← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 313

Sashe 74

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

kai, ya juya ya fice daga parlon Abba ya bi sa da kallo. Maheer ne tsaye dakin Ammi kansa a kasa duk da bacin ran dake tare da shi bai nuna a fuska ba but deep down him he is boiling and yana ta controlling kansa baya son yayi wani magana da zai kara hurting din Amminsa hankalinta ya kara tashi, gwara ya bar ta ma taji da wanda take ciki yanzu, Ammi dai sai goge hawayen da ya ki tsaya mata take maganar ma ta kasa ci gaba da yi, not long ago ta dawo daga gidan Hajja don ko minti sha biyar bata yi da shigowa gidan ba, after a 5 minutes silence tsakaninsu Maheer ya dago kansa yana kallon Ammi yace "Shikenan... Na kuma fahimce ki Ammi, for the meantime Mayraah zata koma gidana...." Ammi ta daga kai tana kallonsa, yace "Eh zata dawo gidana, a nan kuma zata zauna, Hajja don't have any say in this, ba kuma wai don Hajja zata hanata zaman nan gidan Abba bane yasa zata koma gidana don zamanta a gidan nan ma Hajja bata da say cause this is our father's house, ban san irin zaman da za ku fara yi da Mayraah ba idan ta ci gaba da zama a gidan nan shi yasa zan maida ta gidana, don haka gobe zan je gidansu Haseenah in daukota, duk sanda Hajja ta gane kuskuren abinda take kokarin yi fine, zan so ki rabu da ita lafiya, don haka ki ci gaba da yi mata biyayya...." Aunty Mariya ce ta shigo dakin da akwatinta, tana kallon Ammi cikin sanyin murya tace "Toh Ammi, ni zan tafi sai mun yi waya" Kai kawai Ammi ta gyada mata tana share hawayen da ya ki tsaya mata har sannan, Aunty Mariya ta kalli Maheer tace "Zan tafi Maheer" Sauke idonsa yayi yace "Bari in kai ki park Aunty" Fita tayi daga dakin ya juya ya bi bayanta, bayan ya kullo kofar Aunty Mariya na kallonsa cike da damuwa tace "Ku yi hakuri Maheer, kuyi hakuri da duk abubuwan nan dake faruwa, Allah zai daidaita al-amarin nan in sha Allah, sannan nasan Mayraah bazata yi nisa ba, duk inda ta tafi zata dawo a yau da izinin Allah, tunda Hajja tace in tafi gwara in tafi kawai" Shi dai Maheer bai ce mata komai ba, ta fara tafiya ya bi bayanta. A hankali Mayraah ta bude idonta, ta dinga bin dakin da take da kallo, kwance take saman gado an rufeta da lallausan farin duvet, ta mike zaune da sauri trying to recall where she is, and who brought her here, idonta ya sauka kan alluran dake kan bedside drawer da drugs, cikin few seconds komai ya fara dawo mata, ta cire duvet din jikinta zata sauka daga kan gadon taji kamar an soka mata mashi a kirjinta, dafe kirjin tayi da sauri feeling so much pain, dai dai nan aka bude kofar dakin, ta daga kai ta kallesa, tsaye yayi bakin kofar yana kallonta, can dai ya karasa yana tafiya a hankali ya isa har inda take ya zauna cikin sanyin murya yace "How are you feeling now?" Tun safe sai a yanzu taji kukan da ta kasa yi ya taho mata ta kasa controlling kanta, kamo hannunta yayi yace "Noo pls kar kiyi stressing kanki Mayraah, u need rest" Ta warce hannunta daga nasa cikin kuka tace "Saboda kasan wacece ni shi yasa kake avoiding dina yanzu kake kashe wayarka don baka son...." Dakatar da ita Musharraf yayi yana girgiza kai yace "That is the last thing i will do on earth Mayraah, and mind u tun kafin ke kanki ki san ko wacece ke na riga ki sani, kuma hakan bai sa naji kin canza a zuciyata ba, i switched off my phone for my mental health..." Tace "You are avoiding me because of ur mental health?" Yayi shiru yana kallonta kamar yanda ita ma ke kallonsa, daga fuskarsa kadai zaka