Sashe 206
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 1 min read
ganta, Yace "Nan din ba gida bane?" Ta wani hade rai tace "Ni dai pls mu tafi gida" Sama ya wuce ta bi bayansa har zuwa parlon Abba, kusan duk bayan kwana biyu sai Usman ya zo gidan sai in baya gari, Maheer ne dai tun ranan da Abba ya kirasa ya zo bai sake bin hanyar gidan ba har yau, Da kyar Mayraah ke cin abincin da Abba ya zuba masu, Hajiya Amina na zaune parlon tana kallon TV, har daga karshe Mayraah ta mike tace ta koshi, Hajiya Amina tace "To mu je kiyi sallan isha" Babu yanda Mayraah ta iya haka ta mike ta bi bayanta suka fita parlon zuwa part dinta, bayan tafiyarsu with few minutes Usman ya ajiye spoon din hannunsa, Abba yace "Are you satisfied" Usman bai yarda ya kallesa ba, kansa na kasa yace "Sure... dama Abba akwai maganar da nake son zan yi maka" Abba na kallonsa yace "Ohk, i am all ears barrister" Ganin yayi shiru kamar me tunanin ta inda zai fara maganar Abba yace "Ina jin ka Usman, tell me what is it" Usman ya daga kai a hankali ya kalli Abba.....