Sashe 165
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ur evidence via 07087865788 Washegari da safe Mayraah ta sake komawa gun me pos din a tasha, kamar jiya ma yau Nose mask ta saka don gaba daya a tsorace take da Abujan gani take kawai zata yi jamming wanda ta sani, wajen karfe goma da rabi ta isa shagon nasa, bayan sun gaisa yace "To yanzu zan bar yaron shagona ya jire min shagon sai mu kama hanyar sulejan ki ga gidan Hajiya...." Mayraah tace "Toh shikenan, nagode" Mayraah bata yi tunanin haka Sulejan ke da tafiya daga cikin Abuja ba, don har bayan minti arba'in bata ga sun isa ba, though is not as if she cares about the distance tunda babu abinda ma zata dinga shigowa garin Abujan tayi, at last dai suka iso garin Suleja ya tare masu adaidaita sahu suka tafi anguwan da yace mata gidan yake, anguwar dai ba laifi amma duk yawancin gidajen unguwan na average class ne har ma da lower class, suna isa gidan da aka kama mata bayan ya shiga da ita ko ina tare da wani agent sun nuna mata suka fito compound din gidan yace "Toh ya kika ga gidan ya maki kuwa Hajiya?" Mayraah da bata da choice kawai tace "Eh yayi" Agent din ya bata makullin gidan da reciept din payment ta saka a handbag dinta, bayan ya tafi Mutumin da ya kawota yace "Kin ga ai anguwan bata da hayaniya ko? Ga shi kuma a cike yake da jama'a" Mayraah tace "Haka ne, yayi kam" Yace "Kuma gidan kin ga sabo ne dal bai da matsala" Mayraah tace "Eh duk na gani, amma kasan abinda zai faru? Don Allah idan baza ka damu ba ina son in baka list din wasu abubuwa ka taimaka min ko a kasuwan garin nan ne ka siyo min, gobe nake son zan dawo gidan gaba daya" Yace "Toh babu matsala kamar me da me kenan kike bukata" Nan Mayraah ta zayyane masa duk abubuwan da zai siyo mata a kasuwa na bukatar gida har da kayan abinci, ta mika masa Atm card dinta yace "Aa Hajiya, da dai kawai ki min transfer" Tace "Kar ka damu, bana iya transfer ne shi yasa" Yace "Toh amma fa mantuwa gareni, kyau kawai muje kasuwan tare Hajiya" Ta ɗan yi shiru tana nazari, sai kuma tace "Toh shkkn mu tafi" Tricycle suka samu zuwa kasuwan. kafin yamma Mayraah ta siyi duk wasu abubuwan da tasan zata bukata a gidan tare da mutumin da yace mata sunansa Aminu, har gas da few kitchen utensils sai da ta siya, da labule da aka dinka masu sharp sharp a kasuwar suka siya da karafen labulen, wajen karfe biyar da rabi tana kallon Aminu bayan ya gama saka mata labulen karshe tace "Gaskiya Nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi" Yace "Ameen Hajiya, amma yanzu abinda zai faru ya kamata ki ɗan shiga makotanki ku gaisa su sanki ki ce masu ke daliba ce, yau kika dawo unguwan, kinsan yanzu yan sa ido sun yi yawa a duniyar kar su yi zaton ko zaman kanki kike a nan bayan basu san karatu ya kawo ki garin ba" Mayraah dai tayi shiru tana kallonsa, a hankali tace "Haka ne, zan shiga in sha Allah amma sai gobe idan na dawo nan din gaba daya, yanzu na gaji ina son mu koma Abuja ne in hutu sannan in harhada kayana na can" Yace "To ba laifi Hajiya, in dai da wani abu da kike bukata ko na aike koma na menene kawai ki buga wayata, in kin dawo nan din gaba daya har iyayena zan hada ki da su da matana duk da dai gaskiya anguwansu da nisa daga wannan anguwan, sai a dinga zumunci" Mayraah na murmushi tace "Toh shkkn, in na dawo din duk sanda kake da lokaci ko kuma in ka shigo garin sai ka hadani da su" Yace "In sha Allahu kuwa, Allah kuma ya baki sa'an abinda kika zo nema" A hankali Mayraah tace "Ameen nagode" Sai kusan shidda da wani abu suka shiga garin Abuja, Mayraah tayi tayi da shi ya tsaya ta ciri kudi a wajen wani me pos ta basa yace mata wllhi wanda ta basa ma ya isa saboda Allah yayi mata, taji dadin hakan har ranta, she really appreciate him, ta samu adaidaita sahu da ya maida ta hotel don duk ta gaji. The next day Mayraah tayi check out daga hotel din ko kwanakin da aka biya mata bai cika ba ta koma sulejan wajen karfe sha daya na safe, zaunawa tayi a gefen gadon dakin tana bin ko ina da kallo, tun barin ta gida sai yau kawai taji tunanin yayyinta ya cika zuciyarta, ita kanta tasan tana kewansu, this made her feel so down tun safe take jin ranta babu dadi, lokaci daya ta ba kanta courage ta shiga kitchen ta dafa Indomie wanda har ta mance rabon da ta ci Indomie, kamar yanda Aminu yace mata gidan kam da wuta don har suka gama abubuwan da suke yi jiya ba a dauke wuta ba yanzu ma gashi da ta zo ta tarar da wuta, ta jona wayarta a caji sannan ta saka hijab ta fito zata yi