Sashe 129
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read
maki, kuma wallahi kullum sai Maheer yaje wajenta sau biyar a rana, ashe wannan fitan daren da yake wajenta ma yake zuwa ke kina nan kin saki baki sai karfe goma ya dawo mana nan" Haseenah ta dinga kallon Badiyyah with straight face, kamar wasa yau Badiyyah ta tashi da cewar sai Haseenah ta bata kudin gold, da yake Haseenah ta san ta kan dubara tuni ta san yanda ta shashantar da zancen ta shigo da zancen Mayraah shine har da debo ma Badiyyah dankali da kwai da hado mata shayi, shine Badiyyah take bata labarin tasan inda Mayraan ma take yanxu haka, Haseenah tace "Kuma su Ammi sun sani???" Badiyyah tace "Nima fa jiya nayi binciken na gano, har yanzu ban gaya masu ba, so nake sai naje gidan anjima, to ai yau ma Ammin zata koma gida" Haseenah ta zaro ido tace "Da gaske don Allah?" Badiyyah tace "Wallahi, ai shi yasa kika ga Maheer ya fita can gidan Hajja zai je ya dauketa ya maida ta gida" Haseenah ta fara sosa kai tana kalle kalle, can ta kalli Badiyyah da ta cika dankali da kwai a baki tace "To dai gaskiya zan je gidan in taya ta kwalema tun da kinga ko ina dole zai yi ƙura yanzu" Badiyyah ta kalleta da sauri sai kuma tayi dariya tace "Ji neman kugun zama da sabon salo, ance maki babu me aiki ne a gidan??" Mikewa Haseenah tayi ta wuce dakinta da sauri sai ga ta ta fito sanye da doguwar riga da Hijab hannunta rike da handbag dinta, Badiyyah ta saki baki tace "Ina za ki?" Haseenah tace "Gaskiya can zan je in taya su aiki, ko ba komai ai Ammi kamar mahaifiyata take, kuma zata ji dadi idan taga na rigasu ma zuwa gidan na fara mata gyare gyare...." Badiyyah tace "Tabdi, to kin gaya ma Maheer din ne?" Haseenah tace "Ba sai ma gaya masa ba, ai Mahaifiyarsa zan je in kyautata ma" Badiyyah tace "Toh bari in sa kaya mu je tunda bani da inda zan je yau" Haseenah tace "To don Allah kiyi sauri" a haka Badiyyah ta mike ta tafi dakinta ta shirya ta yafa gyale ta fito suka kama hanyar gidan a cikin adaidaita sahu, Haseenah sai fatan ta riga su Ammi zuwa gidan take......