Sashe 232
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kadai, Mayraah na kallonsa tace "Yaya ka sha shayin?" Yace "Na sha" Kitchen ta nufa ta zubo ma Ammi sauran abincin da ta dafa ma Maheer dazu sannan ta dawo parlon, yace "Yaushe kika fara cin abinci haka Mimi?" Dariya tayi tace "Ammi fa zan kai ma" Yace "Better" Murmushi tayi ta koma sama ta kai ma Ammi abincin, Ammi na amsa kawai ta mike don ta rasa ta inda zata fara mata maganar da ya kawo ta dakin, ta sa a rai zata bari in sun dawo daga England kawai. Yau tun da Mayraah ta tashi take dakinta a kwance bata fito ba, breakfast ma har Bedroom Ammi ta sa me aiki ta kai mata, it was a Friday kuma yau ne ranan tafiyar tasu zuwa Uk amma evening Flight, jin ana knocking kofarta ta kalli agogo dake nuna karfe uku na rana ta sauka daga kan gadon ta bude kofar, Maheer ne tsaye bakin kofar yana sanye da farin Gezna, daga sama har kasa take kallonsa, sai kuma tayi murmushi ta jingina da kofar a hankali tace "Good afternoon" Yace "Afternoon Mimi" Ta langwabar da kai tace "Kayi kyau kamar wani sabon ango, nasan yau mata suna ta kallon ka a hanya ko" Ya ɗan buda ido yace "Ango kuma" Tana murmushi tace "I am serious u look gorgeous" Bai kulata ba yace "Duk efizyn zaki je England ne yau ya sa kika ki fitowa parlor mu ganki?" Tayi dariya tace "Yaya wallahi kamar a fasa tafiyar da ni, i wish kawai za ace banda ni, i am so tense" Yace "Why?" kamar zata yi kuka tace "Kawai haka nan, i don't understand why i am tense" Ya sauke idonsa kasa yace "Sauko mu yi Lunch" a hankali tace "Ohk" Daga haka ya juya ya sauka kasa, ita kuma ta juya ta koma dakin zata dauko hular ta, suna zaune parlon su biyu kadai, eating from the same plate Haseenah ta shigo parlon, kamar hadin baki suka mata kallo daya suka dauke kai a tare, kitchen ta nufa ta je ajiye warmer din da za a sa mata abincin dare, tana fitowa bata ko kallesu ba ta fita daga parlon, Mayraah na gama cin abincin ta dinga ma Maheer hira a parlon tana basa labarin irin cases da take gani a asibiti, wanda kawai sauraronta yake a ransa kuma yana tunanin may be ta mance shi ma likita ne, a haka Ammi ta sauka downstairs ta samesu, ta kalli agogo tace "Ke ba karfe biyar bane Flight dinku kike nan zaune?" Sai da gaban Mayraah ya fadi don ita ko son a tuna mata da tafiyar nan bata yi, Maheer yace "Mimi that's true ki je ki shirya da wuri, gwara ki jirasu da ace sun jiraki" A hankali ta mike ta wuce sama, bandaki ta shiga tayi wanka ta dauro alwala ta fito, bayan ta idar da sallahn asr Ammi ta shigo dakin, tana kallonta tace "Kin sa kayan naki cikin akwati ne?" Girgiza kai tayi, Ammi tace "Ke dai komai kin fi son sai kinyi cikin kurarren lokaci, ance maki flight karfe biyar ya kamata ace kuna airport ma yanzu" Usman ne yayi knocking kofar dakin sannan ya bude, yana kallon Mayraah yace "Ina kika ajiye wayarki ake ta kiranki?" Ta ɗan buda ido da sauri ta nufi karkashin pillow da ta ajiye wayar dazu, miss calls din Dr Khalil ta gani har uku, ta kalli Usman dake mata wani kallo, Ammi ta fiddo mata wani abaya ta ajiye gefen gado tace "Gashi nan ki saka" Usman yace "Kin bar su tun dazu a waje suna jiranki" Daga haka ya juya ya bar bakin kofar, Ammi ta bude baki tana kallon Mayraah da ta kasa tabuka komai, da kanta ta fara hada mata few clothes dinta da duk wani abu da zata bukata a akwati, bayan barin Usman wajen sai ga Maheer, a bakin kofa shi ma ya tsaya yace "Mimi they are waiting for u outside kiyi sauri...." Kayanta ta dauka ta fara sa wa, Ammi ta gama hada mata komanta a akwati, Maheer na kallon Ammi yace "Akwai sanyi sosai Uk, she shouldn't forget her jacket" Ammi ta kalli Mayraah tace "Rigunan sanyinki suna dakina kije ki dubo da sauri" Mayraah na fita daga dakin Maheer ya bi bayanta yace "Do not forget ur sanitary stuffs, hopefully har ki dawo kila...." Mayraah ta buda ido don har ta manta, sai bayan kusan minti goma Maheer ya sauka downstairs da akwatinta tana biye da shi a baya, Ammi ta rakasu har compound tana mata Allah ya tsare hanya, kana ganin Ammi kasan babu yanda ta iya ne da tafiyar Mayraah, suna fita kofar gida Mayraah ta ga mota anyi parking, Dr Khalil ya bude masu booth Maheer ya ajiye akwatin, tana kallon Maheer tace "Yaya gobe Ya Usman din zai je can?" Maheer ya gyada mata kai yace "In sha Allah" A hankali ta bude back seat ta shiga don ko ba a gaya mata ba taga alamar da mutum a front seat din, Dr Khalil