Sashe 173
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
abinci" Mayraah tace "Toh, nagode" Mikewa tayi ta nufi dakin da aka sauketa, Rabi'ah da ta bi ta da kallo tace "Ummi wacece?" Ummi tace "Bakuwa ce" Daga haka ta mike tace "Bari in je lokacin sallah yayi" Mayraah ta kai minti sha biyar tana nazarin zaman gidan da Ummi tace tayi, anya zata iya kuwa, though taga matar is very kind amma ita sai abun yayi mata wani iri a kai, shi ko tsoro baya jin kar su zargi wani abu ko ayi tunanin budurwarsa ce ita, kauda zancen tayi kawai a ranta daga karshe ta mike ta shiga bandaki. Da daddare Mayraah na daki Ummi ta shigo dakin tace "Ilham zo ki duba magungunan nan da Khalil ya bada aka kawo dazu bai bada prescription ba" Mayraah tace "Toh" Mikewa tayi ta bi bayanta suka fita zuwa wani daki, Wata tsohuwa ce zaune dakin kana ganinta kasan bata da lafiya, Mayraah ta zauna tana kallonta tace "Ina wuni kaka" Tsohuwar bata amsa ba, Ummi tace "Hajiya ba lafiya Ilham, duba magungunan ki ga" Da kyar tsohuwar ta bude baki tace "Kar ki sake sa ni a bakin duniya kice bani da lafiya Zuwaira, na kuma samu lafiyata babu abinda yake damuna yanzu, aniyar kowa ta bi shi" Ummi na kallon Mayraah tace "Ilham in kin bude maganin sai ki bata" Daga haka ta fita daga dakin, Tsohuwar na kallon Mayraah cikin rawan murya tace "Ke kiji rainin wayo, ita da 'ya yanta fa suka sa min guba yau sati uku kenan ina fama jiki yaki dadi, amma duk wanda ya zo sai tace masa Hajiya ba lafiyaa, sai terere take min" Tana kai wa nan ta fashe da kuka, Mayraah dai sai kallonta take ta ma kasa cewa komai, ta karasa buda mata maganin ta mike mata, hannu na rawa ta amsa ta dau cup din ruwa, Mayraah tace "Sannu, amma jikin da sauki ko?" Tsohuwar tace "Ke ba wani sauki, yanzu haka duk jikina ciwo yake er nan, banda yaron nan Halilu ɗan albarka ai da na mutu mushe a dakin nan, wai fa a haka an sa min gubar ban mutu ba sai ki ga ita wannan er figigiyar macen da suke ce ma Mimi tana lekoni tana raye raye da tafe tafe, su kuma yan biyun maza sai su zaga baya suyi ta buga kwallo kan windown dakin wai duk don kar in yi bacci, ke bari kawai abinda suke min a gidan nan wallahi kare bazai ci ba, Allah ya isa kawai, banda mutuwa me tonan asiri" Mayraah dai ta ma rasa me zata ce, Tsohuwar na matse kwallan idonta tace "Ga flask can ki tafi da shi ki dafo min wani ruwan zafin a kitchen ban yarda da wanda ke ciki ba tun dazu nake jiran shigowan Halilu ya dafo min wani ruwan shima shiru shiru gantalallen bai shigo ba yunwa nake ji kamar zan suma, ita ma munafukar me aikin gidan na daina yarda da ita duk bakinsu daya da yan gidan" Mayraah ta mike tace "Toh bari in dafo maki Kaka" Daga haka ta fita daga dakin, Tsohuwar tace "Gwara na kama bare kawai, in ma ta cuceni bazai min ciwo ba kamar na jikina" Mayraah na fitowa Ummi dake parlor da karime tace "Ikon Allah...." Karime ta kyalkyale da dariya tace "Ai kuma shikenan kun ƙulla da Inna tunda har ta yarda ki dafo mata ruwan shayi" Ummi tayi murmushi tace "To Allah shi kyauta, sai ki je ki dafo mata" Hajja na kishingide bayan isha a parlor tana kallon Badiyyah dake kwance ko sallan la'asar bata yi ba balle Magariba ga isha har anyi, daga gefenta kuma plate din abinci ne da Hajjan ta ajiye mata har ta cinye ta bar mata plate din a wajen, Hajja tace "Ke yanzu fisabilillahi Badiyyah ina ta magana tun dazu kin ki tashi daga kan kujeran nan, ga salloli a kanki, kima je kiyi sallan mana sai ki dawo ki ci gaba da latse latsen wayar Badiyyah" Badiyyah tace "Kai na shiga uku, ke Hajja nace maki bazan yi sallan nan bane da kika dameni haka, ina fa sane, ki bari in gama abinda nake a wayar mana tukun" Hajja tace "Kina jin ai gorin da suka maki ranan babu dadin ji, amma ni ko a jikina tunda nasan ba su suke bada mijin auren ba, ita Ladi dama makwadaiciya duk inda galmi galmi yake nan take makalewa, cabdi ta zo nan tayi min me tasan ni ba me