Sashe 136
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
naki bane" Daga haka ta bar dakin, Ammi ta fito tare da last box dinta, tana ganin Abba cikin bacin rai tace "Me ka biyo ni nan ka gaya min kuma? Dama in kasan ba takardata ka kawo min ba ka tashi ka fita bana bukatar ganinka, takardan kuma in ma kaki badawa to za mu hadu a kotu ne" cikin tsawa Mama Ladi ta kunduma mata zagi tace "Takardan uwaki? Baki san gidan mijin shine rufin asirinki ba gode gode dake? A baki takardanki ki tafi ina wai? Ai yanzun ma kawai kin hada akwati ne a banza don in har na isa dake to babu inda za ki, kin dawo dakin ki kenan, don mu ba kananun mutane bane, kuma mu ba gantalallu yan iska bane" Cikin kuka Ammi tace "Wallahi ban dawo ba Mama Ladi don minti biyar bazan kara a gidan nan ba, Maheer ne kawai ya cuce ni ya takura rayuwata na dawo banda haka wallahi har abada ni da gidan, kuma a yanzu zan sake komawa inda na fito ya zauna da warce ya auro, idan nayi masa halacci a rayuwa zai sani wataran...." Mama Ladi tace "Kaji mahaukaciya, to wallahi ko Hajja bazata maki baki ya kamaki ba kamar yanda ni zan maki ya kama ki, tunda naji ance ranan gobe kiyama ma ni zaki gani ba Hajja ba, haka dai naji ance, don haka in kin isa ki fita gidan nan mu ga, tun farko da kin ji ta nawa ai da duk haka bai faru ba Ammi, kishiya kuma dama nace masa baza ki zauna da ita ba, in ma ta bar maki gidan ya kama mata haya ko kuma ke ki bar mata gidan ya gina maki wanda yayi ukun wannan, ai shi Mamudan ba ɗan iska bane yasan abinda ya kamata..... Karfe biyu saura Mama Ladi ta sauko downstairs daga part din Ammi duk ta hada zufa tsabar sulhun da take ta kokarin yi tun karfe sha daya take abu daya har yanzu da ta fito shi ma saboda lokacin sallah ne yayi Mamuda zai je masallaci, tana fifita da gyalenta cikin bacin rai tace "Tirrrr, tunda uwata ta haifeni ban taɓa kai wa warka ban ci abinci ba akan abinda bai shafeni ba, tun shayi da ɗan burodi da na ci da safe fa, ita kuma wannan mata Ammi Allah wadaranta, Allah wadaran hali irin nata, don wannan taurin kai ko a kafurai ba a samun me shi gaskiya, kai ko a dabba ma yanzu a daina samun masu taurin kai haka, ni ko nace in ta haifu cikin Sadiya da Ubale ta bar gidan nan taga tsiyar da zan mata wallahi, ita ko ɗan kuturun gidan Hajja bazai sa ta hakura ta zauna cikin rufin asirinta ba, mata sae kace kanwar shaidan don ma Mamudan me hakuri ne, to uban wacece ita da baza a ma kishiya ba ma dai tukun, kishiyar da rubabbiyar uwarta ce ta ja mata kowa ya sani, sam ni Ladiyo bana goyon bayan rashin gaskiya, abinda shegiyar amaryar da ke tafiya tinkis tinkis da duwaiwuka ba kanki zata zauna ba ina ruwanki da ita, to ni dai ba ruwana na daina asaran kudi na kan Ammi, in ma taki jin maganata ta koma kuturun gidan Hajja ni dai ina nan wallahi tallahi" Hajiya Amina ce ta sauko downstairs ita ma, Mama Ladi tayi tsit tana bin ta da kallo, Hajiya Amina tace "A kawo maki darduman nan ne Mama?" A fusace Mama Ladi tace "Ke ni fa ban ci komai ba fa sai ɗan burodi da shayi da safe" Hajiya Amina tace "Toh kiyi sallan zan hado maki abincin yanzu in sha Allah" Mama Ladi tace "Aa bari dai in fara ci don yunwar ta gigita ni wllh, kada inje sallan bai yi dai dai ba" Hajiya Amina tayi murmushi kawai ta shiga kitchen, Mama Ladi ta dinga murmushi ganin uban liyafan abincin da Hajiya Amina ta hado mata kamar wata matar sarki, babu abinda bata taɓa a abincin ba don sai da ta kusa cinye duk abincin tass, ta kwankwade shayi me ƙauri da ta hado mata sannan ta tafi bandaki tayi alwala tana cewa "Alhamdulillah" ko kafin ta fito Hajiya Amina ta shimfida mata dardumanta me laushi da kamshi, bayan Mama Ladi ta idar da sallah ta koma bangaren Ammi tana ta murmushi tunda ta koshi, har a sannan Ammi kuka take a parlor, Aunty Mariya na ta bata baki, Mama Ladi ta kyabe baki ta kishingida kan carpet tana sakace hakori tace "Mariya ga abinci can me shegen dadi Aminar ta dafa da zuka zukan kaji ki rufa ma kanki asiri kije ki deba ki ci kar ya kare, na ji tace har da na Umar Usman yaje daukosa a filin jirgi sun iso" Ko kallonta Aunty Mariya bata yi ba ta koma daki don tuni Ammi ta mike ta shige daki, Mama Ladi tace "Kishiya sai kace kanki farau, abinda na ga Aminar ma na da hankali da biyayya, ina laifin wanda ya mutunta naka, tun dazu take ji da ni a parlor, sai kinga liyafar da ta hada min na abinci ko iya cinyewa ban yi