← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 235 OF 313

Sashe 235

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mayraah ta daga kai a hankali jin an bude kofar dakin, Ceo ta karaso da cup din hot chocolate ta zauna gefenta tace "Here dear" Mikewa zaune tayi ta amshi cup din hade da sauce dinsa tace "Thank you Ma" Murmushi ta mata tana kallonta calmly tace "You are welcome" Mayraah ta fara shan chocolate din a hankali, Ceo ta mike ta fita, ba a dau lokaci ba ta dawo dakin da few pizza slices a plate ta ajiye mata tace "Will you be okay with this?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Thank you Ma" daga haka ta dau slice daya ta fara ci, after some minutes ceo ta mike ta nufi kofa Mayraah ta bi ta da kallo har ta fita ta jawo mata kofar ta rufe, Mayraah ta sauke idonta tana ci gaba da cin pizza din, bayan ta gama ta dau handbag dinta ta ciro wayarta dake ciki, cikin minti kadan tayi activating international roaming sannan ta fara dialing number Maheer, yana fara ring ya daga, a hankali tace "Yaya" Yace "Mimi" Tace "Ka fara bacci ne?" Yace "No Mimi, was waiting for ur call, i couldn't reach you... ya hanya?" Kamar zata yi kuka tace yaya it's soo cold here, i am so cold" Murmushi yayi yace "Yeah i know, akwai sanyi sosai, hope you are on ur jacket?" Kallon jacket din MD dake jikinta tayi, ta kara lullube jikinta da shi murya can kasa tace "Yeah" Yace "kina ina yanzu?" Ta kalli babban dakin tace "Gidan Ceo din mu" Da mamaki Maheer yace "Ceo dinku kuma? Why? Where are ur colleagues?" Mayraah tace "Ni kadai ce dai a nan, su ba a nan suka sauka ba, may be they lodge in hotel, kasan duk maza ne" Maheer ya ɗan yi shiru, can kuma yace "But that's weird, why will she keep u in her home? Any way it's fine..." Mayraah tayi shiru, yace "Hope you are comfortable?" Mayraah ta gyada masa kai a hankali tace "Yeah" Yace "To abinci fa?" Tace "Ta bani har na ci" Da damuwa Maheer yace "Gashi har muryarki ya fara nuna alamar sanyi ya kamaki" Tayi murmushi tace "Yaya kasan fa bana son sanyi" Yace "I know Mimi, shi yasa nake tausayinki" Tace "But ta ban heavy duvet" Yace "To better" Tace "Yanzu Yaya tambayar ta inda zan kalla inyi sallah zan je in yi?" Maheer yace "But she is a Christian how will she know? Ke baza ki gane qibla ba?" a hankali tace "Bazan gane ba, i am confuse" Yace "Ohk try asking her... Meye ta baki kika ci?" Mayraah tace "Ta bani hot chocolate da pizza" Yace "Ohk to ki samu kiyi sallan, idan kin idar sai ki kirani" Tace "Toh" Daga haka ta katse wayar, tana sauka daga saman gadon duk da dumin dakin she was still feeling cold, a hankali ta saka hannunta a sleeve din jacket din MD sannan ta nufi kofa walking slowly ta bude kofar, tana shiga babban parlon gidan ta dinga bin ko ina da kallo sai kuma ta kalli sama, Muryar ceo ta ji ta juya da sauri ta ganta a study room dinta with heap of textbooks a gabanta, tasowa tayi ta shigo parlon calmly tace "You need anything Mary Ann?" Ta gyada kai da sauri tace "I want to pray Ma...." Ceo tace "Ohh kina tambayar gabas kenan ko?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Yes Ma" Kalle kallen Parlon ceo din ta shiga yi, can tace "I can't really tell where Aliyu faces and pray whenever he is around, let me call him on the phone sai ya gaya maki inda zaki kalla" Mayraah tace "Okay Ma" Ta koma ta dauko cellphone dinta ta fara kiran MD, yana dagawa tace "Aliyu zaka gaya mata inda zata kalla tayi sallah" Daga haka ta mika ma Mayraah wayar, Mayraah ta amsa da ladabi ta kai kunne tayi shiru, jin shi ma yayi shiru tace "Ina ji" Sai a sannan yace "Baki da Google a wayarki ne?" Taki ce masa komai saboda ceo dake tsaye, yace "In rashin kunya ne ai ba sai kin jira wani ya gaya maki yanda za ki yi ba, ba ni kika ce ma Quack Doctor ba, za ki sani" Mayraah dai taki cewa komai, Yace "Install Qibla finder on ur phone and stop being a nuisance" Mayraah bata sake tsayawa ta sauraresa ba ta katse wayar ta mika ma Ceo, Ceo tace "Ya gaya maki ko?