← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 286 OF 313

Sashe 286

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juyawan da wannan matar da ta kira sunan Aaria zata yi suka yi ido hudu da Ammi dake ta kallonta da wani expression gabanta na faduwa, Matar ma ta dinga kallon Ammi ba ta ko kiftawa alamar tana son tuno inda ta taɓa saninta ita ma, duk da haka dai fuskarta da fara'a take nuna masu kujeru tana welcoming dinsu tace "Bismillahn ku ga kujera...." Ammi ta sauke idonta, hannunta rike da na Mayraah ta karasa kujeran suka zauna tunani iri iri na yawo a ranta, gaba daya she is just confused, Abba ma duk suka karasa can cikin parlon suka zauna kan kujera, Ceo na rike da kanwarta ta zauna tare da ita a gefenta, Dai dai nan wata dattijuwar mata ta shigo parlon zata raka wasu baƙinta biyu, tana ganinsu Abba duk da bata san ko mutum daya a cikinsu ba tayi welcoming dinsu da fara'a, after seeing off her visitors ta dawo parlon ta zauna tana murmushi idonta da attention dinta duk na kan Mayraah tace "Sai dai har yanzu ban wayi kowa a cikin ku ba wallahi" Tana fadin haka ta kalli matar dake tsaye tun shigowarsu Abba parlon tace "Aunty Sadiya a kawo masu ruwa mana ko" Matar da ta kira da Aunty Sadiya ta juya ta bar parlon don duk iya kokarinta na ganin ta tuno inda ta taɓa sanin Ammi ta kasa tunowa, tunanin da take ta yi kenan a tsaye amma ta kasa tuna Ammi, Ceo na kallon dattijuwar nan da ta kasa dauke idonta kan Mayraah calmly tace "Wajen Mai gidan mu ka zo idan babu damuwa pls Hajiya" Matar na murmushi tace "Oh... Allah sarki, to ku karaso parlon nasa ai yana ciki" Tana fadin haka ta mike, ta nufi wani parlon suka bi bayanta gaba daya, wannan din ma wani babban parlor ne that is well furnished, tayi masu iso har ciki duk suna biye da ita a baya, bayan duk sun shigo ta kulle kofar, tsaye Abba da Ammi da su Maheer suka yi ba tare da sun karasa can cikin parlon ba basa ko kiftawar kirki suna bin duk occupant din parlon da kallo, wani Dattijo ne kishingide a saman lallausan carpet ga fruits iri iri a gabansa, daga gefensa kuma Musharraf ne zaune sai MD da shi ma yake zaune kasan carpet din kusa da Mamin sa, daga daya side din wannan dattijon kuma wani mutumi ne da bazai haura shekaru 48 ba, MD ne ya fara mikewa da sauri tsabar yanda ya rikice yana kallon su Abba da Ceo, sai kuma Musharraf da shi ma ya mike yana kallonsu da mugun mamaki, sannan wannan mutumi da yake late forty's dinsa shi ma ya mike tsaye da sauri cikin wani irin yanayi yana kallon Aaria yace "Maryam?" Ita dai Aaria kallonsa kawai take bata ko kiftawa, MD ya ji kafafuwansa sun kasa ci gaba da daukarsa a hankali ya durkusa kan knees dinsa yana repeating Innalillahi wa inna ilaihi raji'un a zuciyarsa, Mami was dumbfounded sai bin su Abba gaba daya take da kallo, shi ko Dattijon nan da yayi saurin daidaita zamansa in ya kalli su Abba, sai kuma ya kalli Ceo, sannan ya kalli su Maheer, haka nan dai ya dinga bin su da kallo kana ganinsa kasan shi ma dai ya shiga rudani a wannan lokacin, Matarsa da ta kawo su parlon sai bin kowa take da kallo with confusion, infact everybody in that parlor was more than confused, Ceo ta kama hannun Mayraah dake ta kallon su Musharraf da uwarsu da idanuwanta kamar za su fito don mamaki, ita Ammi tsabar kidimewa haka ta bude baki hangangan tana kallonsu, Ceo na rike da Mayraah ta tafi har gaban wannan mutumi dake tsaye ya kasa daina kallon Aaria, tana nuna masa Mayraah babu yabo babu fallasa tace "Abdallah!! Your Child" Tana fadin haka ta juya ta koma inda su Abba ke tsaye ita ma ta tsaya tana kallon Abdallah wanda ke ta kallon Mayraah da ta sunkuyar da kanta hawaye na sauka idonta kamar an bude pampo, Mikewa tsaye dattijan yayi yana ma Ceo wani kallo yana huci kafin yace komai matarsa warce ita ce mahaifiyar Abdallan ta dakatar da shi, cike da takaici tace "Kar ka ce mata komai, kar ma ka fara Alhaji, fuskar yarinyar nan kawai zaka kalla and it says it all" Juyawa Dattijon yayi ya sake kallon Mayraah, zuwa sannan ne Aunty Sadiya ta shigo parlon tana kallon Ammi wanting to know their mission a gidan Babban yayansu don sai yanzu ta tuna a inda ta taɓa saninta wato ranan da suka je kai lefen Mayraah da kuma sanda suka je amsowa, Hajiya Ramatu ta fashe da matsanancin kukan takaici a parlon tana girgiza kai, Ceo ta juya tana kallon Abba hawaye cike idonta tana nuna masa Abdallah, Calmly tace "Alhaji wannan mutumi da kake gani shine yayi assaulting Kanwata many years ago, putting her in a family way, a sanadin haka har ta samu 'ya mace out of wedlock...." Sai kuma ta nuna masa Dattijon wanda aka fi sani da Hon Alhaji