← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 251 OF 313

Sashe 251

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ur evidence via 07087865788 Mikewa MD yayi ya jingina da bango yana kallon Dr Khalil dake kallonsa, Calmly yace "She is on her way with Medical Toxicologists, try convincing them" Dr Khalil dai yayi shiru yana kallonsa ganin yanda duk ya fara fita hayyacinsa, maganar ma kamar yana forcing kansa ne yake yi, Dr Khalil ya kwantar da murya yace "MD ka je ka huta, i will remain here...m" MD ya koma ya zauna yace "Pls kayi ma Abban nata bayanin da nayi maka yanzu..." After some seconds Dr Khalil ya juya ya fita, mikewa MD yayi yana kallon Mayraah that is on Medical Ventilator, walking slowly ya isa kusa da ita ya duka ya kamo hannunta yana kallonta a hankali yace "I know you are strong, and u are gonna make it in sha Allah, you have many years and a bright future ahead, come back pls" gently yake murza fingers dinta yana kallonta, yayi hakan for almost 5 minutes sai kuma ya daura kansa saman gadon ya lumshe ido. Maheer na isa gida, Haseenah dake kwance dakinta har ta fara bacci amma jin an bude kofa ta farka tana kallon agogo taga karfe hudu da yan mintuna, sauka tayi daga kan gadon ta fito dakin da sauri, a corridor ta hadu da shi zai shiga nasa dakin, da damuwa tace "Wai me ke faruwa ne Maheer? Bilkisu tace min Mayraah ba lafiya an tafi asibiti, kuma kafin inje dauko hijab har sun wuce ita da Ammi basu jirani ba, yanzu ya jikin nata?" Maheer da ya bude kofar dakinsa yace "Da sauki" Daga haka ya shiga dakin ya kulle kofar, Haseenah sai da taji kanta ya wani sara jin yace da sauki, wato da sauki?? ita da take ta jiran a dawo da gawan Mayraah ana koke koke, meye kuma da sauki? nan da nan taji ranta ya wani baci, shkkn wannan poison din da ta samu da kyar da siddin goshi ya tashi a banza a iska kenan, tun a kano take adana poison din nan ta rasa ta yanda zata saka masa a abinci tunda ba cin abinci yake a inda take ba sai can wajensu Ammi, ko shayi baya sha a Chalet shi yasa har suka taho Abuja bata samu daman aiwatar da nufinta a kansa ba, rai bace ta koma dakinta ta zauna gefen gado tayi tagumi, amma matsiyaciya ce yarinyar nan duk ta ɓata mata aiki don ba don ita ta saka poison a abincin ba gashi ta ci kuma ance jiki da sauki, Maheer ya sa ma kofar dakinsa makulli ya dauko laptop dinsa da sauri ya fara danne danne zuciyarsa na bugawa, cikin mintuna kadan ya shiga software din CCtv system din parlor da yayi installing a Laptop dinsa, cikin mintuna kadan yayi fast fowarding har zuwa time frame da yake so, ya dinga kallon footage din a laptop din babu ko kiftawa wasu zufa na keto masa a goshi duk da AC dake kunne a dakin, zaunawa yayi gefen gado ya kama kansa da yayi masa nauyi, a ransa ya dinga furta "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" da kyar ya iya mikewa daga karshe yana ganin wani jiri ya kashe laptop din ya dau makullin motarsa ya fita daga dakin yana rike da laptop din nasa, Haseenah na jin ya bude kofar dakinsa ya fito ta sake tashi ta fito daga nata dakin da sauri, bai yarda ya kalleta ba ta bi sa a baya da damuwa tana cewa "Don Allah in sa Hijab mu je asibitin Maheer?" Ba tare da ya juya ba yayi calming kansa ya dake yace "Aa, gobe za a sallameta in sha Allah" Haseenah ta kasa cewa komai ga dinga kallonsa har ya nufi kofa, bata taɓa jin tayi aikin banza aikin hofi a rayuwarta ba irin yau, wato har za a sallamota daga asibitin, ko dai shaka kawai tayi bata ci poison din ba, har Maheer ya fita parlon bata ce masa komai ba tsabar bacin rai, can ta ja wani dogon tsakin takaici ta koma dakinta tayi banging kofar tana tunanin what step next, Maheer ya fi minti biyar cikin motarsa ya hade kansa da Steering yana sauke numfashi a hankali zuciyarsa na bugawa, he wish shi ne ya ci abincin nan ba Mimi ba, he can't imagine loosing Mimi a duniyar nan, da kyar ya composing kansa ya fita daga compound din, driving kawai yake as if he is learning don gaba daya hankalinsa baya jikinsa, ikon Allah kawai ya kai sa police station. Abba da ya dafe kansa ya kasa ce wa komai ga Dr Khalil dake ta kokarin convincing dinsa a kan barin Mayraah har Ceo dinsu ta iso, shi bai ki ya sadaukar da every of his wealth wajen ceton ran Mayraah ba, ya dago kansa ya jinginar da kujera, Dr Khalil could see how devastated he is, trying so hard to calm him duk da shi ma yana cikin damuwar nan don he can't imagine Mayraah giving up, ya kwantar da murya ce "In sha Allah da