← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 287 OF 313

Sashe 287

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

da ni partially har ya kai ta sanar min a little about her self and her sister da irin rayuwar da suke tun bayan rasuwan iyayensu, har cikin raina naji ina son zan auri Maryam duk da karancin shekaru na don komai nayi offering dinta as gift bata amsa kuma bana jin dadin haka" Bude baki Ceo tayi tana kallon Aaria babu ko kiftawa, Abdallah ya rufe idonsa ya bude ya ci gaba "Na samu Dad dina na sanar masa ni na samu matar da nake son zan aura a lokacin, shi da Mom dita sun yi mamaki sosai don tun ma kafin su ji wacece suka yi against din auren wai i am still young, Dad dina ya kara da cewa kasar waje yake son tura ni in yi karatu, daga karshe saboda yanda nayi persisting akan ni fa aure nake so, sai suka ce min wace yarinyar nake son aura kuma a ina suke zaune a Adamawa, being an only son sannan nasan babu wani abu da nake so da iyayena basa min sai ban boye masu wacece Aaria ba, dad dina na jin wacece ita yayi min iyaka da ita nan take, duk da nayi kokarin fahimtar da shi ita tana addinin musulunci amma ya ki saurarata, he was so mad at me ban taba ganin bacin ran Dad dina ba irin na ranan, ya dinga min fada wai shi zan kawo ma arna cikin zuri'a, to kaf zuri'anmu ba a taɓa haka ba kuma baza a fara a kan ɗan cikinsa ba, cikin fushi ya koreni daga parlonsa, ina bedroom dina cikin damuwa Mom dita ta shigo ta dinga consoling dina don My dad's No is always No, still dai ban daina zuwa gun Maryam da ta saki jiki da ni ba a lkcn, babu yanda ban yi da Maryam a kan mu je wani gari mu yi auren mu ba amma taki, always reminding me of how her mother suffered because of her father's relatives, sannan karatu yayarta take son tayi, duk wannan abubuwan sun faru ne within few months da na fara haduwa da ita don i had to wait to be sure she didn't conceive after our first encounter tun da har raina ina son aurenta ne, and i repented from my bad ways because i was deeply in love with Maryam wanda a lokacin ni kaina ban san wani irin so nake mata ba, kawai watarana na zo da wani plan don naga iyayena are not even giving me listening ears anymore, after coming up with my plan sai naje gidansu Maryam don in sanar mata, coincidentally ranan yayarta bata je kasuwa ba wai bata jin dadi sun fito tare za su je Chemist, nan ta turke kanwarta ta tambayeta waye ni jin na kira sunanta, Maryam is somebody that is so naive and meek, sannan matsoraciya ce, sai ta boye ma yayarta wanene ni, nan yayar ta nuna bata son ina zuwa wajen kanwarta duk tunaninta ai zance ke kawo ni unguwan, nan dai ta ja min layi da Maryam tace min karatu take son kanwarta tayi, a haka dai na kama hanya na bar anguwan" Ceo dai ta kasa dauke idonta a kan Aaria don sai bayan da Hajiya Amina ta gano tana dauke da ciki bayan sun turketa tace ai wannan mutumin da suka taɓa haduwa sanda za su je Chemist ne, a sannan ne kuma ta gaya masu wanene mutumin tunda kowa yasan babansa a garin, Aaria dai ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, A hankali Abdallah yace "Bayan yan kwanaki ban hakura ba na sake komawa gun Maryam hoping yayarta ta tafi kasuwa, luckily muka hadu da Maryam yayarta bata nan, she was so afraid seeing me ta dinga min magiya in tafi kar in sake dawowa bata son yayarta ta kara ganina, it took me almost an hour to persuade Maryam to follow me, na kuma yi assuring dinta ba dadewa za mu yi ba zan dawo da ita immediately, plan din nawa da nayi niyyar gaya mata wancan ranan kawai na fasa don aiwatarwa kawai nake da niyyar yi, after some minutes ride muka je can wani local government a nan Adamawa not too far away, na kai ta har gun wannan limami da ya riga ya san da zuwan mu, i wasn't bothered with how shock Maryam was bayan ta gano what I was up to, a haka aka daura mana aure da Maryam auren da a washegari aka warwaresa amma kafin a warware auren nan I took advantage of Maryam for the second time on that same day, bayan na koma gida ranan nan banyi bacci ba kawai tunanin yanda zan bar Adamawa tare da Maryam ba tare da ta bani ciwon kai ba nake, first na fara tunanin ko in fara kai ta gun Kanin Dad dina wanda sunansa naci, sannan yana mugun ji da ni, Allah ubangiji ya ji kansa da gafara wato Dad din su Musharraf, plan dai iri iri na dinga yi a raina, ashe duk baza ayi haka ba don a ranan cikin wa enda ke zaune masallacin da aka daura mana aure akwai wanda ya gane ni kuma yasan Dad dina, tun yamma yake unguwanmu tunda waya bai yi yawa ba a lkcn, Mai gadinmu ya sanar masa Dad dina yayi tafiya baya gari, washegari haka mutumin nan ya sake dawowa yana unguwan har Dad dina ya dawo sannan ya sanar masa abinda yaga ya faru a masallaci, Dad dina bai taba mari na ba sai a ranan nan bayan yaje har masallacin tare da ni yayi confirming abinda aka gaya masa, i was thinking daga marin nan shikenan zai hakura Maryam ta ci gaba da zama matata, amma i was mitaken, don immediately nan take ya sa na saketa, shi kuma wannan mutumi da ya kawo masa zancen abinda nayi dubu dari ya basa, i was so heartbroken, hatta Aunty Halima sai da ya nuna mata bacin ransa sosai bayan ya gano duk tare muka yi plan din kuma ya rabata da Maryam na har abada, even goodbye bai bari naje nayi ma Maryam ba bayan ya daukeni muka tafi Abuja, after few weeks ya fitar da ni daga Nigeria zuwa makarantar da ya samar min a UK, bayan 3 years na dawo Nigeria don a sannan ne ya yarje min in dawo hutu, i never knew Maryam conceived after our second meeting, Aunty Halima ce ta sanar min duk abinda ya faru bayan bari na Nigeria 3 years ago da kuma prison da Dad dina ya aika Yayar Maryam har na wata 7, a ranan da na dawo naje gidansu Maryam aka ce min ai sun ma bar garin kwata kwata, i was so sad, ban sake haduwa da Maryam ba ban kuma san inda zan nemota ba, 5 years back kawai sai muka hadu da yayarta a Uk, ina ganinta kuma na gane ta, tun daga sannan nake bibiyarta nake mata magiyar ta hada ni da Maryam sai ta kai karata gun yan sanda daga nan ne na hakura amma kullum da Maryam nake kwana nake tashi a raina, a saboda haka har yau ina nan ban yi aure ba, ko na yunkura zan yi auren sai a samu matsala one way or the other, tun iyayena na min magana har sun hakura suna jiran lokacin da Allah zai kaddara inyi auren idan suna da rabon ganin jikokinsu....."
Chapter 287 · 0% Book details