← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 194 OF 313

Sashe 194

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mayraah ta sauko daga kan gadon da take kwance bayan tafiyar karime da kusan minti sha biyar, wayarta ta dauko ta bude second sim din da ta kashe tun dazu, ta zauna gefen gado tana ta kallon wayar as if contemplating to call him again or not to, after many minutes of thinking ta ajiye wayar a hankali ta mike ta shiga bandaki, wanka tayi ta fito, tana cikin dauko daya daga dogayen rigunan bacci da ta siya a Suleja cikin jakarta taji wayar ta na vibrate, ta dauko kayan baccin ta mike tana gyara daurin towel din jikinta ta karasa kusa da wayar tana duba me kiranta, sai da gabanta ya fadi ganin number Musharraf, ta zauna gefen gadon a hankali ta dau wayar tana kallo, har ya katse bata daga ba, ya sake kira nan ma bata daga ba har ya gama ringing, sake kira yayi this time around sai ta daga ta kai kunne tayi shiru, daga daya bangaren ta ji yace "Pls who is this?" Ai bata san sanda ta zamo kasa ta zauna ba, she just realized she missed him so very much, ta kasa cewa komai zuciyar ta na bugawa, daga daya bangaren yace "I know u can hear me, pls say something...." Mayraah ta jinginar da kanta da gado a hankali tace "Good evening" Musharraf ya mike tsaye daga zaunen da yake yace "Mayraah" Shiru tayi bata ce komai ba, ya marairaice mata yace "Plss tell me kina ina Mayraah?" A hankali tace "Ina lafiya" Trying all best to be calm yace "I know, yes i know, amma plss ki gaya min inda kike trust me, tell me pls Mayraah, just trust me pls" Lkci daya ya birkice mata, Ta langwabar da kai tace "You don't worry about that" Yace "Nooo pls, Mayraah kin san halin da kika tafi kika bar ni ciki kuwa, not only me, ur brothers, ur parent, haba Mayraah, pls i am begging u ki gaya min inda kike, Baby don't u trust me?" Mayraah ta lumshe ido ta bude tace "I am somewhere far away, kar ka damu tunda ka ga na kira ka i am fine, and i just wanted to say hi...." A hankali yace "Mayraah" bude kofar dakin taji anyi ta juya da sauri taga Ahmad, kallonsa ta dinga yi don duk tunaninta idan ya ga yanayin da take zai fita sai taga ba haka ba, instead he is even walking in, dauke kanta tayi zuciyarta na bugawa tace "I will call you back" Bata jira cewar Musharraf ba ta katse wayar wondering dalilin da zai sa ya shigo mata daki duk da yanayin da ya ganta, she just tied a towel, gefen gadon ta ji alamar ya zauna, lkci daya ta juya ta kallesa tace "I am sorry, i want to dress up" Ya ɗan yi shiru yana kallonta, sai kuma ya buda mata hannu alamar what is there? Kasa motsawa tayi daga inda take zaune with shock amma taki nuna hakan a fuskarta, ko hijab dinta ta kasa yunkurin daukowa don dole sai ta tashi zata yi hakan, banda faduwa babu abinda gabanta yake gaba daya ta rasa wani tunanin zata yi a lokacin, silencing kiran da Musharraf yake ta yi mata tayi ta ajiye wayar a gefenta, kawai gani tayi ya dawo gabanta ya durkusa yana kallon idonta as if counting his words yace "I understand what u are going through Mayraah, Khalil briefed me earlier, it's sad and i get kin fito ne ki samu relieve by chilling away ur worries right? i love ur courage and braveness" Mayraah ta fara matsawa jikin gadon a hankali tana kallonsa babu ko kiftawa, a hankali tace "You are drunk" Buda ido yayi sosai yana gyada mata kai yace "Not much though, but how did u know? Ko kema kina sha ne?" Tayi murmushin da iyakarsa lips tace "Yeah" ya kara buda ido yace "Really?" Ta gyada masa kai tace "I won't mind some" Ya karyar da kai yace "Unfortunately I can't bring that home because of my Ummi, i drink only outside" Sosai gaban Mayraah ya fadi a tunaninta zai ce bari yaje ya dauko mata ne tasan na kwatanci, nan da nan hankalinta ya tashi, yayi kasa da murya holding on to her hand yace "Would u mind us spending the night somewhere...." Ta dake tace "Somewhere like??" Yace "Hotel, club, guess inn... And what have you" Tayi saurin gyada masa kai tace "Ohk, let me get dressed" Yayi kasa da murya yace "Thank you...." Bata yarda ta mike ba a gabansa, gaba daya idonsa na kirjinta, da sauri tace "Can u excuse me in shirya?" Yace "C'mon meye in kin shirya while am here" Daga ta zai yi ta wani fizge hannunta tace "Stop it" Ya mike yace "Ohk then" Jikin window ya koma ya tsaya ya rungume hannunsa yace "Ki shirya" Babu yanda ta iya haka ta mike tsaye, wani takaici ya tokare mata wuya, she