Sashe 41
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
kai yayi sau uku, to kinji dalilin fasa auren" Shiru Haseenah tayi tana kallonta, lkci daya tana kokarin fahimtar abinda take ce wa, sai taji kamar ba hausa ma take mata ba, Badiyya tayi wani shegen dariya tace "Ya naga kin ƙame? to wllh shock din nan da kika shiga bai kama kafar nawa ba da na samo labarin wacece Mayraah, sai da nayi kwana hudu cikin shock da wasi wasi a raina, at first na ma kasa yarda in gaya maki amma daga karshe that is just it, wllh babu abinda Mayraah ta hada damu tsintattciya ce don ki ji ma in gaya maki, abinda yasa ban gaya maki ba tun a lokacin da na sani, ina tsoron kar kije ki gaya ma Maheer don hatta shi bai san cewar Mayraah ba kanwarsa ta jini bace kilan duk sai yau za su sani, Ammi da Abba suka boye wannan sirrin kusan shekara ashirin da biyu babu wanda ya sani ko da wasa" Haseenah da taji kanta na juya mata ta dafa Badiyya ta samu gefen gado ta zauna tana haƙi, Da mamaki Badiyya tace "Meye haka ke kuma? Duk shock din ne haka?" Haseenah da har zufa ya fara ketowa mata ta ko ina a jikinta tayi karfin halin cewa "Yanzu kina nufin da aure tsakanin Mayraah da Maheer?" Shiru Badiyya tayi tana nazarin abinda Haseenah tace, lokaci daya ta zaro ido after realizing what she said really made sense, Badiyya ta zauna gefenta da sauri tace "Kin ji ki da wata magana, shi yanzu Maheer don bashi da kai sai yayi sha'awar auren warce for 22 years yake ma kallon kanwarsa ta jini? Ta yaya haka ma zai faru? Ashe ma kenan sha'awar kanwar tasa yake duk ba a sani ba all this while" Haseenah ta fashe da matsanancin kuka tace "Na shiga uku na lalace Badiyya, ni kika yi ma wannan abu ba wani ba, ni kika cuta ba kowa ba, ashe dama wnn ne yasa tun farko naji na tsani yarinyar nan ban san dalili ba" Badiyya ta tabe baki tace "Ke dai kin cika fitina wllh, yanzu baza ki daina wannan kazamin maganar ba Haseenah, ta yaya ma Maheer zai yi sha'awar auren Mayraah sai kace wani ɗan iska, ashe ma kenan ba kallon kanwa yake mata ba a gidan, misali ma idan ya zama ɗan iskan ai ita nasan ba er iska bace Mayraan, baza kuma ta taɓa amincewa da wnn tabargazan ba balle shi kansa nasan bazai yi hakan ba kawai silly thought dinki ne, kamar kece fa rana guda a tashi ace Sufyan ba yayanki bane kawai sai yayi sha'awar aurenki ko ke kiyi sha'awar aurensa? kinga ni don Allah kar ki lalata min farin cikina let me go home and know my next move" Tana kai wa nan ta mike ta fice daga dakin ita tsabar farin ciki ta ma mance da batun Gold a yanzu dai, Haseenah ta mike tsaye har sannan hannunta na daure a kanta ta dinga zaga dakin tana cewa "Na shiga uku na lalace, Badiyya ta cuce ni...." Tun Mayraah na dakewa tana masa magiya ganin tafiya kawai suke for almost 35 mins now a motarsa har dai ta fara masa kuka ta marairaice tace "Don girman Allah sir kayi min magana, why are you quiet? And where are you taking me to? Ba fa a san na fito daga gida ba, yanzu fa magariba zai yi" Har sannan Musharraf bai ce mata komai ba, driving dinsa kawai yake idanuwansa da suka kada na kan titi, gashi ba a hankali yake tafiyar ba, ita bata ma taɓa ganinsa a wannan yanayin ba, wannan yasa taji gabanta na ta faduwa ta kasa sukuni tana ta kallonsa hawaye na sauka idonta, duk wannan magiyar da take masa bai ma san tana yi ba don yayi nisa tunanin da ya tafi, yasan definitely bata san me ke faruwa ba har yanzu, idan kuma tasani she will get distablize and Depress, taji komai ya fita a kanta daga karshe ta karya alkawarin da ta daukar masa taki amincewa da shi, don haka kafin ma hakan ya kasance zai yi abinda zai sa she won't have any other choice then being with him forever, he will leave her with no choice sai na zama tare da shi as mijinta.....