gane ya rame, he doesn't even look normal, can ya juya yana kallon side daban yayi kasa da murya yace "Na ba Dr Maheer space ne ya gama maki duk injections dinki da aka yi prescribing, sannan ya kula dake kamar yanda likitan ya umarta, so i had to back off for my sanity" Kallonsa kawai Mayraah take, ya mike tsaye yana facing dinta, hawaye ne kawai ke sauka idonta tace "But that isn't enough to let u ignore me all this while, when u know i will need u the most during this hard time" A hankali Musharraf yace "Kinsan yanzu da aure tsakaninku da Maheer and Usman?" Kallonsa Mayraah take babu ko kiftawa, ya juya ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, ta fashe da kuka ta hade kanta da gwiwa, ba a dau lokaci ba ya dawo dakin da plate din abinci da ruwa, ya ajiye mata kan bedside drawer yana kallonta yace "Mayraah" Ta daga kai tana kallonsa hawaye na sauka idonta, zaunawa yayi kusa da ita yayi kasa da murya yace "I am sorry Mayraah.... u know i love you soo much, ina sonki fiye da yanda kike zato, amma the thought of Maheer made me sick for all the 3 days da kika ji wayata a kashe, i became insecure zuciyata na ta raya min abubuwa da yawa, kilan saboda abubuwan nan da suka faru Abba can just decide to get u married to Maheer or Usman, the thought of that nearly took my life this 3 days, Mayraah I can't imagine loosing u, i don't know what will become of me idan na rasa ki, kiyi hakuri ki yarda da ni mu je a daura mana aure, i promise to give u all the love in this life, i will protect you till my last breathe, u will neva regret trusting me" Mayraah na share hawayen dake sauka idonta a hankali tace "I have to because i have no option, a yanzu ina ga bani da kowa kuma bani da inda zan je, i am all alone in this life" Musharraf ya girgiza kai ya kamo hannunta yace "You are not alone Mayraah" Tana kallonsa cikin rawan murya tace "I don't know what is happening but i overheard my grandma telling Ammi to choose between i and her, she said....." Kasa ci gaba tayi ta fashe da kuka sosai, Musharraf ya jawota kusa da shi yace "It's okay Mayraah, baki ji ta bane da kyau, u misheard her, yanzu ki ci abinci ki sha magani, it's almost magrib" Yana fadin haka ya dauko abincin ya fara bata a baki, cokali daya ta ci ta girgiza masa kai da kyar tace "Bazan iya ci ba, my chest is aching" Yace "Bari in kawo maki shayi" Tashi yayi ya fita daga dakin, ta koma ta jingina da gadon all this while sai yanzu ta ɗan ji ta samu relieve, bayan some minutes ya dawo dakin da cup din shayi ya mika mata yace "I diluted it, babu zafi" Amsa tayi ta fara sha, ya dauko mata magungunan yana bude mata, tana gama shan shayin ta amshi maganin ta sha, yace "Zan je masallaci in dawo, kiyi alwala kema kiyi sallah" Ta gyada masa kai ya mike ya fita daga dakin.... Ko da Musharraf ya dawo Mayraah har tayi sallah, ya ajiye mata yoghurt da ya shigo mata da shi ya zauna yana kallonta yace "Are you feeling pain any where?" Ta girgiza masa kai, a hankali tace "But what will be the outcome of my final exams?" Yayi shiru yana kallonta, can a hankali yace "Shouldn't we get married first before thinking of that Mayraah...." Mayraah ta zuba masa manyan idanuwanta, bude side drawer yayi ya ciro wayarsa ya kunna yace "Let me make a call, if possible in ga ko za mu iya zuwa Abuja gobe..." Ita dai kallonsa kawai take, yana kunna wayan bayan ya gama booting kira ya shigo wayar, ya daga kai ya kalleta ganin me kiransa, hade rai tayi ganin Dr Maheer a gaban screen din......
Chapter 74 · 0% Book details