← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 189 OF 313

Sashe 189

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

makullin motarsa bayan ya sa masu cartoon a tv dake office din ya kalli Mayraah yace "Ga cornflakes dinsu da abinci a jaka if they need" Mayraah tace "Ohk" fita yayi daga office din zai tafi gidan Aunty Rabi'ah don ya kira Zainab ya fi a kirga bata daga kiran, Da ya kira Ummi kuma normally suka gaisa nan ya gane ba can taje ba kamar yanda ya zarga kawai sae bai ce ma Ummi komai ba, Mayraah bata san yaran are sharp haka ba, don cikata suka yi da surutu ta rasa wanda ma zata amsa cikinsu, bayan tafiyarsa da kusan minti talatin Ashnaah tace "Aunty i want cornflakes" Mayraah tace "Ohk" Ashfah tace "Me too" Murmushi Mayraah tayi ta tafi inda ya nuna mata jakar ta durkusa tana dubo cornflakes din a ciki, bude office din aka yi ta juya da sauri, sosai gabanta ya fadi ganinsa amma lokaci daya ta dauke kai ta ci gaba da abinda take, tana ji ya shigo office din yaran suka je da gudu suka rungumesa ya duka ya ba ko wannensu peck yana kallonsu yana murmushi yace "Where is papa?" Ashnaah tace "He is gone" Yace "And he left u 2 all alone?" Ashfah ta nuna masa Mayraah da ta mike tsaye, ya juya suna hada ido ya wani sha kunu kamar ba shi ke murmushi ba ya mike tsaye ya jefa files din hannunsa kan table din Dr Khalil, tayi gathering courage zata gaishesa taga har ya fice daga office din daga ita har yaran suka bi sa da kallo, tabe baki tayi ta zagayo ta mika ma yaran bowl din cornflakes da ta hada masu. Sai kusan azahar Dr Khalil ya dawo, duk yaran sun yi bacci ta kwantar da su kan kujera, yana shigowa ya ajiye car key dinsa ya sauke ajiyar zuciya yana kallonta yayi kasa da murya yace "Me yasa baki gaida MD ba da ya shigo office din nan dazu, Why pls Mayraah?" Hade rai tayi tace "Ni gaskiya Dr bazan iya aiki a asibitin nan as far as wannan mutumin yana nan, ya tsaneni, how will i greet someone that just disappeared daga gani na, he is just too rude for my liking, sannan ya fiye nagging" Dr Khalil yace "Let me tell u something, in fa kina karkashin mutum dole za kiyi hakuri a rayuwar nan, mu ma nan duk hakurin mu ke, MD is nyc but he have anger issues sannan baya son wasa baya son raini, he is a man of principle, mun yi degree tare da shi ne shi yasa har muka ɗan saba yake daga min kafa a abubuwa da yawa" Da mugun mamaki tace "To asibitin sa ne nan din with his principality?" Murmushi Dr Khalil yayi yace "Ba nashi bane, amma he is the second in command, he is a braniac Mayraah yasan aiki sosai, i think his dad is also a Dr in the US yanzu haka, and he is an only son, dole sai kinyi hakuri da shi, ni ina maki sha'awar son ace kin zama staff a nan saboda zaki ga advantage din hakan nan gaba" Daukar jakarta tayi tace "Tun da ka dawo ni zan tafi" Yace "No, i spoke to him now, zai yi interviewing dinki, he is less busy a office yanzu" Sosai gabanta ya fadi tace "But i am not ready Dr" yace "Dole ayi inputing data dinki yau Mayraah, don gobe me asibitin nan will be around saboda next workshop da za mu je, kin ga idan bai baki employment din ba u are not a staff, sannan babu vacancy, and they will be none anytime soon" Mayraah da taji hankalinta ya tashi tace "To amma wani irin interview zai min, i don't have knowledge of how it is..." Dr Khalil ya katse ta yace "Just compose ur self, u are not dull Mayraah, i know u can do it" Bude drawer yayi ya ciro farin takarda ya mika mata yace "Apology letter, in kinje kin gaishesa sai ki basa hakuri da baki respectfully sannan ki mika masa wannan" Sake baki Mayraah tayi tana kallon takardan, can tace "Apology letter for what? Are we in secondary school?" Dr Khalil ya daure fuska yana kallonta, da tasan stress din da yayi going through yau duk a kanta da bazata ci gaba da stressing dinsa ba ita ma, first yaje shawo kan matarsa duk a kanta, secondly ko gamawa da matar tasa bai yi ba sai ga kiran MD babu abinda ya mance bai gaya masa a waya ba, yana shigowa asibitin yanzu yaje ya samu MD after almost 30 minutes of persuasion ya shawo kansa har ya yarda yayi mata interview din yau and she is here trying to complicate issues the more, Mayraah ta amshi takardan, on a serious note Dr Khalil yace "Mayraah ko zaginki yayi kice kin gode, kuma kar ki kuskura ki fito office din duk ma me zai ce maki" Ta ɗan yi murmushi kawai ta juya ta fita, ya zauna ya sauke ajiyar zuciya a yanda ya lura ma ta fi MD din girman kai amma bata sani ba, Mayraah na tafiya sama ta tsaya kofar office din MD din tana kallon sunan dake manne jikin kofar daga sama.
Chapter 189 · 0% Book details