suka yi sallama da Maheer sannan ya koma cikin motar, Mayraah ta daga ma yayan nata hannu kamar zata yi kuka, Dr Khalil yayi reverse suka bar anguwan. Tana daga kai suka hada ido da MD ta madubi, sauke idonta tayi murya can kasa tace "Good evening" ya ji ko bai ji ba oho, don bata ji ya amsa mata ba, Dr Khalil yace "Ina kika ajiye wayarki, kin kuma san karfe nawa ne flight din naku" Tace "Shiryawa nake ne" Dr Khalil ya girgiza kai yace "Ku dai mata komai sai kun saka African time a ciki...." Mayraah dai ta ci gaba da danna wayarta bata ce masa komai ba, MD na kallon Khalil yace "Plss ka bi route din da za mu yi sauri, it's easy to miss a flight...." Dr Khalil yace "In sha Allah baza ayi missing Flight din ba we will get there in time" Suna isa airport MD ya sauka, Dr Khalil ma ya sauka daga motar ya fiddo hand luggage din MD wanda jacket dinsa ne kadai a ciki sai textbooks, sannan ya ciro akwatin Mayraah ma, tuni MD ya shiga airport din don baya son ace sun yi missing jirgin, Mayraah dai sai zare ido take tana neman sauran da za su je Uk din tare, Kasa hakuri tayi bayan sun nufi cikin airport tare da Dr Khalil tace "To ina sauran sir?" Yace "Doctors biyu ne kuma suna lagos, daga can za su tafi" Mayraah ta zaro ido tace "Babu nurse ko daya??" Yace "Babu" Mayraah ta marairaice tana kallonsa, dariya ta basa amma ya dake yace "It's fine Mayraah" Ta girgiza kai kamar xata yi kuka tace "Yanzu ni da shi kadai za mu hau jirgin?" Dr Khalil yace "Eh mana, in kun je can za ku hadu da sauran" Ji tayi hankalinta ya tashi tace "Ni dai wallahi i don't want to go with him" Dr Khalil yayi dariya yace "But he is not a monster Mayraah, look kin ga kun yi latti let's be fast pls" Bin sa kawai take a baya with different thought a zuciyarta, duk traveling document dinta suna wajen MD din, bata kara shiga tashin hankali ba sai da taga sun gama check in, Dr Khalil na masu sallama bayan za su shiga departure lounge, dauke kanta tayi don yanzun nan sai ta iya fashewa da kuka. Sun shiga departure lounge din immediately aka fara boarding plane din nasu, ita dai bin sa kawai take gashi ya ki juyowa ma ya ga ko tana biye da shi a baya ko akasin haka, a haka har suka shiga plane din, yana isa seat dinsa ya ajiye hand luggage dinsa a sama sannan ya zauna, tana ganin haka kawai tayi assuming seat din ta ne gefen nasa, ita ma ta zauna tana satan kallonsa. 2 hours into the flight ta fara jin bacci amma tayi ta kokarin ganin bata yi ba, abincin da aka yi serving dinsu ma bata taɓa komai ba, a haka har baccin ya dauketa bata sani ba, she can't tell for how long tayi baccin kawai ita dai kamshin turaren da ya cikata ne ya farkar da ita daga baccin bayan tayi isasshe, zaro ido tayi ganin inda tayi resting kanta, sai kuma ta daga kai da sauri ta kallesa, idonsa na kan wani littafi dake hannunsa, matsawa tayi tana gyara zamanta kamar munafuka, shi dai ko kallonta bai yi ba yana karatun book din hannunsa, ko gyangyadi Mayraah bata sake barin tayi ba har suka sauka UK, bayan ya cire seat belt dinsa ya mike ya dau hand luggage dinsa, ita dai kallonsa kawai take, ya bude karamar jakar tasa ya ciro jacket dinsa ya saka, tana ganin ya fara tafiya ta wani bi sa da harara sai kuma ta mike ko ruwa bata dauka a abincin da aka ajiye mata ba ta bi bayansa, suna sauka jirgin Mayraah taji ta kamar a freezer, nan da nan hankalinta ya tashi, ko wani mutum ta gani a wajen da thick Jacket dinsa, wani mugun sanyi ta dinga ji amma a haka ta dinga bin sa a baya, ko kadan bata shiri da sanyi, yanzu nan sai yayi distablizing dinta nan da nan kuma zata fara mura da tari, har suka shiga airport din tana jiran akwatinta MD yaki kallon inda take don waje ma ya nema ya zauna yake danna wayarsa, after many minutes of waiting akwatinta ya iso ta dauka ta kalli inda yake, kawai gani tayi ya mike ya fara tafiya, ta bi bayansa tana tafiya a hankali har suka fito daga wajen, she was just shivering daga inda take tsaye rike da akwatinta, shi kuma yana tsaye ɗan nesa da ita yana kiran Ceo don yaji hotel din da ta kama ma staffs din nata, tana dagawa tace zata kirasa sannan ta katse wayar, yasan yanzu sai su kai minti goma suna jiranta a haka, ya ɗan juya ya kalli direction din da Mayraah take ta wani takure saboda mugun sanyi, kasa ci gaba da jure sanyin tayi ga shi hankalinta bai je ta bude akwatinta ta ciro rigar sanyinta ba, she was shivering seriously, juyawa tayi da