kudi ba, ai in ma ta zo wallahi koran kare zan ma er iskar makwadaiciya, tunda bata da zuciya tayi ta zama gidan Mamudan...." Ko rufe baki Hajja bata yi ba aka tura kofar parlon duk suka daga kai, wasu maza ne su hudu suka shigo parlon, Hajja ta mike zaune a firgice tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una me zan gani haka, daga ina ni Sadiya??" Badiyyah da ta gigice ta mike tsaye ita ma gashi babu daman gudu duk sun zagaye Parlon, Daya daga cikinsu ya sanar da cewa su yan sanda ne ya ciro ID card dinsa yana nuna masu sannan yace "Wata waya muka yi tracking muka gano tana cikin gidan nan" Badiyyah jiki na rawa tana nuna masa wayarta tace "Wallahi waya ta ce wannan ku duba ku ga" Wani ɗan sanda ya daka mata tsawa yace "Kar ki rena mana hankali ke, bayan wayar taki wani wayar ce a gidan nan kuma?" Badiyyah tana zare ido tace "Waya kuma? Sai ɗan karamin wayar kakata fa wllhi" Hajja dai salati kawai take ta kasa zaune ta kasa tsaye ko ina na jikinta na bari, Wani firgitattcen tsawa da police man din yayi ma Badiyyah sai da ta kusa sakin fitsari yace "Idan kika bari muka shiga muka dauko wayar da kan mu to baza ki ji da dadi ba" Nan suka sanar mata sunan wayar har da color din wayar Badiyyah ta hadiye wani abu da kyar ganin babu wasa fuskarsu ga wani har yana kokarin kai mata mari tace "Yana daki bari in dauko maku" Bin ta suka yi har zuwa cikin dakin ta dauko wayar wanda farashinta zai yi miliyan daya da rabi suka amsa a hannunta suka kado ta parlor, Hajja salati take har a sannan tana zaga Parlon babu wanda ya bi ta kanta aka saka Badiyyah dake rusa kuka a gaba suka bar gidan. Abba na zaune parlor tare da Mama Ladi dake cewa "Ni kaina Mamuda wallahi na gaji da koke koken nan da Ammi take ba dare ba rana kan yarinyar nan Mera, ka tambayi su Mashir babu abinda bana gaya mata don dai ta kwantar da hankalinta amma duk a banza, zuwa yanzu ya ci ace ko mutuwa Mera tayi Ammi ta sa ma ranta dangana kuma haka balle er banzan na can in an bibibiya hankalinta kwance tana sabgogin gabanta mu kuma ta bar zuciyoyinmu cikin walagigi, ni da ba don ma kar ku kullaceni ba da sai ince dama ance tsintattciyar mage bata mage, Mera ta nuna cewar lallai da gaske mu ba danginta bane shi yasa ta shiga duniya kanta tsaye ko duba irin kyakkyawan rikon da aka mata na shekara 23 bata yi ba duk ta mance wannan halaccin, to ni ko Allah ya isa na mata sai ya bi ta duk inda take wllhi, kuma haƙƙin Ammi bazai bar ta ba a dubi mugun damuwar da ta jefata ciki fisabilillah, to shine nake son baka shawara Mamuda anya baza ka dau Ammin nan ko Saudia ne ku je ku kwana biyu ba ko Allah zai sa ta samu salama a zuciyarta, ni wallahi tsoro nake kada ciwon zuciya ya kamata tunda dama tana da hawan jininta duk mun sani, kaga ban ma san zaka kawo min maganar ba ina ta son in samu lokaci in zaunar da kai ince maka gaskiya a duba lamarin Ammi ashe kai ma hakan na damunka bawan Allah" Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Shikenan Mama, shawaran da kika kawo ma yayi gaskiya, in sha Allah zuwa nan da sati daya sai mu tafi Saudi Arabia kawai" Mama Ladi tace "Yauwaaa Allah maka albarka Mamuda, daga nan sai ku saka er banzan yarinyar a addu'a Allah ya karkato da hankalinta gida, ai gantalin ya isa haka kuma, ni dai kafin ku tafi dama kar ka manta kajin firiji sun kare, er mantinar ma duk Ammi nake juye ma a kofi in zuba mata madaran gwangwani duk sun kare su ma, kasan kuma babu dadi a tafi a bar gida babu isasshen kayan abinci" Bude kofar Parlon aka yi duk suka juya, Hajja ta shigo tana rusa kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Mama Ladi ta mike tace "Mun shiga uku mutuwa Badiyyar tayi??" Cikin kuka Hajja tace "Yan sanda ne suka zo suka tafi da ita muna zaune parlor ba laifi ba komai, yaushe rabon ma da ta fita ko nan da gate Marainiyar" Abba da ya mike shi ma yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"