Sashe 52
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
almost Magrib, i will be going to mosque too" Yana fadin haka ya mike ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita daga dakin, tun farkawanta a asibiti sai yanzu tayi feeling a bit relieved daga damuwar da suka yi layi a zuciyarta, a hankali ta mike ta fito parlor ta shiga bandakin dake ciki don yin alwala. Mayraah ta idar da margrib bayan duk ta rama sallolin dake kanta tana linke darduman da tayi sallan Aunty Mariya ta shigo parlon, duk bata san Mayraah na gidan ba sai yanzu da Maheer ya sanar mata bayan ya dawo daga masallaci, dama Usman kawai ya gaya ma tun dawowarsu, Mayraah ta sunkuyar da kanta ganin Aunty Mariya, Aunty Mariya ta nufeta ta rungumeta cike da farin ciki tace "Welcome back home daughter, Maheer bai gaya min kun dawo ba sai yanzu, hope you are feeling much better now?" Mayraah ta gyada mata kai, Aunty Mariya tace "Toh Alhamdulillah, mun gode ma Allah, naga heater din bandakin nan baya yi bari in kawo maki ruwan zafi kiyi wanka ki canza kaya, ki ci abinci yanzu" Mayraah dake kallonta a hankali tace "Aunty, Ammi fa" Aunty Mariya tayi murmushi tace "Kina wanka in kin ci abinci zaki je ki dubata, yanzu bacci take" Aunty Mariya ta zaunar da ita kan kujera tace "Let me get you the hot water dear" Daga haka ta fita daga parlon, dai dai nan yan kawo Haseenah suka iso gidan a motoci biyu, da yake family din nata masu hankali ne sun san abinda ke faruwa ba a wani yi zugan kawota ba, don bai fi mutum bakwai bane suka taho da ita.... Aunty Mariya bata tsaya an amshi Haseenah da ita ba don duk hankalinta na kan Mayraah, tuni ta kai mata ruwan zafi bangaren visitors, ta surka mata ruwan da kanta a bandaki, dama ta taho mata da sosonta da shower gel da towel, bata bari kowa yasan Mayraah na gidan ba, bayan Mayraah ta shiga wanka ta sake komawa cikin gida ta dauko mata kayan sawanta da kayan shafe shafe, nan parlon ta ajiye mata don ta gani idan ta fito daga bandaki sannan ta sake komawa cikin gida hado mata abinci da shayi, she is so happy yanayin da ta ga Mayraah kamar ba ita dazu ba.. Mayraah ta fito parlon daure da towel tana kallon kayan da Aunty Mariya ta ajiye mata kan kujera da turarrukanta at the same time tana tunanin inda zata samu waya ta kira Dr Musharraf, bude kofar parlon aka yi ta juya taga Usman, lkci daya ya juya ya bi gefen Maheer dake bayansa shi bai kai ga shigowa parlon ba, Maheer ya bi sa da kallo ganin ya fito, bai dai ce masa komai ba ya shiga parlon shi ma, Tuni dama ta durkusa kasa tana zare ido, Maheer yace "Ohh sorry, finish wearing ur clothe" daga haka ya juya ya fita, ta kwashe kayan ta shige daki da sauri. Haseenah na zaune dakin da Hajja da Mama Ladi suke an shigo da ita ta gaishesu Aunties dinta uku na zaune gefenta, Hajja dai ta sa mata albarka sannan tayi mata nasiha irin ta manya a takaice, daga karshe tana murmushi tace "Allah kuma ya baku zaman lafiya da zuri'a dayyaba, Allah ya sa gidan zamanki ne na har abada, Allah ya albarkaci auren...." duk yan dakin suka amsa da "Ameeen ya Allah" Mama Ladi ta ajiye kwanon tuwon da take ci tace "Sai dai kuma anyi biki duk bama cikin kwanciyar hankali muna cike da alhinin abinda ya same mu, don da an biye ta Mashir ma ɗaga bikin nan za ayi sai xuwa duk sanda Allah ya nufa, don bakina da nasa yace min lafiyar kanwarsa ta fiye masa wannan auren shi, ta yaya zai yi aure kanwarsa na gadon asibiti, mu dai muka ce ya rufa mana asiri kar ya maida mu kananun mutane a idon duniya ayi ta yamadidi da mu, magana ta zama biyu a kanmu, ga na Mera ga na Mashir" Sake baki Hajja tayi tana kallonta cike da takaici, ba Hajja kadai ba duk yan uwan Ammi da suke dakin haka suka sake baki suna kallon Mama Ladi cike da mamaki, Haseenah ma ta dinga lekota ta cikin mayafi tana jin zuciyarta na bugawa don ita kanta ai ya gaya mata makamancin haka a waya, wato ashe da gaske ma yake??? Mama Ladi ta