← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 313

Sashe 93

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

what?? Gwara da haukanki ke tsayawa iya kaina Haseenah, don daga sanda kika yi gigin fara yi ma Mimi to za a ji kanmu gaskiya, ni za ki min inyi hakuri in shanye amma wllh kar ki kuskura ki ce za ki yi mata, ni ki ci gaba da min kawai i will endure, zan kuma ci gaba da baki hakuri" Yana kai wa nan ya dau makullin motarsa ya fice daga dakin ta bi sa da kallo baki bude.... Mayraah ta fito kitchen kenan da plate din kazarta da tayi warming, ganinsa a parlon tace "Yaya are you going to work?" Yace "Yea, u need anything?" Shiru tayi tana kallonsa, yace "Ko za ki je asibitin?" Gyada masa kai tayi, yace "Ohk, i will wait for you je kiyi breakfast dinki" Tace "Okay" Daki ta koma ya zauna parlor yana jiranta, Kuka wiwi Haseenah take a daki kamar ranta zai fita, yau kawai ji tayi da za a bata wuka wllh zata iya caka ma Mayraah ta huta, yanzu duk hakuri da ƙauda idon nan da take kamar yanda Salima tace ance tayi ya tashi a banza kenan, ita fa ba don umarnin Salima ba kilan da tuni tayi ma Mayraah duka a gidan duk abinda zai faru ya faru, amma ance ta bi komai a hankali, to tana ta kokarin kai zuciyarta nesa gashi yanzu rainin wayon da ake mata ma gaba yake yi maimakon baya, tana jin fitar motar Maheer a gidan ta fito da sauri tana huci ta shigo parlor tana leka compound ta tabbatar eh ya fita tunda taji ai yana cewa Mayraah baza ta makaranta ba, dawowa tayi ta koma kofar dakin Mayraah ta murda ta ji a kulle, kundume kundumen zagi ta fara tana jijjiga kofar kamar zata balla tana cewa "Shegiya tsintattciya mara asali ki bude kofar mana kiga ikon Allah yau, wallahi sai dai wata ba ke ba a gidan nan, hakurin da nake yi ya ci kaza kazansa, an daina hakurin daga yanzu, wallahi sai na canza maki kamanni ta yanda baza a gane ki ba yau" Bata fasa jijjiga kofar ba tana kundume kundumen zagi duk zaton ta Mayraah na ciki, kamar mahaukaciya ta fita daga gidan ta zaga bayan windown dakin Mayraah nan ma tana bubbuga glass din ta dinga cewa "Don kaza kazanki ki fito mana ki ga aiki da cikawa" Ta gama zuba haukanta ta koma ciki sai a sannan ta lura da babu takalmin Mayraah a bakin kofa, da sauri ta koma gun mai gadi tana tambayarsa ko Maheer kadai ya fita nan ya sanar mata ai har da karamar Hajiya, komawa ciki tayi ta baje a parlor ta dinga rusa kuka, wallahi Salimah ta cuceta da fa yanzu an wuce wajen, kilan da har an samar ma Mayraah wani wajen zama amma ba nan ba, daki ta koma ta dau wayarta ta kira Salima taji a kashe, ta zauna gefen gado tana kukan baƙin ciki da takaici, wata zuciyar ta raya mata to ko dai asibitin zata bi su ne, wani yace mata a'a a gida ya kamata ayi duk abinda za ayi a wuce wajen, ta share hawayenta tana nazari iri iri a ranta bata taɓa shiga bacin rai da baƙin ciki irin wannan ba, wayarta ne ya fara ring ta jawo da sauri a tunaninta Salimah ce, sai ta ga kawarta ce Zaliha, yanda take da Badiyyah haka take da Zaliha duk bata wani yarda da su ba bata gaya masu sirrinta, ta daga wayar ta kai kunne Zaliha tace "Meye duniya Haseenah daga aure sai kiyi watsi da mu ki canza layi?" Haseenah ta sauke wani ajiyar zuciya tace "Ba haka bane Zaliha ina cikin damuwa da tashin hankalin da baza ki gane ba, kuma ban canza layi ba wani lokacin kashe wayar nake ko zan samu sassauci" Zaliha tace "Ikon Allah, me ke faruwa Haseenah? Kuma gashi da yau zan zo gidanki, shine ma nace bari in gwada layin ki yau" Haseenah ta ɗan yi shiru sai kuma tace "Ke da wa za ki zo?" Zaliha tace "Ni kadai ce, yanzu haka ma na shirya wllh" Haseenah tace "Toh zan gaya ma mai gadi ya bude maki gate, sai kin zo" Zaliha tace "Toh shkkn, sai na iso" Haseenah na katse wayar ta fita zuwa gun mai gadi tace "Musa zan yi bakuwa idan ta zo ka bude mata gate" Yace "Toh Hajiya" Juyawa tayi ta koma ciki, wajen karfe sha biyu saura tana zaune parlor har sannan ta kasa shan ko ruwa, warmers din da ta ajiye na breakfast da tayi har sannan suna tsakar parlon taki kwashewa, knocking din kofar parlon ta ji anyi ta mike tana kallon agogo ta karasa ta bude kofar, sai da cikinta ya kusa shigewa cikinta ganin Badiyyah da Zaliha a tsaye bakin kofar....
Chapter 93 · 0% Book details