← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 308 OF 313

Sashe 308

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ur evidence via 07087865788 Usman ya zauna side din gadon calmly yace "You need not to be Tensed Mimi, Musharraf na sonki, kema kina sonsa, beside kun yi ma juna alkawarin aure, so stick to that promise, kar ki ji komai a ranki kin ji Lil sis, be a good gal ki tashi ki shirya ki fito yanzu" Lokaci daya hawaye ya cika idonta tana kallonsa, yace "Yeah dress up ki sakko downstairs, everyone is there" Ita dai bata ce masa komai ba, ya mike ya fita daga dakin, da kyar Mayraah ta iya sauka daga kan gadonta ta shirya ta dau veil dinta ta yafa sannan ta fito daga dakin walking slowly, a corridor suka hadu da Maheer da ya hauro sama a lokacin, yana kallonta yace "What happened Mimi? Ba ki zo ki gaishe su ba" Ta sauke idonta tace "Yanzu na gama shiryawa" Yace "Ohk, mu je" tana tafiya a hankali ta wuce sa sannan ya bi bayanta suka sauka downstairs, kanta a kasa ta isa har cikin parlon ta zauna kasan lallausan carpet dake shimfide a kasa ta gaishe da duk occupant din dake parlon, suna hada ido da Mom dinta bata san sanda ta mike ta nufeta ta zauna kasa kusa da ita tana kallonta tayi murmushi a hankali ta kara gaisheta, Ita dai Ammi na zaune kusa da Aunty Mariya, Mama Ladi sai washe baki take ganin Alhaji Saminu da ta saba gani a hoto kawai, banda sai da Ammi tayi mugun kwabarta da yanzu ta cika parlon da zance, yanzu kam ba dama sai murmushi take yi kamar sabuwar amarya, Abba na zaune shi ma tare da ɗan uwansa na lagos wanda shi ya bar ma gidansa na kano dake kurna suke zaune da iyalansa, Alhaji Saminu da brother dinsa wanda shi ne yayi ja gaba wajen amso kudin auren Musharraf wajen Abba, sai sinne kai yake ya kasa hada ido da Abba a parlon tun bayan dai da aka gaggaisa, Abdallah ma na zaune parlon idonsa a kan Mayraah, Hajiya Ramatu da Mamin Musharraf ma duk suna zaune waje daya, Drinks da fruits iri iri ne ajiye tsakiyar parlon sai small chops, a hankali Mayraah ke bin parlon da kallo taga babu Musharraf balle yayansa MD, ta kalli Usman da yayi mata alamar she should be calm don kallonta kawai zaka yi ka gane bata cikin nutsuwa, ta sauke idonta kasa sai kuma ta kalli Maheer, murmushi me kwantar da hankali yayi mata, yayi nodding mata kansa as if giving her assurance, hakan ne ya sa ta ɗan samu nutsuwa a parlon, Alhaji Saminu na kallon Abba yace "To Alhaji Mahmud ni kam ina da flight to catch to Germany zuwa karfe biyu, don haka ku muke saurare mu ji hukuncin da ku ka yanke akan batun auren er ku da ɗan mu" Yana murmushi ya kare maganar, Ceo dake kallon Alhaji Saminu, calmly tace "Ohk i think in za a bani dama i have something to say Alhaji" Abba na kallonta ya gyada kai yace "Yes go on Madam... duk muna sauraronki" Ceo tace "As of 2 days ago na tuntubi Mary ann akan maganar auren nasu da shi yaron, i want to know ko da akwai wani abu dake zuciyarta daban nace ta gaya min tsakani da Allah, sai ta kawo min maganar cewar shi yaron yayi blocking dinta ma a waya, so a ranan yayansa ya zo gidana, sai tayi amfani da wayar yayan nasa ta kirasa...." Ceo tayi shiru tana kallon Mayraah dake kasa kusa da uwarta, tace "Mary Ann say it to everyone now, ya ku ka yi da shi a waya?" Mayraah ta daga kai tana kallonta, nan da nan hawaye ya cika idonta, Ceo tace "Yes say what he told you" Ta sunkuyar da kai tace "Ce min yayi shi ya hakura kawai" Duk kowa na parlon kallonta yake, Ceo ta kalli Alhaji Saminu tace "Babu ta yanda zai ce ya hakura bai yi shawara da ku ba Alhaji, definitely duk kun san da wannan batun, sannan kudin aure ku ke shirin kai masa wani wajen kamar yanda ya gaya mata, let be sincere plss sir is it necessary kuma ku zo jin abinda iyayenta za su ce bayan ku can kun riga kun gama yanke hukuncinku gashi har yaron ya gaya mata, the shocking part of all this is that ya ma riga yayi blocking dinta a waya wanda hakan ke nuni da he have nothing to do with her again, a kaddara ma duk bai sanar maku ba, a wannan era din kun ga ana ma yara dole?" Ceo ta kalli Mayraah tace "Bayan da kika ce min yace maki shi ya hakura, wani hukuncin kema kika ce min kin yanke ta bangarenki?" Mayraah tayi shiru, Ceo tace "Answer me Mary Ann" a hankali tace "Cewa nayi nima na hakura" Ceo ta kalli su Alhaji Saminu tace "So baza mu yi forcing dinsu su yi aure su zauna da juna ba saboda zumunci or anything of such, shi yasa wancan ranan nace kilan an samu changes a zuciyoyinsu baza mu yanke masu hukunci nan take ba, and truly i am