← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 313

Sashe 55

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tace "To hukuncin me kuma? Abinda aikin gama ya riga ya gama, kawai a dai ja mata kunne yanda ya kamata a gargadeta ayi mata jan ido, yarinyar nan fa marainiya ce, ba uwa ba uba" Mama Ladi tace "Ko daga kasa aka tonota karewar rashin uwa da uba sai an mata hukunci dai dai da abinda ta aikata don uwarta...." Bude kofar dakin aka yi Aunty Mariya ta shigo tana kallon Hajja tace "Gani Hajja" Hajja tayi kasa da murya tace "Ammin na iya lallabowa ta zo nan yanzu? Naga tana da baƙi kuma magana nake son maku" Aunty Mariya tace "Toh bari in je in gaya mata, zata iya zuwa ai" Hajja tace "Sannan har Maheer da Usman su zo" Aunty Mariya tace "In ji dai lafiya Hajja?" Hajja tace "Lafiya lau, duk dai ku zo" Aunty Mariya tace "Toh bari in masu magana" Daga haka ta juya ta nufi kofar, Hajja ta juya inda Mama Ladi ke tsaye tace "Ai kin ga gwara haka dai ko?" Wayam ta ga wajen... Mama Ladi na kallon Maheer da Usman tace "Don haka kashe wutan dakin kawai za ku yi kamar kun kwanta kada wanda ya fita wllh in da hali ma ina fita ku sa makulli, ni wallahi na ma fara zargin anya ba Hajjan bace ta turata ta aikata tsiyar nan? Aa gaskiya na fara tsoron Hajja kuma haka, dama tun asali an san na fita tsoron Allah tun muna yara" Usman da Maheer dai kallonta kawai suke, Maheer yace "Gwara da kika zo kika sanar min babu inda zanje" Mama Ladi tace "Atoh dai, dama shi Usuman tace azzalumi ne tun Badiyya na jaririya yake cutarta kiris ya rage wataran ya kasheta aka kama sa, Badiyyar da tsakaninsu bai fi wata 7 ba ko shidda, to ina ruwansa da ita kuma" Usman ya ci gaba da danna wayarsa dai bai ce komai ba, Mama Ladi tace "Dama shine nace bari in lallabo in zo in gaya maku kuyi ta kanku, babu gaskiya ko kadan a lamarin Hajja" Tana kai wa nan ta fice daga dakin, tana fita Usman ya mike ya sa ma dakin key, ai ko haka Aunty Mariya ta zo ta gaji da buga kofar babu wanda ya bude mata cikin shi da Maheer, Mama Ladi na komawa daki Hajja tace "Ina kika je Ladi?" Mama Ladi na kallon Ammi dake zaune kasa ta sunkuyar da kanta tace "Fyace majina na tafi yi a tsakar gida daga nan na leka makota ina ta masu ban gajiya kin san haka ake yi" Hajja ta maida dubanta kan Aunty Mariya da Ammi jin sun yi shiru bayan ta gama masu jawabinta, can Aunty Mariya tace "Haba Hajja, yanzu kina nufin shikenan sai a zuba ma Badiyya ido tayi ta abubuwa baza a dau wani kwakkwaran mataki a kanta ba?" Mama Ladi ta kyabe baki ta tafi gefen gado ta zauna, Ammi kam hawaye ne ke sauka idonta duk da kanta a sunkuye yake, Hajja ta fashe da kuka tace "To ya ku ke so mu yi ne?? Badiyyan nan fa ba bare bace, jininmu ce babu yanda muka iya da ita, ai hannunka baya rubewa ka yanke ka yar, addu'a kawai za mu dinga mata Allah ya shirya mana ita" Mama Ladi tace "Amma dai anya Hajja ba ke kika aika Badiyya tayi mugun abun nan da tayi ba yanda naga kina ta kakkare zancen nan, kamar kina tsoron a tona maki asiri ke ma..." Hajja ta kalleta sai ta rushe da sabon kuka tace "Allah ya isa tsakanina dake Ladi, kuma asuban fari na yi ki dau akwatinki ki koma inda kika fito, bana bukatar ki a nan kuma, har abada kar ki sake dawowa inda nake" Mama Ladi ta mike ta nufi kofa tace "Jama'a sai su ce basa son gaskiya kiri kiri, kuma kiyi ta cewa in koma karaye in koma karaye to dangin uwa gareni a can ko na uba, daga dai aure ya kai ni can miji ya mutu ya bar ni yau shekara goma sha biyu, to ina ruwana kuma da wani karaye, Badiyya ce dai sai an mata hukuncin da ya kamata don ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba zata iya kashe mutum, ke kuma da kike daure mata kugu idan ba ayi hankali ba sai ta iya zama ajalinki, ni tsoronta ma nake yanzu wllh, duk wanda zai iya lalata aure babu abinda bazai iya aikatawa ba a duniya, kuma Mamuda ne kadai ya isa ya koreni a gidan nan" Tana kai wa nan ta fice daga dakin, Hajja dai kuka kawai take, cike da karfin hali Ammi tace "Shikenan Hajja in sha Allah maganar nan ta wuce, babu me tada sa kuma, har su Maheer din zan masu magana, sannan kamar yanda kika bukata na maki alkawarin Mahmud ma bazai ji wannan maganar ba in sha Allah, Allah Ubangiji ya shirya mana ita" Hajja na share hawayenta tace "Ameen, Allah ya maki albarka Hajarah" Aunty Mariya kasa cewa komai tayi tsabar bakin ciki da takaici, can ta mike ta fice daga dakin, Hajja ta kalli Ammi tace "Ki tashi