← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 213 OF 313

Sashe 213

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

mata ta gansa tsaye jikin motarsa, kallonta yake babu ko kiftawa kamar yanda ita ma take kallonsa, she just can't explain how she felt seeing him at the same time sai taga ya rame, kana ganinsa kasan ba shi da rest of mind, tayi karfin halin cewa "Ka shigo" Ya nufota har sannan yana kallonta, ta juya ta koma cikin gidan, wajen shan iska ta tafi yana biye da ita ta zauna, shi ma ya zauna yana facing dinta, a sanyaye tace "Good evening sir" kasa amsawa yayi ya dafe kansa, ta sauke idonta tana goge hawayen da ya fara taruwa da yatsunta, cikin rawan murya tace "Kayi hakuri, this our destiny" Yace "What is our destiny Mayraah?" Ta daga kai ta kallesa tace "Allah bai rubuta za mu yi aure yanzu ba" Yace "Sai yaushe?" Tayi karfin halin cewa "May be years to come, in dai da rabon za mu yi aure babu wani abu da zai hana hakan amma a yanzu kam ban ga alaman za mu yi ba" Yana gyada kai yace "Sai yanzu na sake tabbatar da baki so na Mayraah, i now believe ni ne kawai nake son ki, ni ne kawai nake bata lokacina" Ta fashe da kuka tace "Saboda me zaka ce haka? Iyayenka baza su yarda ka aureni ba, nima iyayena baza su yarda in aureka ba bayan duk abubuwan nan da suka faru a dalilin wedding dinmu that never occurred, and ah baya da nake tunanin zan iya bin ka mu tafi mu yi aurenmu a wani waje may be ban zauna nayi tunani da kyau bane a kan hakan, i get to understand that it's the biggest mistake da ni da kai za mu yi making idan mun yi hakan, aure babu albarkan iyayenmu bazai mana lasting ba, daga karshe duk za mu zo muna da na sani ne, but keep in mind sir, you still remain my first love, a kanka na fara soyayya akan ka nasan menene so ina alfahari da hakan, sannan kayi min so na tsakani da Allah, kayi min so na aure, kuma har gobe bazan taɓa daina sonka ba sai ma sonka ya karu a zuciyata, kawai mu jira lokaci Sir, ina ji a jikina we are meant for each other kuma za mu yi aure amma ba yanzu ba, may be sai a gaba ta yanda bamu yi zato ba, but for now let act just like frnds mu ci gaba da zumuncinmu da communication don mu samu sauki a ranmu...." Ya ɗan yi murmushi ya mike, a hankali yana kallonta yace "Thank you Mayraah" kallonsa kawai take ganin yanda idonsa ya kada, ya juya ya nufi gate, mikewa tayi da sauri tace "Sir..." Ko waiwayowa bai yi ba har ya isa gate din ya bude ya fita, wasu hawaye ne suka dinga sauka idonta ta koma ta zauna ta hade kanta da table tana kuka a hankali.....
Chapter 213 · 0% Book details