← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 143 OF 313

Sashe 143

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake.* [7/13, 6:11 PM] Khaleesat Haiydar💖: Karfe goma saura Abba ya zo asibitin duba Mayraah, tana zaune kan gado da fruits a gabanta an sa mata wani drip din don wancan ya kare, Ta daga kai tana kallon Abba dake tambayarta ya jikinta tace "Da sauki Abba" Yace "Are you sure?" Ta gyada masa kai, yace "Toh Allah ya kara afuwa daughter" Mama Ladi tace "Yo jiya ina ma ta samu sararin shan kankana da su lemo, jiki ai yayi sauki Mamuda" Abba yace "Gaskiya ne, yanzu zaki tashi in maida ke gida kema kiyi wanka ki huta kiyi bacci Mama, ita kuma Hajiya Amina ta zauna nan da ita zuwa anjima...." Mama Ladi ta katse sa tace "Aa ai ba cewa nayi na gaji da jinyan ba Mamuda, ita Aminar ta koma kawai ko girki ne sai tayi ta kawo mana" Abba yace "Aa da dai mun tafi gida kin huta Mama" Mama Ladi tace "Na fa ce kar ku damu da wai ban yi bacci ba, na saba da irin wannan jinya a asibiti, idan Aminan ta kawo abincin anjima muka ci sai a maida ni gida inyi wanka, in ba a sallameta ba har zuwa dare sai a dawo dani nan wajenta" Abba yace "Toh shkkn" Hajiya Amina na kallon Mayraah tace "Allah ya kara lafiya dear, anjima zan dawo in sha Allah" Kai kawai Mayraah ta gyada mata, Hajiya Amina tayi ma Mama Ladi sallama sannan suka fita da Abba, Mama Ladi ta jawo sauran ƙwan da ke cikin warmer da Mayraah ta ki ci ta fara ci. Mayraah na kwance wajen karfe sha biyu da rabi ta kalli Mama Ladi dake shan lemon ɓawo tace "Mama, yaya ya zo ina bacci ne?" Mama Ladi tace "Waye kuma yaya? Mashir ko Usman?" Mayraah ta gyada mata kai, Mama Ladi tace "Yanzu lemon nan da nake sha nazarin da nake kenan a raina wallahi, ai baza su ce basu ji baki da lafiya ba kina asibiti tun da tun a jiyan da ake ta neman inda kika tafi har Mashir sai da Mamuda ya kira aji ko kin je gidansa Mashir yace a'a baki je ba, ai idan ya damu da sai ya zo gidan a daren da yaji ba a ganki ba amma wallahi bamu ga ko keyarsa ba, tun da garin Allah ya waye nake zuba ido in ga shi ko Usman sun zo duba ki shiru har yanzu ana neman karfe sha biyu, babu shi, babu Usuman din balle uwa uba kafurar nan don ni dai na fara tunanin anya Ammi musulunci take kuwa, kai kamar fa bata cikinmu yanzu gaskiya, ke ki ga fa sai wani bare can da kawai taimakonki yayi ya kawo ki asibiti ke ta sintirin shigowa duba mu kamar wasu marasu galihun dangi, jiya ma sai da na kore yaron wajen karfe sha biyun dare sannan ya tafi, kina ganin yau da sassafe kuma sai gashi, ga yaron kyakkyawa da shi kamar bafillatani ne ina ji, to daga shi sai Mamuda da sabuwar amaryarsa kadai ke zuwa mana, ma'aikatan asibitin ba sai suyi tunanin bamu da dangi bane" Ko rufe baki Mama Ladi bata yi ba aka bude kofar ward din ta daga kai da sauri, Musharraf ne ya shigo da sallama with basket of food, Mama Ladi ta gyara zama ta ajiye bawon lemon hannunta tana ɗan murmushi tace "Sannu da zuwa" Ya ajiye abincin ya gaisheta, ta amsa da fara'a tace "To wai ya ma sunanka ne?" Yace "Sunana Musharraf" Mama Ladi ta gwalo ido tace "Musharri? Sharri fa kace?" Mayraah ta kauda kai ta ɗan yi murmushi, Musharraf ya sunkuyar da kansa yace "Abdallah ake kirana" Mama Ladi tace "Ayyo, har hankalina ya tashi, to sannu da zuwa Audullahi, naji dadin yanda ka nuna ka damu da jikata daga taimako, Allah ya maka albarka" Ya ɗan yi murmushi yace "Ameen" Mama Ladi tace "Dama ina ta jiran wanda zai zo nima in ɗan samu in fita in ɗan motsa kafafuwana, tun jiya mutum na waje daya kamar gunki kada jini ya daskare min" Daga haka ta mike tana yafa gyalanta ta nufi kofa, Musharraf ya nufi Mayraah bayan ta fita yana kallonta yace "How are you feeling now dear?" Ta gyada masa kai kawai, yace "Ba inda kike jin ciwo?" Nan ma ta gyada masa kai, yace "Mami ta bada abinci a kawo maki, zata zo dubaki nace mata ba sai ta zo ba" Mayraah ta sunkuyar da kanta a hankali tace "Nagode" Hannu zai kai goshinta ta kauce da sauri, yayi kasa da murya yace "I just want to feel ur temperature" A takaice tace "Don't worry, i felt it my self minutes ago" Bai sake cewa komai ba ya zauna kan kujera, yace "Ammi bata nan ne? Naga ban kanta ba har yanzu" Mayraah ta gyada masa kai kawai, sai kuma ta kwanta ta juya masa baya don bata