← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 257 OF 313

Sashe 257

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 11 min read

Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788
Maheer ya karasa kusa da su ya duka yana kallon Mayraah ya kwantar da murya yace "Me kike so Mimi?" Shiru Mayraah tayi tana kallonsa tana sauke numfashi a hankali, Mikewa Ammi tayi ta bar wajen ta koma jikin window ta tsaya tana kallonsu, gaba daya damuwa yasa ita ma duk ta rame ba kadan ba don ko abincin kirki bata iya ci ganin halin da Mayraah take ciki, jin Mayraah tayi shiru Maheer ya rike hannunta yace "Talk to me Mimi, what is it? Me kike so?" Hawaye na sauka idonta cikin rawan murya tace "Yaya i just.... want to ask Musharraf for forgiveness, kilan mutuwa zan yi wallahi..." sai da Maheer ya sa kunne sosai sannan yaji abinda take cewa, ya dinga kallonta ya ma kasa cewa komai, da damuwa ya girgiza kai yace "No Mimi, baza ki mutu ba, ki daina kira ma kanki mutuwa pls, you will heal completely nan ba da dadewa ba in sha Allah, i know u are strong" Ta daura kanta a shoulder dinsa tana kuka a hankali tace "I am always finding it difficult to breathe, I can't do anything my self, my body is getting weaker everyday, bana iya tsayawa da kaina.... ina jin kamar mutuwa zan yi, ina son kowa ya yafe min..." Nan da nan hawaye ya cika idon Ammi tana kallonsu daga inda take tsaye, Maheer dai ya kasa cewa komai yana rungume da ita maganganunta na yawo a kansa, bata san he is just acting strong because of her ba, don a yanda yake ji kullum da yanzu an kwantar da shi shima amma bai bari abinda yake ji yayi weighing dinsa down ba cause he wants to be by her side always, kuka kawai Mayraah take tana jin kirjinta ya mata nauyi, shi kam he was trying all possible means to control him self yana patting bayanta a hankali, after many seconds da kyar ya dake yace "Za ki samu sauki Mimi, in sha Allah..." Ta girgiza kai da kyar tace "Amma ina son in masa magana pls Yaya, even Hamidah" Maheer bai sake cewa komai ba, ya kasa ci gaba da sauraronta yayi karfin halin kwantar da ita ya mike ya fita daga ward din, Ammi dai sai kallon Mayraah take ta kasa karasawa kusa da ita, ji take ina ma zata iya dauke duk wani ciwo da take ji a jikinta, hawaye ya kasa tsaya mata, tasan duk za su cinye wannan jarabawar ma kamar yanda suka cinye na baya, Bude kofar ward din aka yi MD ya shigo da sallama, ya kalli Ammi dake share idonta, ya kalli Mayraah dake kuka ita ma saman gadon, yayi kasa da murya yana kallon Ammi yace "Ma'am za mu ɗan yi magana a waje" Ba musu Ammi ta bi sa tana share hawayen da yaki daina zuba idonta, suna fita waje MD na kallonta da damuwa yace "Kukan nan da kike a ko da yaushe isn't helping her, you need to be strong, she will recover fully in sha Allah nan ba da dadewa ba" Ammi ta fashe da kuka tace "Dr dole inyi kuka, ko da yaushe sai tayi ta ce mana zata mutu, ta yaya hankalina zai kwanta, wallahi she is all i got, ita kadae ce macen da Allah ya bani" Tana kai wa nan ta kara fashewa da kuka sosai, MD ya jingina jikin bango yana kallonta bai iya yace komai ba, bayan few seconds a hankali yace "Bazata mutu ba in sha Allah, she will heal completely, i know it's not going to be easy, she is experiencing all this because she stayed too long in ICU, gradually jikinta zai dawo dai dai in sha Allah.... Abinda ya kamata yanzu idan akwai ko aunt dinta sai ta dawo nan ke ki koma gida, you need rest too, kema ba lafiya gare ki ba" Da sauri Ammi tace "Aa zan iya, i will be with my daughter" MD ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "Toh shikenan, let me speak with her now...." A hankali Ammi tace "Toh" Kujeran dake corridor din ta tafi ta zauna tayi tagumi, shi kuma ya shiga ward din ya kulle kofar, karasawa yayi gaban gadon yana kallonta, ta sauke idonta daga kallonsa tana sauke numfashi a hankali, ya dafa gadon cikin kwantar da murya yace "Akwai inda yake maki