kwararrun Medical Toxicologist zata shigo kasar, kar ka manta Mayraah staff dinmu ce Alhaji, our Ceo will definitely do what ever it takes na ganin mun ceto rayuwarta idan Allah ya amince, Ceo dinmu na aiki a kasashe sun fi hudu as a medical expert a duniya, sannan tana daukan masu PHD da masters a jami'ar Uk" Abba na kokarin controlling kansa yace "Nan da awa nawa zata shigo kasar Dr?" Dr Khalil yace "Daga UK zuwa Nigeria awa shidda ne da rabi or so, muna sa ran nan da karfe takwas na safiya suna kasar nan in sha Allah, ai tun dazu suka taso" Abba ya mike yace "Ina son ganin daughter ta, a bar ni in ganta don Allah" Dr Khalil ya girgiza kai calmly yace "Kayi hakuri Alhaji, bazai yiwu ba a yanzu... Kayi hakuri" Dr Khalil na fadin haka ya juya ya bar wajen Abba ya bi sa da kallo looking so confused. Haseenah na kwance ta fara bacci bayan anyi sallan asuba ta bude ido jin an bude kofa a parlor, taɓe baki tayi ta gyara kwanciyarta don ko fita ma bazata yi ba, ji tayi an kwankwasa kofar dakinta, ta mike zaune cike da mamaki tana kallon kofar, to ko ce mata zai yi su tafi asibitin, ikon Allah wai Maheer ne ke mata knocking yau, yaushe rabo?? Sauka tayi daga kan gadon ta karasa bakin kofar ta bude, sai da zuciyarta ya kusa shigewa cikinta ganin yan sanda hudu bakin kofar, ta wani gwalo ido tace "Lafiya? Daga ina haka? Wa ku ke nema?" Wani ɗan sanda ya ciro handcuff yana nuna mata yace "You are under arrest" A gigice tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ban gane under arrest ba? Me aka yi? Ko dai batan hanya ku ka yi ba gidan nan zaku shigo ba? Matar aure ce fa, gidan mijina ne nan...." Makalewa maganganunta suka yi ganin Maheer dake tsaye yana kallonta cike da takaicin ranan farkon haduwarsa da Haseenah, Ta hadiye abu da kyar tace "Maheer lafiya? Me ke faruwa? Wa su ke nema haka?" Maheer na girgiza kai zuciyarsa na masa zafi yace "I regret the very first day i met you, nayi da na sanin haduwa dake a rayuwata har na aureki, marrying you was the worst mistake i made in this life, poison kuma kamata yayi ace wanda zan shaka kika nemo ba wanda zaki zuba a abinci har kanwata ta ci ba, ni kika yi niyyar kashewa, da cikin sauki wa enda suka baki wannan deadly poison din za su iya baki wanda zaki shaka min, Haseenah u will surely pay for this, all this while Ina zaune da ke ne ba don na yarda dake ba sai don yi ma mahaifiyata biyayya, sannan ita da ta saka in ci gaba da zama dake har zuwa wani lokaci ita ta bani shawaran saka Cctv a parlon nan to be watching ur movement don haka na sake ki saki biyu, there is nothing left between me and you again, i dissolve our marriage this very moment" Haseenah taji kafafuwanta sun kasa daukanta, wasu zufa suka dinga keto mata ta ko ina a jikinta tun da ta ji ya ambaci cctv camera, durkusawa tayi a kasa ba tare da tasan tayi hakan ba ta fashe fa wani matsanancin kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku na lalace" Tsawa ɗan sandan ya daka mata ta mike da sauri duk jikinta na rawa, ya saka mata handcuff din a hannu suka kadata zuwa cikin parlor tana rusa kuka, da sauri ta tafi gaban Maheer ta durkusa bakinta na rawa cikin kuka tace "Maheer kar ka manta ɗanka dake cikina...." Ko rufe baki bata yi ba ya hade fist dinsa ya sauke mata dai dai bakinta da duk strength dinsa lkci daya kuma ya wanka mata wani wawan mari da sai da ganinta da jinta ya dauke na wasu dakikai, hakan bai yi ba ya wani haureta da karfi da kafarsa, ji tayi kamar hakorinta ya fado kan harshenta, ta zaro ido ta tofar kasa taga aiko hakorin nata ne kuma na gaba ya cire tsabar kullin da ya kai mata a baki, tuni jini ya fara bulbulowa, wani ɗan sanda ya dafe Maheer trying to calm him down yace "Kar kayi laifi Yallabai... Ka riga ka damka ta ga hukuma, so this is not accepted...." Daga haka suka kada Haseenah da jini ke ta zuba a bakinta suka fitar da ita daga parlon tana rusa ihu tana kiran Maheer, Maheer ya duka nan parlon ya dafe kansa lokaci daya idanuwansa suka kada. Da safe sai da aka yi admitting Ammi a asibitin don collapsing tayi a reception jininta ya hau sosai, bayan an kara mata ruwa Dr Hamid yayi mata alluran bacci sannan ya bar Abba a ward din ya fita, Maheer dake zaune corridor din IC unit ya rike kai, tun dawowarsa asibitin yake wajen a zaune likitocin sun ki bari ya shiga, ya dago da sauri jin an bude kofa, mikewa yayi da sauri ganin Dr Balogun ya karasa gun sa duk da Dr Balogun bai tsaya ba balle ma ya kallesa haka ya dinga
Chapter 251 · 0% Book details