Sashe 32
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mikewa Musharraf yayi ya amshi Envelope din hannun Mami ya dake yace "What is it for?" Mami tace "Ka duba" Tana fadin haka ta zauna saman kujera tana kallonsa, a hankali ya ciro takardan cikin Envelope din ya warware yana karanta rubutun jiki, same content ne da wancan da aka fara kawowa, sai dai wnn an kara abubuwan da suka linka na farkon tsayawa a rai, Musharraf ya kalli Mami dake ta kallonsa babu ko kiftawa, zaunawa yayi side dinta yayi kasa da murya yace "And did you believe this Mami?? ke kin yarda da wannan takardar?" Mami dai kallonsa kawai take, can tace "Uhnn abun ne ai da mamaki da daure kai" Musharraf ya mike a fusace yace "Mami i swear to God wannan ba komai bane facce sharri, karya da hassada, daga ganin wannan rubutun kasan mahassadi ne yayi sa, beside dama ai babu wani auren da baya zuwa da kalubale barin idan shaidanu suka cika lamarin from every angle, all i know is that, koma wani mara aikin yi ne ya turo da wannan saƙon to yayi a banza, babu abinda hakan zai canza...." A hankali Mami tace "Musharraf" Kallonta kawai yake bai ce komai ba, Mami tace "Akwai abubuwan dubawa a lamarin nan...." Da mugun mamaki yace "Mami so u believe all this?" Mami ta girgiza kai tace "No ba wai nace maka na yarda bane my dear, kawai dai ina gudun abinda zai je ya dawo ne, this isn't a minor issue, sannan babu wasa a zancen aure don abu ne da ake son ayi sa na har abada...." Bai kuma ce mata komai ba ya bar parlon kamar zai tashi sama ya wuce dakinsa Mami ta bi sa da kallo, mikewa Mami tayi ta bi bayansa, bayan ta shiga dakin nasa tana kallonsa tace "Look Musharraf, bana son ka daga hankalinka, pray hard about it, Allah Ubangiji ya tabbatar mana da Alkhairi, and i pray this should be between me and you, ba sai kace ma kowa komai ba, Allah ya daura mu kan makiyanmu, no need to disturb ur self, i gat ur back" Musharraf ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, dama yasan Maminsa bazata taɓa juya masa baya ba, duk abinda yace mata ba haka bane, ita ma a hakan zata tafi a ba hakan bane, bata son komai yayi stressing din mata son dinta, because she loves him so dearly, he always reminds her of her late husband, shi yasa take jin sa har cikin ranta, and she can go any extent for him, mikewa Musharraf yayi ya kamo hannunta yace "Thank you for always believing in me Mami, and i appreciate ur support always" Ta sakar masa murmushi tace "Anything for you sweetheart" Ammi ce zaune dakinta sai Aunty Mariya da har a sannan ta kasa daina hawaye da ta tuna a hannunta zinarin nan yake aka sace sai ta kara rushewa da kuka, Maheer ma na tsaye dakin ya ma rasa abinda zai ce bayan Ammi ta kirasa ta gaya masa abinda ke faruwa, Ammi ta kalli Aunty Mariya tace "Wai baza ki rabani da wannan kukan da kike ba Mariya?" Aunty Mariya ta kara fashewa da kuka tace "Dole inyi kuka Ammi, ni fa aka ba abun nan a hannuna, kowa yasan ni aka ba ajiya, yanzu ta ina zan fara fisabilillahi? Waye yayi mana wannan aika aikan? sarkan kusan miliyan biyar, na shiga uku na lalace" Maheer yace "Yaushe Badiyya ta bar gidan nan?" Duk suka daga kai suna kallonsa, Aunty Mariya tace "Babu wanda tayi ma sallama kawai nemanta aka yi ko sama ko kasa" Maheer yace "To ita ta dauka" Ammi ta zaro ido tare da dafa kirji tace "Ka rufa mana asiri kada Hajja ta tsine mana Maheer, ta yaya zaka ce Badiyya ce ta dau zinari?" Aunty Mariya tayi shiru tana nazarin abinda Maheer yace, dazu fa da Hajja ta Kirata tana mata maganar zinarin Badiyya na zaune parlon, daga ita sai Hajja a parlor, kuma throughout today babu baƙin da suka hau sama banda Mama Ladi, Aunty Mariya ta mike tace "Wallahi babu tantama ita ce, don babu wani visitor da ya haura sama duk yau, Mama Ladi kuwa ko motsawa bata yi daga dakin Mayraah ba har yanzu" Aunty Mariya ta figi Hijab din Ammi zata fita, Ammi ta rikota tace "So ku ke ku jawo mana tashin hankalin da bashi da ranan karewa ne Mariya? Ta yaya za ace Badiyya ce ta dau zinari bayan ba ita kadai bane a gidan nan?" Maheer ya kalli Aunty Mariya yace "Ai kin ji irinta, ban san me yasa Ammi take haka ba, kuma wllh yanzu zan tafi gidan Hajjan duk inda Badiyya ta kai zinarin nan sai ta fito da shi wallahi idan ba haka ba in kakkarya yar iska" Aunty Mariya dake huci tace "Tare za mu tafi Maheer, sai dai duk abinda zai faru ya faru yau, idan ba tasan ta aikata rashin gaskiya ba