Sashe 219
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
ku dai ku shirya nan da karfe uku sai in kai ku airport din nasan yanda zan yi da ita" Ammi tace "Toh shikenan" Daga haka ta mike ta wuce sama, karfe biyu da rabi Maheer ya shigo bangaren Ammi, har sannan Mama Ladi na kwance cikin bargo, Maheer na kallonta yace "Sannu Mama" Ta gyada masa kai kawai, yace "Ko za mu koma can bangaren ne Kinga za su tafi airport ne yanzu" Mama Ladi ta ki kulasa, yace "In kuma kin fi son nan din to...." A mugun fusace tace "Kai dalla rabu da ni inji da cutar dake damuna, ko don ba kai ne ke jin jiki ba?" Maheer yace "Shine nace ma Ammi da naga ta dage a tafi Abuja dake nace mata baxa ki iya ba kina jin jiki, zaman jirgi sai me lafiya..." Mama Ladi na kallonsa tace "Ni muka yi haka da kai Mashir?" Maheer yace "Toh ai basa barin mara lafiya ya hau jirgi shine dama matsalar" Mama Ladi ta mike zaune tace "Ciwon kan ne ma kawai ya saka ni gaba amma ni kaina nasan jikina da sauki bana jin komai wallahi" Maheer yace "Sai dai in zan tafi mu je tare, tun da kin ga sati daya ake dauka kafin mutum ya samu kujeran jirgi don ba kullum jirgin ke tashi ba, wannan ma sai da Abba yayi sati biyu yana bi sannan ya samar masu kujeran" Mama Ladi ta koma ta kwanta, Mikewa yayi ya shiga dakin Ammi dake sauraronsu, yayi murmushi yana kallon Ammi yace "Bari in fita da akwatunan" Ammi dai bata ce komai ba tana mamakin Mama Ladi yanzu kawai sai ta kara kwasan jiki ta bi su Abuja, ina laifin ma ta bari sai bayan kwana biyu haka da komawarsu in ma zuwa zata yi, ai sai abun ya zama rashin hankali kuma, tun bikin Maheer fa take gidan, har Maheer ya kai akwatunan mota Mama Ladi na kwance ta maida bargon gefe daya, Ammi ta fito daga dakinta don karfe ukun ya kusa ta zauna tana kallon Mama Ladi tace "Toh Mama za mu tafi, idan ya so in Maheer zai je sai ku taho tare tunda kujera biyu kawai Abbansu ya samu...." Mama Ladi tace "Ai shikenan, banda ma jikina ya matsa min ai tun a shekaranjiyar nayi niyyar tafiya karaye, to kana naka ne Allah na nasa, ban yi zaton zan kai har yau a gidan nan ba" Ammi tace "Haka ne kam, sai kun zo din dai, bari in je kar mu rasa jirgin" Mama Ladi bata kara tankata ba har ta fita daga Parlon, Maheer ya kai su airport din tare da Mayraah, bayan sun shiga departure ya koma gida.... Karfe biyar suka sauka airport din Abuja, sabon Driver da Abba ya dauka ne yaje airport din daukosu. Ammi bata taɓa zaton irin gidan da Abba ya siya ba kenan a Abuja, she never expect it, mansion ne na gani na fada a anguwa me kyau, kai kana ganin gidan kasan account yayi bala'in girgiza, ga masu gadi biyu da ya saka a gidan da driver daya, har da me watering flowers da sharan babban compound din, abu daya ne babu a gidan wato swimming pool cause it won't be of any use to them, tsabar farin ciki sai da Ammi tayi hawaye bayan ta shiga part dinta it was something she never saw coming, Bedroom din Mayraah yayi biyun wanda ta bari a kano, bandakin ma was very big, dakuna sun wadata sosai a gidan, tun daga sama har downstairs, wajen karfe shidda Abba ya shigo gidan don yana Abujan, Ammi na zaune Bedroom dinta ta ma kasa yin komai sai kallon Mayraah dake jera mata kayanta a press take, Abba na shigowa dakin yana kallon Ammi yace "Me ya samu wayarki ne" cikin sanyin murya Ammi tace "Ban cire a flight mode ba" Mayraah ta gaida Abba, Abba yace "Kema na kira baki daga ba" Mayraah tace "Yana cikin handbag dina" Abba yace "Ohk" Mayraah na murmushi tace "Abba the house is so beautiful Allah ya sanya alkhairi, Allah ya kara maka budi da daukaka, Allah ya sa kafi haka" Abba ya dafa kanta yana murmushi yace "Ameen my Baby gal, hope u are prepared for ur interview tomorrow?" A hankali Mayraah ta gyada masa kai, yace "To maa sha Allah, i know u can do it, congratulations in advance daughter" Tana murmushi ta fita ta bar masu dakin, nan da nan hawaye ya cika idonta, tana komawa nata dakin ta fashe da kuka sosai, she knows she can never pay them in anyway, bata ta taɓa iya biyan duk abinda suka mata a rayuwar nan ba, even if she will how is she going to repay all this? with what will she repay? because of the genuine love they have for her they still have to relocate back to Abuja for the sake of her new work, Bayan Mayraah ta fita dakin Abba ya kalli Ammi da ta kasa dago kanta yace "Gidan ya maki ko a canza yan mata?"