← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 313

Sashe 71

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

mu riketa don kanwar mu ce har yau har gobe and this is our fathers house, beside ko gidana Mayraah zata zauna nobody is going to question that, dalilina kuma na maida Haseenah gida still remains between i and her, wannan tsakanina da ita ne babu wanda ya shafa, kuma babu ruwan Mayraah a mayar da Haseenah gida da nayi" Usman dai na tsaye ya rungume hannu fuskar nan tasa a murtuke tsabar bacin rai ko magana yaki yi, Aunty Mariya dai sai goge hawayen da yaki tsaya mata take, gaba daya ta ma rasa abinda zata ce, tun dazu Ammi dai ta kama hanyar zuwa gidan Hajja and this is 12pm bata dawo ba, wa ya sani ko zuwa zata yi ta ce mata ta amince babu ita babu Mayraah din kamar yanda Hajja ta bukata, Mama Ladi na tafe hannu tace "Kai in fa za ku fito fili ku buda ma ubanku abinda ke faruwa ku fito, babu wani zancen nuku nukun da za a mashi wannan karan, Hajja ce ta zo har nan da sassafe ko tashi daga bacci bamu yi ba tace zata ɗaga ma Ammi mama idan bata sallama Mera ba ta shiga duniya, fitar Hajja ke da wuya aka nemi Mera ko sama ko kasa aka rasa alamar yarinyar ta ji duk abinda Hajja ta fada a gidan nan, iyakar maganar fa kenan, duk da nasan Mera dole ta dawo duk inda ta tafi tunda babu dangin uwa balle na uba a duk inda za ta, yarinta ce kawai yasa ta bar gidan nan amma nasan tana hango magariba zata dawo shi yasa hankalina bai wani tashi ba, wancan lokacin da ta gudu ai tana ganin babu sarki sai Allah sai gata ta dawo da asuban fari, wa ya sani ma ko a titi ta kwana ranan, to yanzun ma muna zaune za ku ga ta dawo wujiga wujiga wanda ke da dangi ma ya ya kare idan ya shiga duniya balle ita da aka tsinta bakin masallaci a tsumma, sannan a buda ma Mamuda cewa Badiyya ce ta ruguza auren Mera, in ma Shari'a zai yi da ita bismillah dama ya haifi lauyan da zai tsaya masa ai, ita kuma Ammi karshen biyayya idan ta dawo muga tana watsi da kayan Mera titi taga ita ma irin koran da Mamuda zai mata, ai Mamuda ke da iko da gidansa ba ita ko uwarta ba, ko shi da 'ya yansa kadai sun isa su rike Mera, sannan nima nan ban ki in riketa in samu lada ba, sai in koma karaye in tattaro sauran kayana in dawo kawai, Mariya kuma ku bar ganin tana matsar kwalla a nan muna barin parlon nan ita ma zata saɓa gyale ta bi bayan er uwarta zuwa gidan uwarsu duk kukan munafurci take yi a nan, a yanzu gatan Mera Mamuda sai ni da ku kawai" Ficewa Usman yayi daga parlon ya tafi na baƙi don Abba na can, zaune ya tadda Abba shi kadai a parlon, tun bayan fitar Ammi daga parlon zuwa gidan Hajja bai motsa daga inda yake zaune ba don Ammi bata boyesa masa duk abinda ke faruwa ba, bai taɓa tunanin abubuwa will turn out this way at the end ba, da sun san haka abubuwan za su kasance da har ita Mayraah din baza su boye mata wacece ita a garesu ba baza su boye mata ba su suka haifeta ba, iyaka su sakaya suce iyayenta hatsari suka yi suka mutu suka tsinceta ita kadai a motar, and sun yi bakin kokarinsu basu gano relatives dinta ba, da hakan suka yi tun farko da abubuwa sun tafi smoothly, all this while Abba avoiding din Mayraah yake don bai san da idon da ma zai kalleta ba, gani yake daga shi har Ammi failed her, they disappointed her don ta taso da mentality din su suka haifeta amma all of a sudden rana daya taji ba su ne iyayenta ba, she is going through all this because of them hakan na damun Abba sosai, yanzu ko nan gaba aka samu wanda zai aureta tabon nan na rashin asali bazai taɓa goguwa a tare da ita ba, kawai he is just acting like everything is okay but deep down him he feels so sorry for Mayraah and he regret their actions, ya ma ga kokarinta duk da yasanta to be a very strong gal tun tasowarta, to yanzu ga kuma wani matsalan da Hajja ta billo da shi, Ammi kuma duk duniya babu maganar wanda take ji bayan shi da yake mijinta sai Mahaifiyarta, and her mum first in everything.... quite alright ba don Hajja ba da gidan Marayu zai mika Mayraah shi da yan anguwan a ranan da aka tsinceta duk da yanda Ammi ta nace masa a lokacin ya bar mata ita amma yaƙi har sai da Hajja ta saka baki... Bayan wani lokaci Abba ya daga kai yana kallon Usman da ya shigo parlon, Usman ya nemi waje ya zauna, Abba dai bai ce masa komai ba, after few seconds Usman yayi karfin halin cewa "Yanzu a ina za mu samo Mayraah?" Abba ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya calmly yace "Zata dawo, she will come back in sha Allah, babu inda zata je" Usman ya mike yace "But It's over 3 hours da fitar ta gidan nan fa, who knows the condition she is now??" Abba ya jinginar da kansa da kujera kamar bazai ce komai ba, can yace "Sit Usman" Usman ya koma ya zauna, Abba yace "Ga wata alfarma da nake nema gun ka Usman" Usman ya daga kai yana kallonsa, Abba ya nisa, cikin calm voice yace "Usman ina son hada aure tsakaninka da kanwarka Mayraah, i know u will protect her as ur sister, ur wife and as the orphan dat she is"
Chapter 71 · 0% Book details