son zancen, a hankali Musharraf yace "Thursday za ku yi Internal Defense, but u need not to worry about that, external din ma kar ki damu i will sort it out, kina bukatan hutu sosai yanzu" Murya can kasa Mayraah tace "Thank you" shi dai kallonta kawai yake don har a lokacin bata juyo ba, ko minti biyar ba ayi da fitan Mama Ladi ba sai ga ta ta dawo tace "Toh Alhamdulillah na zaga har na dawo" Musharraf yace "To sannu da dawowa Mama" Mama Ladi tace "To amma na fa ji ana ta kiran sallah a masallaci" Mikewa yayi yace "Eh yanzu zan tafi" Tace "To maza ka tafi" yana fita Mama Ladi ta hau bude abincin da ya kawo, buda baki tayi tace "Kai kai kai, wannan abinci haka kamar a gidan sarauta" sai kuma tayi murmushi ta kalli Mayraah tace "Za ki ci ne?" Mayraah tace "Na koshi" Mama Ladi bata sake bin ta kanta ba ta dau plate ta fara zuba abincin ta tula nama ta koma ta zauna tana ci. Throughout ranan daga Mama Ladi, Hajiya Amina sai Musharraf idan ya shigo ne kadai ke tare da Mayraah a asibitin, wajen karfe uku na yamma 3 of her lecturers tare da Dr Asmau suka zo dubata a asibitin da ledan fruits, Mama Ladi sai sa masu albarka take bayan Mayraah ta sanar mata malaman makarantansu ne har suka tafi, Sai a sannan Mayraah ta koma ta kwanta da tunani iri iri cike fal ranta, she felt so relieved da ta tuna bata da wani issue na project da defense a yanzu kuma, she will just assume ta gama kawai. karfe uku da rabi Hajiya Amina ta koma gida don yin girkin dare ta kawo masu, sai bayan da suka fita Mama Ladi ta rike kanta tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah wadaran Ammi, Allah wadaran kafirin zuciya irin nata, wato har 'ya yan ma ta hanasu zuwa kenan, magana na ta ci na ba daman inyi gaban wannan baiwar Allah dake ta hidima da mu a asibitin nan taje kawai ta raina mu, Kaiii a gaskiya Mamuda bai yi dacen uwar gida ba bazan ci amana in ki fada ba gaskiya" Ita dai Mayraah na kwance bata ce komai ba banda ɗan murmushi da tayi, Mama Ladi ta ciro wayarta da aka nannade da rubber band ta mika ma Mayraah tace "Kira min Mashir din" Mayraah ta kalleta, a hankali tace "Me za ki ce masa Mama, kawai ki..." Katseta Mama Ladi tayi a fusace tace "Ina ruwanki? Ke dai ba kawai cewa nayi ki kira min shi ba ki miko min" Mayraah ta amshi wayar tayi dialing number Maheer ta mika ma Mama Ladi da ta danna handsfree, sai da ya kusa katsewa ya daga, Mama Ladi bata amsa sallamansa ba tace "Mashir wai baka da labarin an kwantar da kanwarka tun shekaranjiya yau kwananta uku kenan a asibiti?" Maheer ya ɗan yi shiru sai kuma yace "Ai bana gari" Mama Ladi tace "Baka gari? To shi Usuman shi ma baya gari da wannan farin yaron da ya dawo jiya?" Maheer yace "Gaskiya ban sani ba" Mama Ladi tace "Toh ko da baka gari ai sai ka kira kace a baka Meran kaji jikinta, yarinyar da aka kawo asibiti bata numfashi sai da kyar yau ta fara numfashi amma duk cikin kai da yan uwanka babu wanda ya zo dubata?" a hankali Maheer yace "Aiki naje ne Mama" Mama Ladi tace "To ba laifi" Daga haka ta ba Mayraah wayarta tace "Kashe min" Mayraah ta amsa ta katse sannan ta mika mata. Karfe shidda saura likitan ya shigo daki zai sallami Mayraah, Mama Ladi tace "Kar fa mu koma gida jikin ya kara rikicewa dafta, ni dai ina ga gwara a bari a ga zuwa gobe tukun" Likitan na murmushi yace "Jinin nata ya dawo normal Baaba, kawai magunguna zata ci gaba da sha, da kuma wasu cimar da zata maida hankali gun ci yanzu, duk na gaya ma Abbanta" Mama Ladi tace "Toh shikenan, amma ai uban bai san za ayi sallama ba yau, ga abinci can anje gida za a kawo mana kuma" Likitan yace "Bamu jima da gama waya da shi ba, yace zai zo bayan magariba ya tafi da ku gida" Mama Ladi tace "Atoh shikenan ba damuwa, Allah maka albarka" Likitan yace "Ameen Baaba" Ya maida dubansa kan Mayraah yace "Allah ya kara afuwa yan mata" A hankali tace "Ameen Nagode" Juyawa yayi ya fita, Mama Ladi tace "To kuma idan muka tafi wannan malamin ya kara kawo abinci fa, kar fa asa yaje yayi asaran abinci da sun bari can bayan isha'i a sallame mu" Mayraah dai kallon Mama Ladi kawai take, don tayi nisa tunanin da take bata ma san me Mama Ladi take cewa ba, Bude kofar aka yi Musharraf ya shigo Mama ladi tace "Kaga ɗan halaq yanzu nake maganarka nace kar kuma ka zo
Chapter 143 · 0% Book details