was trying her best kar ta bari hawaye ya taran mata a ido, daukan kayanta tayi ta shiga bandaki ya bi ta da ido, sai a sannan hawaye ya fara sauka idonta ta jingina da bangon bandakin bayan few minutes ta saka kayan ta fito ta dau Hijab dinta ta saka, ta dau handbag dinta with her charger and phone, duk yana ta bin ta da kallo, without looking at him tace "I am done" har suka fita compound din gidan a motarsa Mayraah bata yarda sun hada ido ba, kamo hannunta yayi yana kallonta yace "or should we go for the hotel we met first?" Ta gyada masa kai kawai, yace "Ohk, but do u have an international passport?" Duk da tana da shi haka ta girgiza masa kai tace "Nop" Da mamaki yace "Why? Big gal kamar ki ace baki da International passport" Ta yi feigning murmushi bata dai ce komai ba, yayi kasa da murya yace "I will get you one if u don't mind, sai a maki visa ko na Uk ne don zaman kasar nan baya wani cire ma mutum damuwa a rai ga sa ido irin na malam bahaushe, u need to be far far away, i think next week zan koma i will try and see if we can make it together" Mayraah tace "Thank you" All through the ride shi yake ta surutunsa, ita kam tayi nisa tunanin da take suna isa hotel din kafin ya shiga ciki ta kallesa tace "Zan ɗan amso abu a mart din can na gaba, wait for me" Yace "Me za ki amso?" Tace "Chewing gum" Yace "Oh ok, bari in amso maki" Ta masa murmushi tace "Ai baka san irin wanda nake so ba" Yace "True" Bude motar tayi ta sauka ta kulle masa tana kallonsa tace "Not every girl that left home is a bitch, not every girl that left home is useless, don kaga na baro gida ba yana nufin ni er iska bace, kuma hakan ba yana nufin bani da tarbiya bane, i chose leaving home because of my mental health..." Tana kai wa nan tayi tafiyarta, sai a sannan wasu hawaye masu zafi suka dinga sauka idonta tana jin zuciyarta na mata zafi, ko waiwayawa bata yi ba har tayi nisa daga hotel din, tana isowa main road ta tare adaidaita sahu ta shiga ta gaya masa inda zai kai ta, har suka iso bata san sun iso ba don tayi nisa tunanin da take ga hawayen da ke ta saukan mata, sai da mai tricycle din yayi alerting dinta sannan ta sauka tana goge idonta ta basa kudinsa, tana shiga gate ta nemi kujera ta zauna, sai da tayi kukanta me isarta sannan ta ciro wayarta, missed calls din Musharraf ta gani ya fi goma, tayi dialing number Dr Khalil yana fara ringing ya daga, gaishesa tayi a hankali, ya amsa yace "Ya kike, ya gida?" Tace "Alhmdlh, are you at work?" Yace "Yeah ina night duty, Why do u ask?" Tace "Aa just want to be sure" Yace "Are you okay?" Wasu hawaye ne suka cika idonta kawai ta katse wayar, mikewa tayi taji ya sake kiranta bata daga ba ta shiga cikin asibitin, sau uku yana kiranta bata daga ba, tana shiga reception ta gaida nurses da ta gani ta haura sama zuwa office dinsa, wata nurse fa'iza ta mike da sauri ta tafi inda jakarta yake ta ciro wayarta ta fara kiran Zainab. Dr khalil na zaune still calling her line ta shiga office din ko knocking bata yi ba, yana ganinta ya mike yana kallonta, bata yarda sun hada ido ba ta zauna kan kujera, ya zagayo yace "Mayraah are you okay?" Bata san sanda ta fashe da kuka ba, ya iso gabanta da mamaki yace "Lafiya? Talk to me, me yake faruwa?" Duk da tambayoyin nan da yake jefo mata hankalinsa kawai ya tafi kan kila Zainab taje ta sameta ne a gida don not long ago ya kira Ummi tace masa tana gidan biki, ganin taki basa amsa sai kuka take ya duka gabanta yace "Plss talk to me Mayraah, an maki wani abun ne?" Bude office din aka yi duk suka juya, MD ne ya shigo, Dr Khalil ya mike yana kallonsa, Mayraah ta kauda kanta da sauri, tunda ya kallesu sau daya bai sake kallonsu ba ya ajiye files din hannunsa yana kallon Khalil yace "See me off" Dr Khalil yace "Ohk" fita yayi office din Dr Khalil na kallon Mayraah yace "I will be back right away" Daga haka ya fita daga office din ta bi sa da kallo tana goge hawayen dake sauka idonta. Dr Khalil na kallon MD bayan sun fita reception yace "Drivern ya iso ne?" MD yace "Ban kirasa ba, just drop me" Dr Khalil yace "Ni fa da na ga kayi dare na zata u will pass the night here MD" MD na mika masa makullin hannunsa yace "Ka taba ganin na kwana asibiti in ba dole ba?" Dr Khalil bai amshi makullin nasa ba yace "Sae dai mu je a motata ka bar naka a nan, tunda zan dawo asibitin" MD yace "Mu tafi a nawa sai ka dawo da shi, bazan iya jira sai kaje sama ka dauko
Chapter 194 · 0% Book details