← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 209 OF 313

Sashe 209

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Mamuda kawai fitowa za kayi kace min kana son ta koma gidan matarka, ba sai ka yi wani corner corner ba, just go straight to the point" Mayraah ta sunkuyar da kanta lokaci daya har hawaye ya kawo idonta, Abba na kallon Mayraah yace "Tashi ki tafi kiyi abinda nace maki" Mayraah ta mike ta juya ta nufi kowa hawayen dake makale idonta ya zubo fuskarta ta fita daga parlon, sai a sannan Ammi ta fashe da kuka ta nufi dakinta, Abba ya bi ta da kallo, sai kuma ya tashi ya bi bayanta, kuka sosai ya sameta tana yi, ya zauna gefen gado yace "Kin ga, babu ta yanda za ayi kice zan raba ki da Mayraah, Mayraah is staying there for just 2 days ta dawo nan..." Cikin kuka Ammi ta katse sa tace "To ban amince ba Mamuda, kuma bazan taɓa amincewa ba, babu inda Mayraah za ta je ai ba wani ɗan iskan ya rainan min ita har zuwa yau ba, ba wani ya sha min wahalanta ba, ba wani ya...." Kasa ci gaba tayi tana kuka sosai zuciyarta na mata zafi tace "Mamuda kar ka sa inji ina dana sanin aurenka, abinda ban taɓa yi ba sai yanzu da aurenmu ya doshi shekaru arba'in, wahalan da na ci a gidanka da irin sadaukarwa ta da abinda zaka biya ni kenan? Is this what i deserve Mamuda? Is this how to pay me? Ko me zan maka na cancanci haka? Me yasa zaka yi saurin mance halacci na gareka? After all my sacrifice yanzu wata from no where zata zo ta fi ni ƙima da mutunci a idonka, wata ce zata zo tayi reaping where she never sowed, ban taɓa zaton haka daga gareka ba Mamuda, kuma a duk zaman mu in dai na cuceka...." Kasa ci gaba tayi tana kuka sosai ta mike ta bar masa dakin kawai, ya sake tashi ya bi ta parlor. Mayraah na dakinta bayan ta ci kukanta Abba ya kwankwasa kofar ya bude, mikewa tayi daga zaunen da take tana kallonsa, Abba yace "Dauko kayanki" Yana fadin haka ya bar bakin kofar, jikin Mayraah yayi sanyi sosai, fitowa tayi daga dakin ta tafi bangaren Ammi, a bedroom dinta ta sameta, Mayraah ta karasa kusa da ita ta zauna ta ma rasa abinda zata ce, Ammi tayi karfin halin cewa "Ki je kiyi yanda Abbanki yace Mayraah" Mayraah ta fashe da kuka tace "Ammi ni bana son in je gidan" Ammi tace "Ran sunday za ki dawo in sha Allah, in ma ba a dawo dake ba zan sa Maheer yaje ya dauko ki, be a good girl kije ki dau kayanki kala biyu" Kuka kawai Mayraah take, Ammi tace "Tashi ki je my dear" Mikewa tayi tana goge hawayen idonta ta tafi ta dau kayan nata kala biyu a karamin jakanta, tana dawowa bangaren Ammi ta tadda Abba a parlon, hakan ya sa ta juya ta fita ta sauka downstairs kawai, bayan kusan minti sha biyar Abba ya sauko yace "Je ki mata sallama ki zo mu tafi, i don't want go miss my flight" A hankali Mayraah ta mike ta wuce sama zuwa part din Ammi, a parlor ta sameta still a zaune, Mayraah ta zauna kasa tana kallonta cikin sanyin murya tace "Ammi don Allah kiyi hakuri..." Sai kuma ta fashe da kuka, Ammi ta dafa kanta tace "Kar ki damu daughter, u are not to be blame, ba komai, ranan lahadi Maheer zai je ya dauko ki" Mayraah ta gyada mata kai hawaye na sauka idonta, Ammi tace "Tashi ki je, idan yayi dropping