ba, to ni dai ba ruwana wllh..." Mayraah dake kwance ta daga kai tana kallon Hajiya Amina da ta shigo dakinta, mikewa zaune tayi tana kallonta, Hajiya Amina tace "Ko dai baki da lafiya ne Mayraah?" Mayraah ta girgiza kai tana murza ido don ko kallonta bata son yi tace "Bacci nayi" Hajiya Amina tace "It's almost 3pm ki fito ki debi abinci ki ci" kai kawai Mayraah ta gyada mata, ganin Hajiya Amina taki fita yasa Mayraah ta sauko daga kan gadon, har sannan taki yarda ta kalleta, Hajiya Amina ta bude kofar dakin ta fita Mayraah ma ta fito tana tafiya a hankali, ita kanta tasan she is not okay she is just trying to be fine, Hajiya Amina ta shiga nata dakin, Mayraah ta sauka downstairs, tun da tayi ido hudu da Ammi bata sake bude dakinta ba sai yanzu da Hajiya Amina ta shigo, bude kofar parlon aka yi Usman ya shigo Umar na biye da shi da jakansa a hannu, Umar na ganinta ya ajiye jakarsa yana kallonta, can ya nufeta yana murmushi, duk da maganganun da Usman da Maheer suka masa na ringing a kansa hakan bai hanasa rungumeta ba kamar yanda ya saba duk sanda ya dawo, yace "Me kika dafa min Mimi?" Usman dai na tsaye yana kallonsu, Mayraah tayi murmushin karfin hali kawai ta kasa ce masa komai ya daga kanta yace "Are you sick?" Kai ta gyada masa tace "Amma da sauki" bata jira cewarsa ba ta nufi jakarsa ta dauka tace "Welcome back home bro" Daga haka ta tafi dakinsa dake downstairs, Umar ya bi ta da kallo sannan ya kalli Usman, zaunawa yayi kan kujera ya rike kansa, Mayraah na zuwa dakinsa wanda tun da sassafe Hajiya Amina ta gyara masa ta ajiye jakarsa sannan ta fito, bata sake kallonsu ba ta shiga kitchen, Usman ya bi bayanta, yana shiga kitchen din ta juya ta kallesa, yayi kasa da murya yace "Kin shiga kin gaida Ammi?" Ta girgiza masa kai alamar A'a, ya ɗan yi shiru sannan yace "Yanzu me za kiyi?" Tace "Abinci zan zuba ma Ya Umar" Yace "Ke kin ci abincin?" Ta girgiza masa kai, yace "Debi naki kawai ki wuce daki, idan kin gama ci ki tafi ki gaida Ammi" Ta gyada masa kai, kasa cin abincin Mayraah tayi bayan ta deba ta tafi dakinta, can dai ta rufe ta mike ta fita daga dakinta ta nufi bangaren Ammi tana tafiya a hankali gabanta na faduwa, parlor ta bude a hankali kamar me tsoron taɓa handle din, tana shiga Mama Ladi dake ta zuba gyangyadi ta bude ido, gyara zamanta tayi da mamaki tace "Mera? wai dama kina gidan nan?" Mayraah ta gyada mata kai ta zauna kasa cikin sanyin murya tace "Ina wuni" Aunty Mariya da har a lokacin bata gaji da ba Ammi hakuri ba ita kanta tayi mamakin jin muryar Mayraah don ta ma mance ta tambayi Maheer ko ya dawo da ita, Ammi dake zaune gefen gado bata daina kuka ba ta mike ta nufi kofar dakinta ta saka makulli, jikin Aunty Mariya yayi sanyi ta bi ta da kallo, Mama Ladi ta kalli kofar dakin jin an kulle da makulli, taɓe baki tayi tace "Tashi kiyi tafiyarki in baki ci abinci ba ki samu Aminar kice ta baki abinci, ta girka lafiyayyen abinci me kyau, nima ban dade da gama ci ba" Mayraah dai sai kallon kofar dakin Ammi da taji an sa makulli take, Mama Ladi tace "Ko kin ci abincin?" Mayraah bata son taga hawayen da ya kawo idonta ta mike tace "Aa, zan ci yanzu" Daga haka ta juya ta fita ta koma dakinta, fadawa tayi kan gado ta dinga kuka tana jin zuciyarta na mata zafi... Babu yanda Aunty Mariya bata yi da Ammi kan ta gyara mata bangarenta ba don yayi ƙura Ammi ta ki daga karshe ta rufe Aunty Mariya da fada, Aunty Mariya ta ja bakinta tayi shiru.... Wajen karfe shidda Aunty Mariya ta fito rike da handbag dinta da akwatin Mama Ladi tana kallon Mama Ladi dake ta kallon TV a parlor ga bowl din fruits cike a gabanta tana sha, ganin Aunty Mariya ta washe baki, bata ko lura da akwatinta dake hannunta ba tace "Kin ga yanzun nan ta kawo min wannan Mariya, anya kuwa ba er kirki bace matar...." Aunty Mariya ta wani hade rai tace "Za mu koma gidan Hajja ne" Sai a sannan Mama Ladi ta lura da akwatinta dake hannun Aunty Mariya, ta ajiye slice din kankanan hannunta tace "Ajiya kika min a akwatin ne kika dauko min?" Aunty Mariya tace "Ae tashi za ki yi mu tafi magariba ya gabato" Mama Ladi ta matsar da bowl din gabanta kamar zata yi kuka tace "To gidan uwarki na zo da za ki ce in tashi mu tafi Mariya? Ko ina ruwanki da ni fisabilillahi idan ba neman magana ba?" Aunty Mariya tace "Yanzu Mama Ladi ko wani yace ki kwana gidan nan sai ki kwana bayan kin san abinda ke faruwa?" A fusace Mama Ladi tace