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Eh ya gaya min" Ceo tace "Ae kina da darduma?" Mayraah tace "Ina da shi" Ceo tace "Toh sai kiyi using warm water kiyi performing ablution din so u won't catch cold" Yanda Ceo tace mata haka tayi da ta koma dakin tayi alwala da ruwan dumi bayan ta fito daga bandakin ta bude akwatinta ta ciro darduman da Ammi ta sa mata sannan ta tada sallan, tana idarwa ta kwanta ta kashe fitilar dakin sannan ta lullube da duvet nan da nan bacci ya dauketa ko Maheer din bata kira ba, cikin dare taji zazzabi ya rufeta ga tari da ta dinga yi, wajen karfe uku ceo ta bude kofar dakin ta shigo ta kunna wutan sannan ta karasa ta zauna gefen gadon ta cire duvet din jikinta tana feeling temperature dinta tace "Are you okay?" Mayraah ta mike zaune tana rawan sanyi, Ceo tace "You are running temperature dear" mikewa tayi ta fita, ba a dau lokaci ba ta dawo da magunguna da ruwan gora, bude maganin tayi ta ba Mayraah ta amsa ta hadiye da ruwan sannan ta koma ta kwanta ta takure waje daya, ceo ta lullubeta da duvet tace "Sannu kin ji...." Kafin gari ya waye ceo ta shigo dakin ya fi a kirga, da asuba haka Mayraah ta daure ta tashi tayi alwala tayi sallah sannan ta koma ta kwanta…. duvet din da taji an cire jikinta ya sa ta bude ido a hankali, MD ta gani tsaye kanta, ta mike da sauri ta ja duvet din ta wani daure fuska tana kallonsa, sae kuma ta ga CEO tsaye a bayansa, sunkuyar da kai tayi, Calmly yace "How are you feeling?" Ta gyada kai a takaice tace "Fine" Ceo tace "Will u take noodles for breakfast?" Mayraah ta gyada mata kai, ceo ta juya ta fita daga dakin sai da yaji ta kulle kofa sannan yace "Cire min jacket dina" Wani kallo ta jefa masa ta sauka daga kan gadon ta bude akwatinta ta ciro towel din wankan ta da shower gel with sponge sai toothpaste and toothbrush tayi wucewarta bandaki ta bar sa wajen tsaye, ya bi ta da ido har ta kulle kofar ta sa makulli, Bayan kusan minti daya ya gyada kai ya juya ya fita daga dakin, Mayraah na fitowa wanka taji kamar zazzabin ya sake dawo mata, ta ajiye jacket din hannunta ta kwanta ta dukunkune cikin duvet ta fi minti goma a haka daga karshe ta daure ta mike ta shirya, ta dau jacket din tana kokarin sa wa Ceo ta shigo dakin tace "In kin gama ki fito kiyi breakfast" Tana fita Mayraah ta saka jacket din sannan ta fito parlor, dinning area ta nufa ta zauna kujeran dake facing na MD dake kallonta ganin she is still wearing his jacket, garnished noodles with chicken Ceo din tayi mash, MD dai na rike da spoon yana kallon plate din abincin, lokaci lokaci yake satan kallon Mayraah, Mayraah ta fara cin abincin haka ma ceo, bayan some seconds ceo ta kallesa amma bata ce komai ba, mikewa yayi ya wanke fork din da knife din hannunsa a washing hand basin dake dining area din ya dawo ya zauna, Ceo tace "Ya maganar Therapy da nayi maka kwanaki?" Karo na farko da Mayraah ta fara ganin murmushin sa, yace "Soon Ma'am" Ceo ta ci gaba da cin abincin ta a nutse, Mayraah sai kallonsa take kasa kasa without letting him notice, gaba daya he doesn't look comfortable a wajen, kawai ta ga ya jawo wani clean plate din ya goge da tissue ya juye abincin a ciki, Ceo ta kallesa ta ci gaba da cin abincinta, sae a sannan ya fara cin abincin, Mayraah bata ci abincin da yawa ba duk da ɗan manna masu ceo tayi a plate kamar wasu turawa, cikin minti kadan ya gama cin abincin ya mike ya bar dinning area din, duk suka bi sa da kallo, dakin da Mayraah take ya shiga, Mayraah dae sai kallon ikon Allah take, ba a dau lokaci ba sai ga shi ya fito, kallonsa Mayraah ta dinga yi da mamaki ganin Jacket dinta a hannunsa, yana kallon Ceo da ladabi yace "I will take my leave now ma'am” CEO tace “Ohk" Daga haka ya juya ya nufi kofa ya fita daga Parlon yana rike da jacket din, Mayraah ta mike zata kwashe plates din Ceo tace "Ki bar shi, yanzu mai aikin zata shigo" Mayraah tace "Toh" barin dinning area din tayi ta tafi daki, bayan ta kulle kofar ta dinga kallon akwatinta dake bude, ta wani hade rai, saboda me zai bude mata akwati, is he even okay?? tsaki ta ja ta karasa ta kulle box din, kwanciya tayi ta dau wayarta tayi dialing number Maheer har ya katse bai daga ba, ta ajiye wayar ta rufe jikinta da duvet. Har ta fara bacci Ceo ta shigo dakin cikin sparkling suit da skirt din da iyakarsa gwiwa, sosai tayi kyau kamar wata baturiya, tana kallon Mayraah tace "You just stay back and rest Mary Ann, za mu je conference din yanxu, it's only for today and tomorrow.... if u need anything feel at home ki shiga kitchen" Mayraah tace "Ohk Ma, nagode" Ceo ta mata murmushi sannan ta juya ta nufi kofa Mayraah ta bi ta da ido har ta fita ta kullo kofar, a hankali ta jawo wayarta tayi dialing number Amminta.... Karfe sha biyu saura kiran Usman ya shigo wayarta, ta mike zaune daga kwancen da take da kyar saboda mugun ciwon da kanta yake mata, picking call din tayi ta gaishesa ya amsa yace "Mura kike ne?" A hankali tace "Eh" yace "Kin sha magani?" Tace "Na sha daxu" yace "Where is ur location?"
Chapter 235 · 0% Book details