dau ƙashin dake kwanon abincinta tana gwagwiya tace "Mu kanmu tun safe bamu gansa ba yana can asibiti da Mera, ko er farar shaddan biki da angwaye ke sa wa ma ban ga ya sa ba duk yau, yana ta yawo da wata jallabiya ruwan hoda ko guga babu sai daga baya nake samun labarin ko wajen daurin auren ma bai je ba, Yo banda uban nasa ma yace a taho dake yau a in don ta shine tarewarki ba yanzu ba sai sanda Mera ta farfado kin ga kuma ba rana kenan, ai yau kam mun ga jarabawa ganin idonmu, don haka nake baki shawara ki zama me kwantar ma mijinki da hankali akan wannan iftila'i da ya fada mana, ai kinsan an fasa auren Meran ko? To in gaya maki dazu matsiyatan dangin shegen da zata aura suka zo kwashe kayansu da suka kawo nan, da jefe jefe muka rabu da yan iska, nayi masu wankin soso da sabulu nace masu gayyar tsiya" Maman Shafa na kallon Aunties din Haseenah tace "Kamar baku je bangaren Ammi ba ko? Muje in kai ku nasan yanzu ta farka tunda anyi magariba" Tana fadin haka ta mike, Aunties din Haseenah da sai kallon Mama Ladi suke, har dai suka daga Haseenah suka bar dakin, Mama Ladi ta bi Maman Shafa da harara ta ajiye ƙashin hannunta cikin kwano tace "Wai ita kuma wannan katuwar dake yawo da kodadden zani da yagunannen hijabi wacece ita fisabilillahi? Naga sai shigar min hanci take da kudundune tun da garin Allah ya waye, banda taron biki me zai hadani waje daya da ita mata kamar almajira kaya duk a yamutse" Rai bace Hajja tace "Ladi ke yanzu baza ki saka ma bakinki linzami ba, wllh kar ki bari in maki koran kare daga gidan nan, kin isheni kuma haka tsakani da Allah, wannan wani irin bala'i ne baki gyara abu sai dai ki tabarbare lamari" Mama Ladi tace "Wai kiyi ta cewa zaki min koran kare yaya, ni fa gidan Mamuda nake ba gidan kowa ba, daga magana sai a juya min a fassara abinda nake nufi ta wata tsigar? Ko don anga ban haihu ba balle in aurar da jika?" Tana fadin haka ta fashe da kuka ta jawo mayafinta tana matsar kwalla ta mike ta fice daga dakin da kwanon abincinta. Mayraah na biye da Aunty Mariya suka shigo parlon Ammi, babu wanda ya lura da shigowarsu gidan don ta baya suka shigo ta bangaren Abba, Ammi na zaune kan darduma bayan Hajiya Safiyya ta cire mata drip din hannunta tayi sallah har ta idar, ta daga kai tana kallon Mayraah babu ko kiftawa don bata ma san sun dawo gida ba, nan da nan Mayraah taji hankalinta ya tashi don daga fuska zaka fahimci Ammi na jin jiki, ta karasa da sauri ta durkusa gabanta ta riko hannunta tace "Ammi are you this sick??" Ammi ta rungumota jikinta amma ta kasa cewa komai, kuka kawai Mayraah take a jikinta, Ammi ita ma hawaye ne ke sauka idonta, Babu wanda yace masu komai a dakin, cause bond din exactly irin na uwa da ɗan ta, Aunty Mariya dai na tsaye bakin kofa ta ma kasa karasowa cikin parlon duk jikinta yayi sanyi, Kwankwasa kofar parlon aka yi, Maman Shafa ta leko tace "Za a shigo da amarya wajen Ammi" Aunty Mariya tace "Ohk to ana zuwa" Aunty Mariya ta nufi Ammi da damuwa tace "Plss kiyi composing din kanki Ammi, za a shigo da Haseenah" Aunty Mariya na fadin haka zata janye Mayraah daga kusa da Ammi a hankali Ammi tace "Ki bar ta, su shigo kawai ba komai" Aunty Mariya da Hajiya Safiyya suka yi mamaki sosai don fa tun safe Ammi bata yi ma kowa magana sai dai ta bi ka da ido kawai, Aunty Mariya ta koma tayi masu iso har cikin parlon don dama an shimfida tsadadden carpet babba, Haseenah da Aunties dinta suka zauna, Mayraah dake makale jikin Ammi ta daga kai tana kallonsu, cike da karfin hali Ammi ke amsa gaisuwarsu da ya jikin da suke mata, Haseenah kuwa sai leko Mayraah take ta cikin gyale don sarai ta ganeta, nan taji bacin ranta ya ninku, wato saboda wannan er iskar aka yi bikinta kamar ana zaman makoki yau ko? Frnd din Ammi ce tayi ma Haseenah nasiha wanda Ammi zata yi mata, amma duk Haseenah bata san me take cewa ba don gaba daya hankalinta na kan Mayraah da tunani iri iri da take yi a kanta....