ta yaya zata sidade ta gudu ta bar gidan ba wanda ya sani, yarinya shaidaniya kawai bayan gulma da munafurci ashe har da halin bera duk tana yi?" Ammi da hankalinta yayi mugun tashi ta fashe da kuka tace "Ni dai duk wanda ya fita da sunan zuwa gidan Hajja ya samu Badiyya da zancen zinari ban yafe ba koma waye" Daga Maheer har Aunty Mariya haka suka tsaya kallonta, Maheer yace "Toh Allah ya baki hakuri Ammi, yanzu dai gold din nan zai yi miliyan 5 ko ma fin haka, kuma babu ta yanda za a kai Mayraah gidan mijinta babu wannan gold din tunda su suka saka a lefe, don haka sai a san yanda za ayi" Ammi na goge hawayenta tace "Ba komai, ai anyi hotonsa a waya, Zan sa a shiga kasuwa a duba min sak irinsa, Allah ya sa hakan shi yafi alkhairi" Maheer ya juya ya fice daga dakin, Aunty Mariya ta bi bayansa. Aunty Mariya ta bi Maheer har zuwa dakinsa ta kulle kofar, a fusace Maheer yace "Kinga exactly abinda kika gani yanzu Aunty? To kullum a haka ake, kwata kwata Ammi bata son ace Badiyya tayi laifi balle a hukuntata, idan kayi magana tace bata son Hajja ta kullaceta ne saboda wasu dalilan da ta bar ma kanta sani, Hajja bata da aiki sai lakaba ma Badiyya maraici wanda wannan mentality din ya riga ya makale a kwakwalwar yarinyar yanzu, an lalata mata rayuwa kawai, babu wanda ya isa ya hanata ko ya sa ta, iskancinta take zubawa yanda ta ga dama...." Aunty Mariya da zuciyarta ke tafarfasa tace "Ai kaga Malam Bahaushe sai Allah kawai, da mutum ya rasa iyayensa ko makamancin haka sai ayi ta binsa da wai maraya ne shi, wanda wnn kalmar ba karamin tasiri yake a zuciyar yaron ba, yayi ta amfani da shi yana iskancin da ya ga dama, dama shi Maraya saboda iyayensa sun mutu sai aka ce a sangartasa har a bar sa ya lalace?" Maheer ya zauna gefen gado yace "Toh baki samu labari bane kwanaki har cewa tayi ita idan ba lecturer din da ke neman Mayraah ba to ita fa sai dai ta mutu, tayi ta iskanci iri iri a period din Ammi da Hajja na biye mata, infact i am fed up with all this wllh, har bana son a nuna Badiyya a kirata da er uwata saboda mugun halinta da yayi tsamari, yanzu ai ya ci ace tana da tsayayye ita ma tayi auren nan, amma babu ko daya, kullum sai dai wannan ya zo ya dauketa a mota ya dawo da ita, wancan ma ya zo ya dauketa ya dawo da ita a gidan Hajja, kuma Hajja bata da bakin magana don rufeta da fada take kamar zata mata duka" Aunty Mariya tace "Yanzu dai ba Ammi tace taji ta gani kar a ma Badiyya magana ba ita zata siyo wani gwal din? To ai shikenan, ko ba komai ni dai hankalina ya kwanta" Tana kai wa nan ta fice daga dakin.... Haseenah ta rike haɓa tana kallon Badiyya tace "Yanzu ke baki ji tsoron wannan abun da kika aikata ba Badiyya? Kilan ba ana can gida ya hautsine ana neman zinarin nan" Badiyya tayi wani dariya hade da taɓe baki tace "Kuma babu wanda ya isa yace ni ne don Hajja kadai ta ishesu wllh" Haseenah tace "Gold din nan fa zai yi miliyan hudu kila Badiyya" Badiyya ta hade rai tace "Ni dai in zaki hada ni da masu siyar da Gold da kika sani a kasuwa ki hadani in kai abun nan su bani kudina, waye zai san na sata ne gwal din idan ba fada aka yi ba tunda dai ba waya bace balle ace za ayi tracking, kawai ce masu zaki yi Mummynki zata siyar amma reciept ya ɓata tunda kince sun saba ciniki da ke" Haseenah tace "Ai ni tsoron abinda zai je ya dawo nake Badiyya, what if daga karshe suka gano na sata ne in one way or the other kuma gashi nayi involving Mummy a ciki, kin fa san halinta" Badiyya tace "Wallahi ke shegiyar matsoraciya ce Haseenah, babu wanda zai tsaya wani bibiyan zinari, abun nan fa family issue ne su kansu baza su so ya fita waje ba, kuma Hajja bazata bada chance din da kowa zai zargeni ba, haba sai kace baki san Hajja ba" Haseenah tace "To nawa zaki bani a ciki yanzu don nasan halinki da kudi, dama in bai min ba to wllh bazan yi hanyar siyarwa ba" Badiyya ta gyara zama tace "Ai wllh kin fi ni son kudi Haseenah nawa ne kawai ya fito fili, yanzu dai in sun siya miliyan hudun da kike ta cewa zan baki 500k a ciki" Haseenah tace "Kan uban can, to ai ni ba er iska bace, ungo abinki kije ki siyar da kanki" Badiyya ta mata wani kallo, can ta kyabe baki tace "To naji zan baki 1M in dai miliyan hudun aka siya, in basu siya haka ba to wllh bazan baki haka ba, ai ba wani ya sato min ba" Haseenah tace "Za ma su siya hakan, wnn fa da kyar in bai yi gram 45 zuwa hamsin ba" Badiyya dai sai murmushi take, Haseenah tace