Sashe 231
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dai hankalina bai kwanta ba kwata kwata, yaushe ma ta fara aikin ta samu full experience har matar zata ce xa aje conference da ita England? Ina manyan likitoci da Nurses din asibitin, aa gaskiya bazata ba" Maheer ya sauke ajiyar zuciya yace "Kai ya ka gani Barrister?" Sai a sannan Usman ya daga kai ya kallesu yace "It's weird gaskiya, daga fara aiki ko sati biyu bata yi ba a kawo maganar fita waje, irin wannan tafiyar ai da experienced staffs ake zuwa" Maheer yace "Haka ne, nima kuma nayi mamaki" Ammi da hankalinta ya tashi tace "Ni gaskiya aikin ma sai a bari, kuma fa matar ba musulma bace, gwara a samar mata a wani waje kawai ta hakura da wannan" Murmushi kawai Maheer yayi, Ammi tace "Abbanku da na dawowa yau zan gaya masa, aikin ya fita kai na gaba daya wallahi" Mikewa Usman yayi ya fita daga parlon, Ammi ma ta mike tace "Kasan zan yi bakuwa bari in je in ga ko me aikin ta gama abinda na sa ta" Yace "Ohk" Ammi na fita parlon Maheer ya mike ya tafi dakin Mayraah. Kusan karfe uku Hajiya Maimuna mahaifiyar Haseenah ta iso gidan, tun da ta shigo hankalin Haseenah ya ki kwanciya, kawai dai tana zaune parlorn ne tana yaken karfin hali, Ammi ta tarbeta sosai suka gaisa da fara'a, Mayraah ta kawo mata abincin da aka mata, Hajiya Maimuna tace "Kawai na ce ko a gurguje ne in zo in ga gida kafin in koma kano, gida kam Alhamdulillah yayi kyau Allah ya sanya alkhairi, Allah ya sa rai aka yi ma" Ammi tace "Ni da na zata kwana za ki yi Hajiya?" Hajiya Maimuna tace "Ai daga gidan nan airport zan tafi, biki muka shigo tun ran juma'a wallahi, to nayi niyyar zuwa jiya asabar sai Allah bai yi ba sai yanzu" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Toh amma ai za ki ci abinci Hajiya" Hajiya Maimuna tace "Wallahi na ci abinci kafin in fito, Alhamdulillah" Ammi tace "Da kika kirani dazu da safe har nake tunanin in kin zo akwai maganganun da za mu yi Hajiya" Sosai gaban Haseenah yayi mugun faduwa jin abinda Ammi tace, Mayraah dai na zaune parlon ita ma, Hajiya Maimuna tace "Flight din na dare ne Hajiya, ko yanzu za mu iya maganar, Allah dai ya sa lafiya" Ammi ta ɗan yi murmushi, sai kuma tace "To gaskiya ba lafiya ba Hajiya" Hajiya Maimuna tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ina ji Hajiya" Haseenah ta mike zata bar parlon, Ammi tace "Aa ki dawo ki zauna Haseenah" Sunkuyar da kai tayi ta koma ta zauna, Nan Ammi ta fara yi ma Hajiya Maimuna bayanin duk abinda ke faruwa bata boye mata komai ba, Daga karshe Ammi tace "Nasan kin san wasu maganganun nan wasu kuma ba lallai ki sani ba... To kin ji abinda ake ciki Hajiya" Hajiya Maimuna da ta kasa dago kanta sai zufa take bayan few seconds, tace "Amma baki kyauta min ba Hajiya, wallahi baki kyauta min ba, yanzu duk abubuwan nan su faru babu wanda ya sanar min, na kwanaki ma da tayi dambe da kawarta Badiyyah banda ta kira kannena suka je suka yi rashin mutuncin da suka yi babu yawuna wallahi ban sani ba Hajiya, ban san komai ba, yanzu ni Haseenah zata tona ma asiri ta kunyata ni a idon duniya duk zatona tana zaune lafiya gidan mijinta?" Sai kuma ta fashe da kuka ta mike tace "To wallahi Allah ya isa tsakanina dake Haseenah, kin cuceni don sai ace tarbiyar da na maki kenan, bayan Allah na gani nayi iya bakin kokarina ganin na maki tarbiyyar da ya kamata dai dai gwargwado" a fusace ta rufeta da mari ta ko ina tana zaginta, Ammi ta rikota da sauri tace "Aa Hajiya ba sai kin doketa ba, don Allah kiyi hakuri...." Hajiya Maimuna na huci tace "Wallahi dama in ta kashe auren ta nemi gidan wata uwar ba ni ba, kar ta kuskura ta nufo inda nake, da dadi ba dadi haka nayi hakuri a gidan ubanta har mutuwa ta rabamu ban taɓa yaji ba wallahi komin tsanani kuwa, shi kuma Maheer saboda me zai zauna yana hadiye wannan takaicin ya kasa sama ma kansa mafita ya kara aure tunda Allah ya rufa masa asiri, Kishiya kawai zai mata ya tattara ya koma wajen amaryar, kai ni ko yanzu ya saki Haseenah bazan ce masa don me ba don naga kokarinsa ya kuma nuna shi cikakken namiji ne, ina kuma me bashi shawara ya kara aure cikin gaggawa don huce wannan takaicin" Ammi tace "Yanzun ka akan maganar auren ake, don bazan boye maki ba aure xai kara nan ba da jimawa" Hajiya Amina tace "Toh maa sha Allah, Allah Ubangiji ya masa albarka wallahi" Kuka kawai Haseenah take kamar ranta zai fita bayan ta gudu bayan kujera, Hajiya Maimuna ta dau jakarta tana kallon Ammi tace "Duk hukuncin da ku ka ga ya dace ku yanke a kanta