ciwo ne bayan chest dinki da kuma weakness da kike ji?" Girgiza kai tayi ba tare da ta kallesa ba, yayi kasa da murya yace "To ina za ki mutu ki je?" Sai a sannan ta daga manyan idanuwanta ta kallesa, Ya sauke idonsa yace "Yea, mutum baya mutuwa sai lokacinsa yayi, tun da baki mutu a ICU ba, a nan ma in sha Allah baza ki mutu ba, you won't die until ur creator is pleased with your soul, you are going no where in sha Allah, think about ur parent, brothers, relatives, friends, And...." Shiru yayi, ita dai kallonsa take, ya mike a hankali yace "And ur new pesky...." ita dai share hawayen dake makale idonta kawai take, yayi kasa da murya yace "You will get married, make babies... And fulfill all ur beautiful dreams in sha Allah" Ta daga kai ta kallesa, sunkuyar da kai yayi ya juya ya fita daga ward din, Ammi na ganin ya fito ta mike, ya karasa kusa da ita yace "Pls Ma'am ki rage kukan da kike a gabanta, always say encouraging words to her, it will really help" a hankali Ammi tace "Toh Doctor Nagode" Ya ɗan yi murmushi ya juya ya bar wajen, Ammi ta shiga ward din. Da yammacin ranan wajen karfe biyar Mayraah na zaune Usman dake gefenta yana bata shayin dake cikin cup din hannunsa, Ammi na zaune kan kujera tana azkar dinta, Umar da Mama Ladi suka shigo ward din, Mama Ladi ta cire gyalenta ta jefar kan kujera ta karasa kusa da Mayraah da sauri tana kallonta tace "Sannu Mera, wallahi yau satina daya a garin nan an ki bari in zo in duba halin da kike ciki yanzun ma zagawa nayi na biyo Umar babu wanda ya sani" Tana kai wa nan ta fashe da kuka ta rike kai tace "Allah ya isa tsakaninmu da Sanisa, Allah ya saka mana cikin gaggawa, Allah yayi mata abinda tayi mana, kuma naji dadi da Mashir yayi dubaran mikata hannun hukuma bakinsa alekum, da wa'e ne kilan kasheta da duka zai yi kinga sai laifin ya koma kansa dumu-dumu" Ita dai Mayraah bata dago kanta ba don hayaniyar Mama Ladi har cikin brain dinta take jin sa, yanzu gaba daya bata son hayaniya ko wani iri ne nan da nan sai kanta ya fara mata matsanancin ciwo ta fara ganin jiri, Ammi ta mike tana son ce mata ta rage murya amma ta rasa ta yanda zata fara gaya mata hakan, Umar dai tun da suka shigo da ita ya tafi far end of the ward ya zauna yana kallonta don tada masa bala'i tayi sai ya kawo ta, ko su Aunty Mariya basu san ya taho da ita ba, Usman na kallon Mayraah da taki amsan shayin yace "Ya isheki?" Ta gyada masa kai, ya ajiye sauran shayin ya gyara mata pillow din bayanta ta kwanta, can dai ya kalli Mama Ladi da taki yin shiru ga kukan da ta cika kunnensu da shi yace "Don Allah Mama ki yi kasa da muryarki asibiti ne nan akwai marasa lafiya, shi yasa ba a barin mutane su shigo anyhow" Ta juya da sauri tayi facing dinsa ta wani tsuke fuska kafin tace komai aka bude kofar ward din, Maheer ne ya shigo da sallama duk suka juya suna kallonsa har ya karaso ciki, da mamaki Ammi ke kallon warce ke bayansa da hijab dinta har kasa, Mama Ladi har da kifta ido don ita ma ta tabbatar da warce take gani a bayansa, Mayraah ma ta dinga kallonta har ta karaso cikin ward din, gun Ammi ta fara zuwa kanta a kasa ta gaisheta a hankali, Ammi ta amsa tana kallonta, daga haka ta karasa kusa da gadon ta kalli Usman tace "Ina yini Yaya" Yace "Lafiya lau" ta maida dubanta kan Mayraah, Mayraah ta sunkuyar da kanta, a hankali tace "Ya jikin Mayraah?" Mayraah ta gyada mata kai kawai, Mama Ladi da abun duniya ya isheta ta ja Kujera ta zauna tace "To yanzu fisabilillahi ke kuma uban wa ya maki kwatancen nan? Salon a ganki cikinmu a gano baki da aure mu bar abun fadi a asibitin nan ayi ta nuna mu da hanci in muka zo wucewa, me yasa baki yi zamanki a inda kike Badiyya, yanzu domin Allah meye amfanin zuwanki nan ki bar mana abun fade" Badiyyah dai kallon Mama Ladi kawai take bata ko kiftawa, Mama Ladi ta kyabe baki tace "Ni yanzu ban ma san yanda zan bi in fita asibitin nan ba gashi ban sa Shijabi ba, tunda nasan duk yan asibitin sun san nan