dinki airport zai wuce" Mayraah ta mike tana goge hawayenta ta nufi kofa Ammi ta bi ta da kallo tana kokarin ganin hawayen da ya taru idonta bai zubo mata ba, Sai da Mayraah ta fara shiga dakin da Badiyyah take, ta duka gabanta tace "Zan je Miller road" Da sauri Badiyyah ta mike zaune ganin jakar hannunta cike da karfin hali tace "Yaushe za ki dawo?" Tana fadin haka hawaye ya cika idonta, Mayraah ta kwantar da murya tace "On Sunday in sha Allah, ba dadewa zan yi ba" Kai kawai Badiyyah ta gyada mata hawaye na sauka idonta, Mayraah ta mike ta fita daga dakin duk jikinta yayi sanyi. Suna isa gidan a waje Abba yayi parking suka shiga ciki, Hajiya Amina tayi farin cikin ganin Mayraah sosai, ganin yanda ta makale bakin kofa tace karaso ciki mana, sai a sannan ta karasa ciki ta xauna, sallama kawai Abba yayi ma Hajiya Amina, tayi amsa addu'an Allah ya tsare ta rakasa har compound ita dai Mayraah na zaune kan kujera makale da jakarta, sabon drivern da Abba ya dauka a gidan shi yayi driving dinsa zuwa airport, Hajiya Amina ta dawo parlor tana kallon Mayraah tace "Tashi mu je ki ga dakin ki" Mikewa Mayraah tayi ta bi bayanta suka tafi sama, Hajiya Amina ta bude mata dakin tace "This is ur room" Mayraah ta dinga kallon dakin ganin tsadaddun furnitures din ciki kamar dakin amarya, sauke kanta tayi kasa ta karasa cikin dakin. Bayan isha Mayraah na daki tana kokarin dialing number Dr Khalil saboda miss calls dinsa da ta gani Hajiya Amina ta shigo, hakan yasa ta fasa kiran, zaunawa gefen gadon Hajiya Amina tayi tana kallonta tace "Abincin ya isheki?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Na koshi" Hajiya Amina tace "To maa sha Allah, ya kika baro su Amminku?" Mayraah tace "Lafiya lau, tana gaisheki" Hajiya Amina tace "Ina amsawa, chatting kike ne" Mayraah ta girgiza mata kai tace "Aa" Hajiya Amina tayi murmushi tace "To yanzu waye surkin namu ne?" Mayraah ta ɗan kalleta sai kuma ta sunkuyar da kai, Hajiya Amina na murmushi tace "Feel free to talk to me dear, i am also ur mother" Mayraah ta ɗan kirkiri murmushi da kyar tace "Aa ba kowa" Hajiya Amina tace "Are you sure?" Mayraah ta gyada mata kai, Hajiya Amina tayi shiru tana kallonta, can a hankali tace "Ni kuma kin san wa nake maki sha'awa Mayraah?" Mayraah ta daga kai ta kalleta ba tare da ta shirya yin hakan ba, Hajiya Amina tayi kasa da murya tace "Yayanki" Mayraah dai ta dinga kallonta tana imagining wani yayan take nufi har ranta bata kawo su Maheer ba fa tunda ita dai tasan ba aure tsakaninsu a mentality dinta, Hajiya Amina tace "Kin ga ya san halinki, ya san wacece ke, kema kuma kin san halinsa kilan har littafi sai ki iya rubutawa akan halayyarsa, you 2 will make a perfect couple Mayraah, beside he is a calm and gentleman" Mayraah ta sunkuyar da kai feeling uncomfortable with the conversation, har cikin ranta bata san wani yayan take nufi ba fa ita, Hajiya Amina tace "Kin dai ga abinda ya faru akan aurenki kwanaki, so hakan kadai shine rufin asirinmu gaba daya" Hajiya Amina ta kalli wayar hannunta dake ring ta mike tace "Bari in amsa waya" Daga haka ta nufi kofar Mayraah ta bi ta da kallo har ta fita.
Chapter 209 · 0% Book details