← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 313

Sashe 125

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 1 min read

ka janye batun auren nan, wallahi yau Ammi tace in je in daukota zata dawo gida...." Abba ya dakatar da shi yace "Ohk ita kuma warce aka daura mana auren da ita jiya sai in saketa yau saboda mahaifiyarka zata dawo ko me kake nufi?" Maheer yayi kasa da murya cike da damuwa yace "Abba masalha fa ake nema..." Dakatar da shi Abba yayi yace "Bana neman wannan masalhar, da mutunci na da furfurata mahaifiyarka da danginta suka walakanta ni suka nuna ban isa ba duk akan son zuciya irin tasu, to ni ba karamin mutum bane Maheer, aure ne an riga an daura kuma yau matar zata tare na sa an mata furnishing dakin Mayraah, Mayraah kuma zata koma dakinka nan din ma na sa an gyara, kai kuma duk sanda ka zo da iyalinka zaku iya sauka Chalet din gidan, period, go and bring back my daughter home....
Chapter 125 · 0% Book details