right" Kallon Ceo kawai Alhaji Saminu da su Abba suke, ita dai Mamin Musharraf direction daban take kallo a Parlon, alamu sun nuna Alhaji Saminu is totally speechless, quite alright Musharraf ya fada masu hakan amma shi yana da dalilinsa na furucinsa kuma ta wani bangaren da gaskiyarsa baya son a sake breaking heart dinsa ne don gani yake kamar baza a bashi ita ba, su kansu sun yi wannan tunanin duba da yanda aka ki bari a daura auren a lokacin, amma basu yi tunanin zai yi saurin gaya ma yarinyar wannan maganar ba don jira suke su fara jin decision din su Abba tukunna, zai yi magana a parlon Abba ya rigasa bude baki yace "Toh shikenan, Allah Ubangiji ya sa hakan shine mafi alkhairi, it's good he spoke out, amma kafin a tashi a nan a matsayina na ubanta, zan daura mata aure da nawa zabin da nasan will be best for her, don tun farko niyyata idan kun zo yau baza mu tashi ba sai an daure auren kamar yanda ku ka so wancan ranan, so now in the absence of Musharraf ni zan aura mata nawa zabin wanda nasan zai zama alkhairi gareta in sha Allah, kai Alhaji Saminu zaka zama waliyyinsa, ni kuma waliyyinta, ga kuma shedu" Kowa na parlon kallon Abba yake with shock, barin Ceo da ta buda baki cause she never saw it coming, Mayraah dai tun da ta daura kanta saman kafar uwarta bata dago ba, kokari kawai take tayi assimilating maganganun Abba amma ta kasa, da gaske bata fahimci abinda yake cewa ba har cikin ranta, Ammi dai gabanta sai faduwa yake tana kallon Abba, Alhaji Saminu da ya hadiye maganarsa da yake kokarin yi na kare Musharraf kafin Abba ya rigasa buda baki, saboda kara da mutuntawa kawai yayi murmushi yana gyada kai yace "To ba damuwa Alhaji, hakan ma dai dai ne, sai a yanke mana sadakin da ɗan namu zai gabatar, in sha Allah sai in bayar...." Abba ya kalli Ammi da ta kasa daina kallonsa, sauke idonta tayi a hankali ta mike tsaye sai kuma ta kalli su Hajiya Ramatu da Ceo tana murmushin karfin hali don har ta fara jin alamar jininta ya hau tace "Mu shiga daga ciki" Aaria ta mike ta dago Mayraah da har sannan ko motsin kirki bata yi tun da taji furucin Abba, duk suka bar parlon gaba daya zuwa sama, Abba dai ya bi Mayraah da kallo har suka haura sama... Mayraah na jikin Mahaifiyarta a parlon Ammi tana sauke numfashi a hankali, sauran baƙin kuma suna parlon dake sama gaba dayansu, Aaria ta dago kan Mayraah tana kallonta ganin hawaye idonta ga jikinta har ya fara zafi, a hankali Aaria tace "Kin san dai Abbanki bazai cutar da ke ba ko Baby?" Mayraah ta gyada mata kai da kyar wasu hawayen na zuba idonta, ga wani mugun faduwa da gabanta yake, rabon da ta shiga irin wannan yanayin da take ciki yanzu tun bayan fasa aurenta da Musharraf bayan ta gano ba su Ammi bane asalin iyayenta, Aaria ta kara rungumeta tana patting bayanta a hankali cikin rarrashi, Mayraah ta lumshe ido still breathing slowly, suna nan a haka da uwarta har bayan minti talatin Ammi ta shigo parlon, Aaria ta daga kai tana kallonta, Mayraah dai taki bude ido gabanta na wani irin bugawa duk da bata san waye ya shigo parlon ba, Ammi ta sauke idonta ta karasa cikin parlon ta zauna tana kallonsu cike da karfin hali tace "Maryam, ana magana da ke a parlon Abbansu" Aaria dake kallonta tace "Ohk" Dago kan Mayraah da ta bude ido tayi, sannan ta mike Ammi na kallonta ta bata direction din inda zata bi taje parlon Abba, Aaria tace "Ohk" Daga haka ta nufi kofa ta fita daga parlon tana waigo Mayraah, bayan Aaria ta fita Ammi ta kalli Mayraah da ta sunkuyar da kanta, mikewa tayi ta koma kusa da ita ta zauna ta jawota bossom dinta tana shafa gashinta tace "ki shiga dakina kiyi alwala kiyi sallah, bari in gama serving baƙi abinci, they will be leaving soon" Mayraah ta gyada mata kai kawai ta mike ta shiga dakinta, Ammi ta bi ta da kallo a sanyaye sannan ta mike ta fita daga parlon, she is just trying to be okay too saboda bakin dake gidan, Tun da Mayraah ta idar da sallah take zaune kan darduma for almost 30 minutes now, har a lokacin kuma gabanta yaki daina faduwa kuma gashi babu wanda taji yace mata komai a gidan, a ranta kawai sai tayi assuming kilan Abba ya canza shawara ne daga karshe yace a bar auren tukunna, wanda tunanin hakan ya sa taji ta dan samu relieve a zuciyarta, probably ceo ta kara convincing Abba a bar batun auren nata tukun, tana ta zaune a dakin Ammu taji an bude kofa ta daga kai da sauri, Aunty Mariya ce ta shigo da abinci ta ajiye mata, Mayraah dai sai kallonta take tana jiran taji ko zata ce mata wani abu amma Aunty Mariya bata ce
Chapter 308 · 0% Book details