← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 237 OF 313

Sashe 237

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read

the ceo might not gree to that since...." Shiru Usman yayi bayan ya hango MD da ya fito daga cikin gidan, tunda Mayraah ta kallesa sau daya ta dauke kai gabanta na faduwa yake, kallonsa kawai Usman yake kamar yanda shi ma MD ke masa kallon cikin ido, har ya zo ya wucesu leaving his designer perfume scent behind, Usman ya dinga kallon jacket din da ya daura shoulders dinsa, can ya kalli Mayraah da ta juya kai taki kallonsu, a kan gado fa ta ajiye jacket din nasa ashe ya shiga ya dauka, Usman yace "Mayraah" Da sauri ta juya ta kallesa, yace "Wannan ba Jacket din da kika ce min Ceo ta baki bane?" Ta hadiye wani abu da kyar tace "Yaya shi ne, amma ai kilan shi ma ta basa ne ya sa...." Kana jin yanda take maganar kasan karya take, Calmly yace "Mayraah" Shiru tayi tana kallonsa, yace "Whose jacket is that?" Ta sunkuyar da kanta a hankali tace "Na shi ne, a airport ya bani saboda ni ban ciro nawa a akwati ba don ban san haka sanyin yake ba, shine sai ya bani nasa in saka" Kallonta kawai Usman yake, ta daga kai ta kallesa jin yayi shiru, after some seconds yace "To kin yi kokari" Tana ganin ya juya zai bar wajen ta marairaice tace "Yaya don Allah kayi hakuri, wallahi ina tsoron kar ka min fada ne shi yasa nayi maka karya" Yace "Infact karya kike still kice min babu komai tsakaninki da wannan mutumin, saurayin ki ne" Mayraah ta buda baki tana kallonsa da mamaki, juyawa yayi ya bar wajen ta bi sa da kallo, tafi minti uku tsaye wajen daga karshe ta juya a hankali ta fara tafiya zuwa cikin gidan.....
Chapter 237 · 0% Book details