace "Nasan baki sani ba, amma nawa ku ke da shi a kasa don in san irin wajen da za a samar maki gidan" Tace "Like 300k yayi?" Khalil ya gyara zama yana kallonta da kyau yace "Yanzu akwai 300k din a kasa?" Ta gyada masa kai, kallonta yake ko kiftawa babu, hakan yasa ta sunkuyar da kanta, Yace "Ilham" Ta daga kai ta kallesa yace "Kuna da 300k din kama gida me yasa baki yi registration din admission da kika ce an baki ba?" Ta hade rai tace "I told u sai da aka tara kudin na taho, kuma da na zo naga an riga ma an rufe portal na registration har ma sun kusa fara exams, kaga ai dole za a soke admission dina" Dr Khalil yace "Wani makaranta ne? And where is the admission list?" Mayraah taji wani zufa na keto mata amma ta wani daure fuska, dai dai nan aka kwankwasa kofar office din ta mike da sauri kamar jira take tace "Kilan patient ne...." Yayi izinin shigowa sai ga wata patient da yake da appointment da ita ta shigo office din, tuni Mayraah ta fice daga office din nasa, gaba daya ta kasa samun nutsuwa a asibitin har aka yi la'asar, Dr Khalil na shigowa daga masallaci Mayraah ta ki barin su hada ido a reception din sai duba file din wata mata take a shelf, ya wuce sama, komawa tayi ta zauna a hankali tana Allah Allah karfe shidda lokacin da yan evening za su amshi duty yayi ta kama hanyar suleja komin dare kuwa, 6 nayi dot Dr Khalil ya sauko ita ko har ta fito daga changing room rike da jakarta, tana ganinsa ta wani hade rai taki yarda su sake hada ido, duk yana kallonta, makullin office dinsa ya mika mata yace "Get me my laptop and bring it to the parking space Nurse Ilham" Ta amshi makullin ya fita daga reception din, ko da ta iso parking space bayan ta mika masa laptop din yace "Ina za ki yanzu?" A takaice tace "Gida" yace "It's late ki ce zaki kama hanyar suleja yanzu, so kawai gidan Ummi....." Katse sa tayi da sauri tace "Aa ni bazan je ba gaskkya" yace "Saboda me?" Tace "Gidansu matarka ce fa" Yace "It's nothing, nace maki nima gidanmu ne, matata tasan wanene ni, ko dazu da muka yi waya da Ummi ta tambayeni ke, i told her anjima zaki je can cause nasan baki da inda zaki zauna nan Abuja yau din ma" it took more than 10 minutes kafin Dr Khalil yayi convincing Mayraah ya kai ta gidan surkarsa, duk jikinta a sanyaye ta shiga gidan kamar munafuka shi ko dama yana ajiyeta ya juya, Ummi na parlor da sister dinta Rabi'ah warce ita ma ranan ta zo, Mayraah ta zauna kasa ta gaida Ummi, Ummi ta amsa da fara'a tace "Ya aikin?" Mayraah tace "Alhamdulillah" Ummi tace "To maa sha Allah, yace min har yanzu baki samu wajen ba ko?" Mayraah ta gyada mata kai, Ummi tace "To in kin ga babu damuwa kiyi zamanki a nan mana sai ki dinga komawa gida weekend, ni dama da yace wai gida kike nema ki zauna hakan bai min ba kina 'ya mace, dama hostel ne cikin makaranta da sauki wannan, amma gida kam bai kamace ki ba" Mayraah dai kanta na kasa, Ummi tace "Sai ki ma iyayen naki bayani in sun gamsu ba wani takura sai ki zauna nan abun ki kina zuwa aikin ki, abinda in kin fita tun safe sai karfe shidda, weekend kuma sai ki je masu gida tun da naga Auxiliary nurses basu fiye aiki weekends a asibitin ba" Mayraah ta daga kai tace "Toh Nagode sosai, Allah ya saka da Alkhairi" Ummi tace "Ameen sai ki shiga kitchen ki debi