Sashe 289
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ceo kuka take sosai tana kallon Kanwarta cikin rawan murya tace "Me yasa kika boye min duk wannan abun Aaria? You told me he forced you" Hajiya Ramatu da hawaye ke zuba idonta ta jawo Mayraah dake kuka zuwa jikinta, Aaria dai kanta na kasa hawaye na zuba idonta, Ceo ta kasa daina kallon kanwarta hawaye wasu na bin wasu a fuskarta, wa ya ga kuka wajen Ammi, nan kuwa kukan farin ciki kawai take with how things later turn out, Abba ya sauke wani nauyayyen ajiyar zuciya yana hamdala a zuciyarsa, Maheer couldn't stop looking at Mayraah that is crying profusely a jikin Hajiya Ramatu, Mami da Allah yayi ta mace me dakiya a ko wani hali ta daura kan Musharraf a shoulder dinta seeing how emotional he was, MD dai kansa na kasa haka ma Usman da tun da Abdallah ya fara magana shi ma bai dago kansa ba, Silence din kusan minti uku ne ya ziyarci parlon, everyone was so speechless and never saw this coming, nobody expect things to turn out this way, Abba yayi karfin hali yana kallon Alhaji Kabiru Saminu yace "Watannin baya da suka wuce idan ba mantawa nayi ba har da kai aka zo nema ma dan ka auren yarinyar da duk duniya mutanen da suka san ba mu ne asalin iyayenta ba basu da yawa, don wani sirri ne babba da muka rufe wanda ita kanta yarinyar bata san ba mu ne iyayenta ba, hatta 'Ya yan da muka haifa a cikinmu bamu bude masu wannan sirri me girma ba, ana saura kwanaki daurin aure sirrin nan da muke ta boye wa na shekara da shekaru ya fallasa wanda hakan ya girgiza mu ainun, babu rashin mutunci da tijaran da yan uwanka basu zo sun mana ba ana gobe daurin aure, suka kirani karamin mutum, suka kirani makaryaci a fakaice daga karshe suka amshi kudinsu suka ce sun fasa wannan aure, though ban ga laifinsu ba don a zance na gaskiya ya kamata ace na buda masu wacece yarinyar nan tun farkon zuwansu neman aurenta amma wllhi wani lokacin mu kanmu mantawa muke ba mu muka haifeta ba, we want nothing but the best for the innocent girl da muka tsinta a walakance shekaru 22 da suka wuce bama san duk wani abinda zai tarwatsa mata farin cikinta gashi ta taso tana mana kallon iyayen da suka haifeta, amma na so su yi considering cewar yarinyar nan bata da laifi in laifin ne ma ni da Amminta ne masu laifin da muka rufa wnn sirri, yarinyar nan tana da tarbiyya, tana da ilimin addini da na boko, wanda shi yaron naku ma lecturer dinta ne a jami'a kuma da bai yi na'am da tarbiyarta ba bazai fara nemanta da aure ba, amma yan uwanka suka rufe ido suka mana abinda suka yi, lefen da suka kawo ma haka nan aka zo aka amsa a nan din ma dai babu irin tijaran da matata warce ita ta rike yarinyar nan tun tana jaririya bata gani ba, to wannan yarinyar da ku ka hana dan ku aurenta don bata da asali ba a san ko er wacece ba ita ce can a zaune, We named her MAYRAAH" Abba ya kai karshe yana nuna Mayraah dake rungume jikin Hajiya Ramatu, Ceo na murmushi hawaye na sauka idonta tace "Kuma yarinyar dake zaune can ita ce warce kanwata ta haifa bayan dan ku yayi putting dinta in a Family way, tana haihuwarta kuma saboda takaicin abinda uban dan yayi min na kai ni prison don na nemi kwatar ma kanwata hakkinta na faki idon kanwata na saka jaririyar cikin kwali na kai ta nayi deserting dinta a wani anguwa wanda a can ne wannan bawan Allah da matarsa suka tsince suka riketa har zuwa yau, bayan raba kanwata da er ta ta shiga halin rashin lafiya har zuwa yau da nake wannan maganar, sai ga shi Allah ya hadani da er kanwata a asibitina na garin Abuja, yanzu kawai DNA test za ayi to clear away doubt din kasantuwarta er Abdallah" Hajiya Ramatu na kara jan Mayraah jikinta ta girgiza kai tace "Babu batun DNA test, don wannan yarinya kamanninta sak na surkata warce ni kaina sai a hoto na taba ganinta tun ina amarya kuma hoton" Mami ta sauke ajiyar zuciya a karo na farko tace "Da naje dubata asibiti da tayi rashin lafiya nima na ga kamannin don ban taɓa ganinta ba sai ranan, har nake gaya ma Musharraf da ya dawo kano, a gidan Alhaji Habibu aka salwantar da hoton nan nake ji da duk an nuna ma kowa" Hajiya Ramatu tace "Kwarai Kuwa" Ceo dai sai kallon MD take don bata taba sanin daga wannan familyn ya fito ba, da tasan Uncle dinsa ne Alhaji Kabir Saminu da ko aiki bazata daukesa asibitinta ba balle har ta basa matsayinsa na yanzu, Halima ta dafe kanta tace "Kaico.. Mun ci mutuncin er mu da kan mu, dama ance rashin sanin yafi dare duhu" Shi dai Abdallah kallon Mayraah dake jikin Mom dinsa kawai yake babu ko kiftawa, A Karo na farko Alhaji Kabir Saminu wanda shi ma tun shigowar Mayraah ya ga kamannin Mahaifiyarsa da ta rasu tun yana shekara sha hudu, a hankali ya fara magana don zuwa sannan kirjinsa yayi masa nauyi, cike da karfin hali yana kallon Abba yace "Da farko Alhaji bamu da abinda za mu ce maka sai dai mu baka hakuri akan abinda ya faru, ku yi hakuri, ku yi hakuri, rashin sani kam yafi dare duhu, shi yasa ake son mutum ya dinga daga kafa akan abubuwa da dama na rayuwa saboda bayansa, gashi dai a karshe ita wannan yarinya daga tsattson mu ta fito bayan duk cin mutuncin da muka yi maku.... Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah ya hanamu jin kunyan duniya da na kiyama, ban taba jin kunya na abinda na aika irin wannan ba a rayuwata" Kallon Ceo yayi still speaking calmly yace "Kiyi hakuri mun zalunce ki kwarai da gaske, mun zalunce ki mun zalunce kanwarki, bani da abinda zan ce da ya wuce kuyi hakuri, i felt so ashame of my act a yau din nan, i am deeply sorry for making u and ur sister pass through a lot many years ago, duk laifina ne ni na ja komai da naki basa goyon bayan auren da ya so yi, duk da matata tayi iya kokarinta na ganin na hakura na bar sa da auren yarinyar bayan da yaje wani waje aka daura, amma saboda wani dalili na da bai da tushe na lalata auren" Shiru ya sake yi na wani lokaci yana sauke numfashi a hankali, sai kuma ya kalli Abdallah yace "Baza a tashi a nan ba sai da auren wannan baiwar Allahn a kan ka matukar ta amince, ni kuma zan bada sadakinta, i don't mind if she is a Christian or a Muslim" Da sauri Ceo ta kalli Alhaji Kabir dake kallon Aaria yace "Kin amince a mayar da aurenku da shi?" Mikewa Abdallah yayi ya isa gaban Aaria ya durkusa a hankali yace "Pls do not say no Maryam, all this years baki taba fita a zuciyata ba, ba da son raina na guje ki ba umarnin iyayena na bi, don Allah kar ki ce Aa, I never knew you conceived" Kallonsa kawai Aaria take hawaye na sauka idonta, Halima ta dawo kusa da su tace "Don Allan kar ki ce Aa Maryam do this for the sake of ur beautiful daughter" Aaria ta jinginar da kanta saman shoulder din yayarta wasu hawayen na sauka idonta, Ceo dai ta kasa cewa komai ita ma tana hawayen, cikin sanyin murya Aaria tace "I will do it for my daughter" Abdallah ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, Alhaji Kabir ya kalli Musharraf calmly yace "In sha Allah kai ma baza ka tashi a nan ba sai da auren er uwarka wanda kai din kawunta ne" Daga MD, Maheer har Usman daga kai suka yi suna kallon Alhaji Kabir Saminu...... Musharraf da kansa ke saman shoulder din Maminsa ya bude ido da sauri amma ya kasa dagowa bayan yaji abinda Uncle din nasa yace, Daga Abba har Ammi kallon Alhaji Saminu kawai suke babu wanda yace komai cikinsu, ita dai Mayraah dake rungume jikin Hajiya Ramatu a hankali ta bude idonta jin abinda kakan nata yace, the parlor was silent for a while, bayan wasu yan dakikai Ceo dake kallon Alhaji Saminu ta girgiza kanta tana kallonsa directly in the eyes speaking calmly tace "Decisions ain't just made that way, Probably an samu wasu changes din da kai baka sani ba, this is something that happened months back not few days ago, so you are suppose to ask her rightful parent ko bayan nan sun mata wani mijin ne kafin ka yanke wannan shawaran, what if da baikon wani a kanta? You ought to have reason that Sir" Hajiya Ramatu ta sauke ajiyar zuciya a hankali tana shafa kan Mayraah dake jikinta tace "Wannan gaskiya ne Alhaji, haka ya kamata ka fara tambaya tunda bamu san ko da wani abu daban dake zuciyar iyayen nata ba ko ita kanta, or may be her parent may have a different plan for her now" Alhaji Saminu ya jinjina kai, letting out a sigh at the same time looking so weary yace "Tunanin hakan bai zo min ba, wannan kam haka yake, duk da shi ma Musharraf din da wata maganar a kasa, amma domin gyara ɓarakar baya shi yasa nayi kokarin zartar da wannan hukuncin kai tsaye amma ba don nuna isa da er su ba, don maganar Musharraf dake kasa magana ce da zan iya shunning considering abinda ya faru a baya" Sai kuma ya juya ya kalli Abba yace "Ku gafarceni Alhaji nayi kokarin yanke hukunci babu neman shawaranku ko opinion din ku, so now Is there anything you want to say akan decision din nan nawa?" Abba ya sauke ajiyar zuciya bai dai ce komai ba, can ya juya yana kallon Ammi da ta sauke idonta kasa, a hankali yace "Hajiya is there anything?" Ammi ta ɗan kalli Maheer, kawai ta girgiza kai tace "Mayraah za a tambaya, abinda yake ranta shi za ayi mata" Alhaji