yanda Aminu yace mata, karamin gidan dake gefen nata ta fara kwankwasa gate din aka bude, matar gidan na kallonta daga sama har kasa tace "Sannu da zuwa" Mayraah tace "Ina kwana" Matar ta amsa still tana kallonta irin ban sanki din nan ba, Mayraah tace "Ni neigbor dinki ce, jiya na dawo wancan gidan..." ta fadi haka tana nuna gidan, Matar tace "Ayya, Allah sarki, bismillah sannu da zuwa baiwar Allah, ai ko naji yan anguwa sun ce an tare a gidan ni dai ban ga kowa ba, ashe kuwa da gaske ne" Mayraah dai ta bi ta har cikin gidan ta zauna kan kujera a karamin parlon ta kara gaisheta, matar ta amsa da fara'a tace "Sannu da zuwa anguwanmu, ya sunanki?" Mayraah bata san sanda tace "Ilham, sunana Ilham.... ni daliba ce ina karatu ne cikin garin Abuja, shine aka samar min daki a nan in zauna" Matar tace "Allah sarki, toh Allah ya baki sa'a Ilham, ai ko zaki ji dadin zama cikinmu wallahi duk bamu da matsala, ni ana ce min Maman Hanan, yanzu zan zaga dake duk sauran gidajen a san juna" daga haka ta mike tace "Bari in dauko maki ruwa ki sha sai mu tafi" Mayraah dai sai kallon yarinyar dake kwance da bazata wuce shekara 8 ba tana numfashi ta baki take, har matar ta dawo Mayraah ta kalleta tace "Bata da lafiya ne yarinyar can?" Matar ta sauke ajiyar zuciya tace "Wallahi Hanan ba lafiya yau kusan sati daya ko makaranta bata zuwa, tun dazu ma nake ta goge mata jiki da ruwan sanyi don naji zafin yau na daban ne da sauran ranaku, gashi zazzabin baya sauka wallahi" Da mamaki Mayraah tace "Kuma ba a kai ta asibiti ba har yanzu Aunty?" Maman Hanan tace "Baban magunguna ya siyo mata a chemist ake ta bata, wanda ya fara siyowa har sun kare ya sake siyo wasu" Mayraah couldn't stop looking at the woman with surprise, a ranta tana mamakin me yasa wasu iyayen ke irin wannan sakacin ace yaro bai da lafiya critically amma sai a wani je chemist a siyo masa magani, mikewa tayi ta tafi kusa da Hanan din ta durkusa tana kallonta don ko rufe baki bata iya yi kamar warce mura yayi ma mummunan kamu, and she is breathing noisily, Mayraah ta bude bakinta tana duba ciki, lokaci daya ta mike tana kallon Maman Hanan tace "Ya kamata a tafi da ita asibiti yanzu Aunty" Da damuwa Maman Hanan tace "Ko?" Mayraah tace "Gaskiya, a nemo adaidaita sahu a tafi asibitin kar a bata lokaci" Wani irin numfashi Hanan din ta fara yi, Maman Hanan ta maza ta dauketa tana jijjigata tace "Haka fa take yi tun dazu sai numfashin yayi kamar zai dauke wllh sai ya dawo, bari in kira baban nasu" Mayraah tace "Mu je kawai asibitin idan mun je can sai ki kirasa" A tare suka fita gidan, Maman Hanan duk ta gigice ko kulle gidan bata yi ba suka nufi titi, Mayraah dai bata karbi yarinyar a hannunta ba, a haka suka samu adaidaita sahu, wani Asibiti nesa da Sulejan Maman Hanan ta sa mai adaidaita sahun ya kai su, duk tunanin Mayraah zata ga babban asibiti saboda taga wajen da ɗan tafiya daga suleja, kawai taga clinic, though ba laifi kamar clinic din sananne ne don taga patients da yawa amma bata tunanin the clinic is well equipped suna isa entrance din clinic din basu fara karo da kowa ba sai Dr Khalil yana kokarin fitowa rike da makullin Motarsa, kallon mamaki yake ma Mayraah kamar yanda ita ma take kallonsa da mamaki, Maman Hanan ta saki ihu don taga kamar numfashin er yayi sama bai sake dawowa ba, Dr Khalil ya saka makullin motarsa a aljihu da sauri ya amshi Hanan din a hannunta ganin condition din da ta shiga ya juya ya koma cikin asibitin sauran nurses suka nufosa, Mayraah ta bi bayansa da sauri har ta isa dai dai wajensa tayi kasa da murya tace "I think it's Diphtheria, symptoms din ne..." Da sauri ya juya ya kalleta, ya kalli yarinyar hannunsa, amma saboda babu lokacin batawa kawai ya shiga da ita emergency dake reception wani likita da ya fito office ya bi bayansa da sauri, Mayraah ta koma gefe ta tsaya Maman Hanan kuwa sai kururuwa take a reception din nurses na bata hakuri, Dr Khalil na shiga emergency din kawai abinda Mayraah ta fada yasa hankalinsa bai kwanta ba ya saka safar hannu, da few protections sannan ya fara gwaje gwaje, nan ya tabbatar da abinda Mayraah ta fada haka ne, Likitan da ya shigo wanda shine me asibitin shi ma ya koma baya closing his nose with nose mask ya buda ido sosai yace "Diphtheria, wannan sai dai a tafi da ita Abuja Dr.... Babu facilities a nan" Dr Khalil bai cire protective gown din jikinsa ba ya dau yarinyar ya fita daga emergency din, kawai ya nufi motarsa Maman Hanan ta bi sa a guje tana cewa "Ina za a