Sashe 256
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read
sam bai mata ba, to meye amfanin zuwan su Abujan kenan har yau basu ga marasu lafiyan ba, Mama Ladi tace "Ko ya zata cin abinci ya kawo mu Habujan, ni wallahi ban da yanda Hajja ta kirani tana kuka, da nayi ma kaina alkawarin ko gwal ake rabawa gidan Mamuda bazan sake tako kafata ba, don ba shi da mutunci mutumin, amma wannan ya zama dole ne kawai babu yanda na iya, don haka kin ga tafiyata asibitin idan kuwa ba haka ba idan zuciya ta debeni wallahi sai in dau jakata in koma karaye, iyaka duk wanda ya mutu in bugo waya ince Allah ya ji kansa ya gafarta masa" Tana kai wa nan ta fice daga parlon tana sakale da wani jaka a hammata, Hajja ta sauke ajiyar zuciya tace "Ae gaskiya ne Mariya, mu muna nan sai dai ayi ta ce mana jiki da sauki an ki barinmu muje mu duba su, a ina aka taba haka?" Aunty Mariya dai bata ce komai ba ta ci gaba da girkinta a ranta kuwa tasan Abba gudun su bar abun fade a asibitin yake ne, barin ma Mama Ladi... Mayraah na kwance bayan an maida ta ward jiya, sai da tayi kwana biyar da Ventilator Machine kafin aka cire, kuma duk da haka wani lokacin sai taji numfashin ta na mata gardama, gaba daya ta rame sosai, sai haske da ta kara ba kadan ba, har a sannan she is having difficulty in saying anything sai dai tayi ta bin mutane da ido, kana ganinta kasan tana jin jiki, Ammi na zaune gefenta tana rike da hannunta trying to comfort her kamar yanda take yi tun da suka fito ICU, wani lokacin kuma Usman ne ke zama by her side, Maheer dai sai dai ya tsaya jikin window yana kallonta, yana jin kamar ya maida pains dinta gaba daya jikinsa ta samu relieve, ganin tana son mikewa zaune Ammi ta zaunar da ita tana mata sannu cike da damuwa, da kyar Mayraah ta bude baki a karo na farko tun da suka fito ICU tana kokarin yi ma Ammi magana, Ammi ta kasa kunne don jin abinda take cewa, Maheer ya karaso kusa da su, Ammi ta kallesa bayan ta fahimci abinda Mayraah ke cewa, dukawa yayi yace "What did she want Ammi?" Kasa cewa komai Ammi tayi, ta kara kallon Mayraah dake sauke numfashi a hankali, Maheer yace "Pls me tace Ammi?" Ammi dai tayi shiru.