ni babu abinda ya sha min kai, ko me ku ka yi dai dai ne wallahi, kuma nayi da na sanin haihuwar Haseenah" Kofa ta nufa tana huci, Ammi ta bi bayanta tana kokarin dakatar da ita Hajiya Maimuna tace Airport zata kawai, a haka ta bar gidan ko minti daya bata kara ba, babu abinda ya tsaya ma Haseenah a rai take kukan da take sai auren da Mumynta tace Maheer ya kara har Ammi na cewa nan ba da dadewa ba zai yi auren, wato nan ba da dadewa ba zai auri Mayraah don karshenta kenan, kuma tayi mafarkin aurensa da Mayraah yafi a kirga a yan kwanakin nan, goge hawayenta tayi ta fita daga Parlon ta ɗan yi murmushi ta nufi chalet. Da daddare Maheer na parlon Ammi bayan ya gama sauraronta yace "Amma dai don Allah Ammi me yasa za ki ma mahaifiyarta wannan maganar, sulhu ma nake nema da ita kenan? Ni fa Ammi na gama zama da Haseenah wllh tllh, duk wannan maganganun da kika yi ma mahaifiyarta ba shi da amfani don ni dai bazan zauna da ita ba" Ammi tace "Aa gwara dai da na gaya mata Maheer, kaga ko da sakin Haseenah kayi we owe them no explanation afterward, nima ai ban ce za ka ci gaba da zama da Haseenah ba kawai hakkin uwar na fita na gaya mata abinda ke faruwa, saboda kar su mana kallon kananun mutane in suka ji ka saki er su" Abba dake zaune parlon Ammi ya ajiye drink din hannunsa yana kallonta yace "Saboda ance za aje kasar waje da ita sai kice ta ajiye aiki Madam? Ai kamar this is a privilege for her, i see nothing wrong don asibiti ya zabe ta cikin wa enda za su je England conference...." A hankali Ammi tace "Gaskiya ni dai hankalina bai kwanta ba, of all the staffs in the hospital why her? Yaushe ta fara aikin har za a zabeta?" Abba ya kalli Maheer dake parlon yana kallonsu yace "Can you hear ur mother?" Murmushi yayi yace "Kuma conference din nasan bazai wuce kwana biyu zuwa uku ba fa Ammi" Ammi tace "Ko ma kwana daya ne ni dai kawai hankalina bai kwanta ba" Abba yace "Toh tunda haka ne sai Usman ya bi su England din, hope yanzu hankalinki ya kwanta?" Maheer ya juya yana kallon Abba, Ammi ma dai tayi shiru tana kallonsa, mikewa Abba yayi yace "Let me get some rest" Daga haka ya fita daga Parlon zuwa part dinsa, Ammi na kallon Maheer tace "Is there anyway da za a sanar ma asibitin a cire sunanta daga masu tafiyar pls? Wani Usman ne zai bi ta kanta in ma yaje England din, harkan gabansa kawai zai yi ya juyo ranan da yaji ance za su dawo" Maheer yace "Kawai ki bari ta je Ammi, kamar yanda Abba ya fada it's a privilege, don ba kowa ne zai samu hakan ba, may be ita me asibitin ta yaba da nutsuwarta ne sannan taga yanda take aiki, ko kin manta daughter din taki da first class ta fita? Did you know what that means? Kar ki ji komai ana samun haka sosai, beside ba da ita kadai bane ai za aje dole da akwai staffs da aka zaɓa, it's something we should be happy about" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Toh shikenan tunda ka ce haka" Mayraah na dakinta da daddare bayan tayi shirin bacci Ammi ta shigo da sallama, zaunawa Ammi tayi gefen gadon tana kallonta tace "Ya ciwon kan?" Mayraah tace "Yayi sauki tun dazu Ammi" Sai kuma ta marairaice tace "Stress din aikin nan ne fa Ammi, kullum da sassafe mutum zai fita bazai dawo ba sai 6:30, and every day the hospital is always busy with patients, ko lokacin hutu fa mutum bashi da" Ammi tace "A haka nan zaki saba daughter" Mayraah ta girgiza kai tace "Gashi kusan 5 weeks har yanzu ban saba ba, meaning bazan iya sabawa ba" Ammi tayi murmushi don kusan kullum sai tayi complain din zuwa aikin nan, Ammi tace "Toh yanxu yaushe ne tafiyar ta ku? You said ur Visa is ready" Mayraah tace "Nima ban sani ba, but naji kamar Dr Khalil yace next week" Ammi tace "To Allah ya kai mu, abincin da kika girka ma yayan naki ya kare ne?" Mayraah tace "Za ki ci ne Ammi?" Ammi tace "In zan samu ba" Murmushi Mayraah tayi tace "Akwai sauran kadan, bari in debo maki" Sauka tayi daga kan gadon ta fita daga dakin Ammi ta bi ta da ido, magana take son mata amma ta rasa ta inda zata fara, can ta sauke ajiyar zuciya still thinking of where to start from, Mayraah na sauka kasa taga Maheer parlon yana kallo, tun da ya dawo Abuja daga kano yau kusan 4 weeks kenan bacci ne kawai ke kai sa chalet shi ma wajen karfe dayan dare wani lokacin, yana dawowa aiki main building yake nufowa, komai a dakinsa da ke nan main building din yake yi, duk aka yi girki mai aikin Ammi ke kai ma Haseenah Chalet, wani lkcn ta kan shigo babba parlon gidan wataran ma kwata kwata bata shigowa tana can chalet ita