ki koma dakinki, Allah ya maki albarka, Allah ya baki lafiya ingantacce" Ammi tace "Ameen" sannan ta mike ta fita daga dakin, downstairs ta sauka don she needs to find a place tayi kukan nan ko zata ji sanyi a ranta, ta shiga dakin baƙi dake parlor ta tadda Aunty Mariya tayi tagumi, Ammi ta zauna dakin ta fashe da kuka tana girgiza kai tace "Shekara kusan ashirin da biyu kenan ake a haka, sau dayawa ina yin abinda nake ne don kada Hajja taga kamar ina fifita Mayraah da ban haifa ba akan Badiyyah da take jinina, don Hajja mahaifiyata ce nasanta ciki da bai, sai ku ga kamar ina goyon bayan Badiyyah a ko da yaushe amma ba a san duk don a zauna lafiya nake yin haka ba tunda gani za ayi na fifita Mayraah a kan er kanwata uwa daya uba daya, yanzu dai kinga yanda ta bi ta kakkare ta rufe wannan maganar ko?" Aunty Mariya da zuciyarta ke tafarfasa tace "Kuma wllh kada kice ma su Maheer komai, Allah ya kawo Badiyyar gobe da safe su fara ball da ita tun daga bakin gate" Ammi tace "Ki rufa min asiri Mariya, tun da tace in ja masu kunne gwara in ja masu babu ruwansu duk su zuba ido kawai, Allah shi yasan dai dai" Wajen karfe tara da rabi Maheer ya bude kofar parlon Ammi ya sameta zaune da Hajiya Safiyya ga plate din abinci a gabanta, yanxu kam she looks much better tun da gashi har tana cin abinci, ya zauna saman kujera yace "Ammi ya jikin?" Ammi na kallonsa tace "Alhamdulillah" Shiru yayi, yana son tambayar Mayraah amma ya kasa, can dai ya mike daga karshe ya fita, a stairs ya hadu da Aunty Mariya tana haurowa sama yace "Aunty Ina Mimi?" Aunty Mariya tace "Tana dakin Ammi" yace "Okay" Aunty Mariya tace "Wai ka ci abinci ma kuwa Dr?" Yace "Zan ci" Daga haka ya koma parlon Ammi, Bedroom dinta ya nufa direct ya bude kofar ya shiga, kwance ya sameta kan gado idonta a lumshe har ta fara bacci, ya karasa kusa da gadon ya zauna gefenta yana kallonta, hannu ya kai forehead dinta yaji her temperature is a bit high, ta bude ido da sauri suka hada ido, sai kuma ta mike zaune ta matsa daga edge din gadon ba tare da ta bari sun kara hada ido ba, yace "Kin ci abinci?" Ta gyada masa kai, yace "Ur injections and medicine" Ta girgiza kai tace "Aa maganin kawai zan sha" Yace "Ai maganin guda daya ne, kuma alluran ya kamata a maki" Mikewa yayi ya fita daga dakin, ba a dau lokaci ba ya dawo da ledan dake dauke da alluran da magani, tana kallonsa ganin ya fara hada alluran, tayi gathering courage tace "Zan yi alluran da kai na" Ya kalleta a bit surprise, Bata sake barin sun hada ido ba, Bayan few seconds ta sake cewa "Kawai idan ka gama hadawa ka bani inyi" Still shi dai bai ce komai ba, tun daga sanda ya zama likita har zuwa yanzu shi ke mata allura idan bata da lafiya, yawanci every month end sai yayi mata alluran cramps, ya ajiye syringe din bayan ya rufe sannan ya juya ya nufi kofa ta bi sa da kallo, ita kanta duk jikinta yayi sanyi, Yana fitowa parlor ya kalli Hajiya Safiyya da yake nurse ce, yace "Mama ana jirana a waje yanzu, ga alluran da za ayi mata can na sa a syringe" Daga haka ya fice daga parlon Ammi ta bi sa da kallo, Hajiya Safiyya ta mike ta shiga dakin, bayan ta gama yi ma Mayraah alluran ta fito, sai a sannan Mayraah ta lura da wayarsa da ya ajiye bedside drawer, ta dauka tayi searching number Musharraf sannan tayi dialing, a kashe ta ji wayar, lokaci daya jikinta yayi sanyi ta ajiye wayar ta koma a hankali ta kwanta da tunani iri iri a ranta... Washegari wajen karfe tara da rabi Aunty Mariya ta shigo parlon baƙi da sallama duk aka amsa mata, kallo daya tayi ma Badiyya dake zaune kasa ta sunkuyar da kai kamar algunguma ga Hijab har kasa a jikinta, Aunty Mariya ta nemi waje a parlon ta zauna ta gaida yan uwan mahaifin Badiyya da kanwarsu Hajiya Murja dake zaune parlon, ko minti ashirin ba ayi da zuwansu gidan ba, dama Aunty Mariya sai da ta tsaya ta gama sallaman su Haseenah da yan uwanta with breakfast sannan ta shigo parlon bakin shi ma don kada Hajja tace bata je bane banda haka da ko keyarta baza su gani ba, Hajja na zaune kasan carpet tayi tagumi, Ammi ma na parlon a zaune, sai Maheer da zuciyarsa ke ta tafarfasa, shi kam Usman dama kin zuwa yayi, Mama Ladi kuma Hajja tace in ta shigo bata yafe mata ba, Alhaji Nura ya daka ma Badiyya tsawa rai bace yace "Baza ki bude baki kiyi magana ba kina bata mana lokaci" Ta fashe da kuka me karfi tana bubbuga kafa tace "Wallahi kawu nace maku ban san komai kan zancen nan
Chapter 55 · 0% Book details