dakin kika shigo, wannan ai sai ayi tunanin kema pamilynmu ce bayan ba haka ba" Badiyyah da har hawaye ya cika idonta ta sunkuyar da kai, a hankali ta fashe da kuka ta durkusa gaban Mayraah tana kallonta cikin kuka tace "Nasan ni ce silan duk wani abu da ya sameki saboda son zuciya na, i wish i never did all what i did to you Mayraah, nasan ban yi deserving yafiyarki ba kuma bazan ce ki yafe min ba, amma ina maki fatan Allah ya baki lafiya, Allah ya ci gaba da daukaka ki a rayuwar ki, i wholeheartedly regret all what I did Mayraah, nayi ruining happiness dinki for my selfish interest..." Mayraah dai kanta na kasa hawaye na sauka idonta, Mama Ladi ta fashe da matsanancin kuka tace "Wayyoo Allahnaa, wayyoo" Badiyyah dake kuka sosai ta mike da sauri ta fita daga ward din, sai a sannan Mayraah ta daga kai hawaye na sauka idonta, Ammi dai ta rike kanta daga inda take zaune, a hankali Mayraah ta jinginar da kanta jikin kafadar Usman dake gefenta tana kuka a hankali, shi dai idonsa na kofar ward din baya ko kiftawa, jin yanda take kuka ya juya ya kalleta, sauke idonsa yayi ya mata side hug trying to comfort her without saying anything, da sauri ta fada jikinsa tana kuka sosai, Maheer ya sauke idonsa ya juya ya fita daga ward din yana jin kukan nata har cikin ransa..... Dr Hamid ne ya shigo ward din, yana kallonsu yace "Plss plss bata bukatar duk wannan hayaniyar a kanta duba da condition dinta, mutum daya ya isa ya zauna tare da ita ba sai an cika daki haka ba, ka'idar asibitin nan kenan kuma lokacin visting ya wuce tun dazu" Mama Ladi ta share hawayenta tana kallonsa tace "Amma dai asibitin yan iska ne asibitin nan, yau naga bala'i da neman fitina, ta yaya za a dinga mana walakanci ana hantaran mu kamar wasu en banza, ko basu san waye Mamudan bane a garin nan, ba fa a banza muke ba don ka ganmu bama cikin hayyacinmu mun yi wujiga wujiga sbda tashin hankali, wallahi ba yan banza bane, meye haka kamar in an mutu a nan din aljanna za aje? Ni tunda uwata ta haifeni ban taɓa jin wannan ka'ida ba sai a shegen asibitin nan, yau kwanana takwas a garin nan anki bari in shigo nan ana ta mana iya shege, na samu da kyar an kawo ni yau kuma kace daga ina na fito? To wallahi ka fita idona in rufe" Dr Hamid dake ta kallonta ya juya ya fita, tuni Ammi ta mike ta kasa tsaye ta kasa zaune taji kamar ta nutse wajen don kunya, Usman dama kauda kai yayi, Mama Ladi ta ja tsaki tana huci tace "Yau ga figaggen likita kawai zai kawo min fi'ili, ko dai asibitin na ubansa ne ne" Dr Hamid na fita office din MD ya tafi, bakin office dinsa ya samesa ya fito kenan, MD yace "Pls karfe nawa ne injection din nata?" Dr Hamid yace "MD pls talk to her family su bar yarinyar nan ta yi recovering yanda ya kamata kar su yi traumatizing ƙwaƙwalwarta, me yasa ma security za su dinga barin suna shigowa haka, ina ce tun karfe uku aka gama visting, noise din wata tsohuwa naji har corridor fa kamar ana cin kasuwa, what if Ceo ta shigo yau...." MD dake ta kallonsa yace "I will talk to the mother, no more visitation till she recovers completely, Ceo din ma na hanya yanzu haka...." Dr Hamid yace "Gaskiya hakan zai fi Sir, talk to the mother" Daga haka ya juya ya bar wajen, MD ya sauka downstairs zai je duba wani patient da suka yi ma aiki dazu da safe kafin ya je ya samu Ammi a ward din da Mayraah take, tun daga nesa yake kallonsa babu ko kiftawa kamar yanda shi ma yake kallonsa har ya karaso cikin reception din, ya cire face cap dinsa zai wucesa without looking at him yace "Good evening" MD ya bi sa da kallo yace "Daga ina kake?" Bai tsaya ba yana ci gaba da tafiya yace "Kano" MD ya bude ido sosai ganin matar da ta shigo Reception din, ya karasa wajenta da sauri, cike da mamaki yace "Mami, daga ina ku ke haka?" Mami na kallonsa daga sama har kasa tace "Daddy you told me u are in Adamawa da na kira ka dazu...." Yana shafa kansa yace "Eh na dawo ne Mami, me ku ke yi a nan?"
Chapter 257 · 0% Book details