Kabir Saminu tana murmushin takaici hawaye na sauka idonta tace "Wannan kuma shi ne mahaifinsa wato kakan Mayraah wanda ya sa aka kulleni gidan yari na wata bakwai" Da sauri Abdallah ya karasa gun Aaria da wani expression yana zare ido bakinsa na rawa yace "Did you hide anything from ur sister afterward Maryam??" Wani kallo Ceo ta jefa masa strictly tace "Kar ka kuskura ka firgita min kanwa Malam, stay back" Abdallah ya koma gun mahaifiyarsa cikin kidimewa ya durkusa gabanta yace "Mommy duk fa kun san abinda ya faru 22 years ago, babu abinda baku sani ba don Allah ku ce wani abu" Mahaifiyarsa dai sai goge hawayen dake ta sauko mata take tana girgiza kai ta kasa cewa komai tsabar takaici da zafin da zuciyarta ke mata, Mami kam rike kanta da yayi mata nauyi tayi tana nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un a zuciyarta, in dai abinda ya faru ne a wancan lokacin ai duk kowa a family ya sani ba boyayyen abu bane, zuwa sannan Aunty Sadiya ƙafafuwanta sun kasa daukarta sai bin kowa na parlon take da ido abu ne wanda ya zo masu dukkansu a ba zata, durkushewa Musharraf yayi a nan kasan parlon zuciyarsa na wani irin bugawa, Tuni Hon Alhaji Kabir ya mike ƙasan tsadadden carpet da yake zaune ya koma kan kujera ya zauna da kyar ya jinginar da kansa jikin kujeran ya dafe gefen kirjinsa, mikewa matarsa tayi da sauri ta nufesa ta zauna kusa da shi cikin rawan murya tace "Baka da lafiya Alhaji, pls let's take everything easy, we should take everything bit by bit, kar kayi stressing kanka, ka kwantar da hankalin ka don Allah" Tana fadin haka ta mike ta kama hannun Mayraah dake kuka ta zaunar da ita saman carpet din gently sannan ita ma ta zauna hawaye na sauka idonta, dafe kanta tayi bayan few seconds ta dago cike da karfin hali take kallon su Abba tace "Alhaji plss ku zauna" Sai a sannan Abba ya sauke wani ajiyar zuciya da kyar ya daga kafa ya karasa cikin parlon ya zauna saman kujera, Ammi dake hawaye ita ma ta tafi ta zauna, Usman da Maheer that were more then shock too duk suka zauna parlon kowa na parlon nan ganin abun yake kamar almara banda Ceo da kanwarta, Ceo na rike da hannun Aaria suka nufi kujera ta zaunar da ita sannan ta zauna tana goge mata hawayen dake sauka idonta da handkerchief. Hajiya Ramatu na kallon dan nata cikin karfin hali tace "Abdallah what happened 22 years back?" Ya juya ya kalli Aunty Sadiya da ita ma hawaye ya cika idonta, sai kuma ya kalli mahaifiyarsa cike da damuwa yace "Amma Mommy ke da Daddy kun san komai fa, even Aunty Halima...." Hajiya Ramatu ta dakatar da shi tace "In mu mun san komai duniya fa??" Ya runtse ido ya mike yana kallon Aaria ya nufeta yana girgiza kai yace "Maryam, why did you chose to hide things from ur sister?" Aaria dake ta kallonsa cikin sanyin murya tace "Like?" Ita dai Ceo da duk sauran occupant din parlon kallonsu suke, banda Mayraah da kanta ke sunkuye tana hawaye, Abdallah ya durkusa gabanta trying all best to compose himself yace "Yes i assault you da farko kamar yanda yayarki tace i can't deny that, amma daga baya fa Maryam? Me yasa na dinga bibiyanki after that? Why did u hide that part from ur sister?" Aaria ta daga kai ta kalli Ceo dake kallonta Keenly don ko da wasa Aaria bata taɓa gaya mata komai ba, Aaria ta sunkuyar da kanta kamar baza tace komai ba, sai kuma a hankali tace "I can't remember anything" Abdallah ya girgiza kai da damuwa yace "You are not saying the truth Maryam.... But why pls?" Ita dai taki ce masa komai, ceo bata fasa kallonta ba tana son jin wani truth ne ta boye mata, Abdallah ya juya yana kallon mutanen parlon bayan few seconds ya dake yace "Bayan encounter dina na farko da Maryam, i was disturbed and regretted all what that happened that day, and that was so unusual of me don kuwa my father was very rich, i was an only child don haka duk wani abu da zan aikata i always have my way babu wanda ya isa ya hukunta ni domin mahaifina zai tsaya min a ko ina kuma bana taɓa regretting, but in Maryam's case it was different don na shiga damuwa sosai hakan yasa na ci gaba da bibiyarta har gidansu, a sannan yayarta na fita kasuwa kullum da safe bata dawowa kuma sai karfe shidda, duk zan je gidansu Maryam tare mu ke zuwa da Aunty Halima warce ita ma ban boye mata abinda ya faru ba, though aunt dita ce ita amma kuma na girmeta sosai don ita ce autansu Babanmu kuma a gidanmu ta tashi bayan kakannimu sun rasu shi sa muka shaku da ita, a ranan ma Dad dina ne yayi niyyar zuwa makaranta ya daukota amma sai tafiya ya kamasa ni naje makarantar, after a while of following Maryam ina mata magiya sai ta dan fara sakin jiki
Chapter 286 · 0% Book details