Sashe 156
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
rayuwar, gashi bata ji alamar Abba a gidan balle matar da ya auro, a yanda ta fahimta ma kamar ita kadae ce a gidan, da safe wajen karfe tara tana zaune kan darduman don tun dawowarta jiya bata shiga daki ba sai dai ta shiga bandaki ta dawo ta zauna kan darduman, ta daga kanta da ke mata azaban ciwo jin an bude kofa, Usman ne ya shigo Maheer na biye da shi, Ammi ta sunkuyar da kanta, Maheer ya zauna yana kallonta yayi kasa da murya yace "Ina kwana" Ammi ta kasa amsa masa wasu sabbin hawayen suka cika idonta, Usman ya zauna kan kujera shi ma yana kallonta a hankali yace "Ina kwana" Kawai ta fashe masu da kuka sosai, Maheer ya rufe ido ya bude cike da karfin hali yace "Don Allah ki bar kukan nan haka Ammi, addu'a kawai shine mafita, pls u are stressing ur health" Ammi ta katse sa hopelessly tace "Ta yaya zan bar kuka Maheer? I failed as a mother, I failed u all, i failed Mayraah, I wished i neva witness a day like this, gwara ace bana duniyar da wannan..." Kukan da take yasa ta kasa ci gaba, Usman na kallonta yayi kasa da murya yace "U didn't fail Ammi, mu kan mu shaida ne kan son da kika yi ma Mayraah, we are not in the position to question God akan abinda ya faru, dama haka Allah ya riga ya tsara babu dubaran da zai canza hakan, ki kwantar da hankalinki, in sha Allah Mayraah will be back home safe and sound, babu abinda zae sameta" Ammi dai kuka kawai take, Maheer ya mike yace "Let me get you tea" Daga haka ya fita daga parlon don yasan tun jiya bata ci komai ba, Usman ya ci gaba da kwantar mata da hankalinta don abun sai yayi masu yawa kuma idan Ammi ta kwanta ba lafiya, it's better su dinga lallabata suna kwantar mata da hankali. Da yammacin ranan Maheer na zaune wani eatry da goran ruwa a gabansa, ya fi awa daya zaune eatry din, ya kalli agogon wrist dinsa for d countless time dai dai sanda Musharraf ya shigo eatry din, Musharraf na hango Maheer ya nufi inda yake zaune, ya basa hannu suka gaisa sannan ya zauna kujeran dake facing dinsa, Maheer yace "Sorry nace mu hadu nan Dr ban san ko na shiga hakkin ayyukan ka ba, i am so sorry for the inconvenience this might have cause you" Musharraf yace "Never mind, i am all ears" Maheer na kallonsa calmly yace "Dr nasan Mayraah tana wajen ka, babu inda zata je da ya wuce wajen ka, don babu wanda ta sani sai kai, and tayi hakan sau uku kenan if i am not mistaken, but if i may ask pls idan kanwarka ce Mayraah zaka ji dadin wani saurayi ya dinga bata shelter ko yana hosting dinta saboda wani issue ya faru a gidansu?" Kallonsa kawai Musharraf yake, can yace "Ban gane abinda kake nufi ba" Maheer yace "Mayraah is missing since yesterday kuma babu inda zata je tun jiya har zuwa yau da ya wuce gun ka, you know her whereabout don haka kaji tsoron Allah, abinda baza ka so ayi ma kanwarka ba kar kayi ma kanwar wasu, at the first place ma in taje wajenka me ya kamata ace kayi as a responsible guy? That aside pls kai ba musulmi bane? Ta yaya ma zaka ci gaba da relationship da yarinyar da iyayenka suka ce baza ka aura ba in dai ba wata manufar gareka a zuciya game da ita ba? Meye amfanin relationship din da kai kasan will neva lead to marriage tsakaninku tunda iyayen ka sunce baza ka auri mara asali ba? Why not go ur way and leave the innocent girl alone pls?" Mikewa Musharraf yayi ya buga table din gabansu yace "You are talking bullshit, da nasan kirana kayi ka bata min lokaci baza ka gan ni a nan ba Malam" Daga haka ya juya ya bar wajen a fusace, Maheer ya bi sa da kallo har ya fice daga eatry din. Musharraf na shiga motarsa maganganun Maheer suka dinga masa yawo a kai zuciyarsa na bugawa, Mayraah bata gida tun jiya? To ina ta tafi? Since yesterday yake ta kiran wayarta switch off, har he was planning on coming to their house to check on her today, sosai kalman Mayraah bata gida tun jiya da Maheer ya fada yayi distablizing dinsa, da kyar ya iya jan motar ya bar parking space din eatry din yana tunanin to ina ta tafi, sosai yaji hankalinsa ya tashi, Maheer na fitowa eatry din ya kira Abba yace "Abba mun hadu da shi, ya ki saurarana, wanda hakan ke nuni da truly suna tare da Mayraah...." Abba da ke ta jiran kiran Maheer tun dazu yace "Turo min numbersa, i will get him arrested immediately, his parent were the root of every problem occuring now, i wil surely get him arrested a yau din nan har sai ya fito min da daughter na...." Maheer ya tura ma Abba number Musharraf, babu bata lokaci Abba yayi making few calls nan da nan aka fara tracking Musharraf.....