Sashe 22
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
07087865788
WhatsApp only
[6/1, 2:56 PM] Khaleesat Haiydar💖: 💖💖 *MAYRAAH*💖💖
By _Khaleesat Haiydar_📚✍🏻
7......
Mikewa Musharraf yayi ya fita gate din gidan da sauri yana kallon security man din yace "Daga ina yace maka yake? And me yace maka da ya baka wannan?" Security man din ya karaso wajensa da ladabi yace "Bai gaya min daga inda yake ba ranka shi dade, kawai mika min yayi yace in ba Hajiya" Musharraf bai kuma sauraronsa ba ya nufi motarsa ya shiga ya bar layin, mai gadin ya koma ya zauna.... Bayan kayan cikin lefe har da akwati hudu su Hajiya Halima suka cire wai babu amfanin a tafi da akwatuna goma sha hudu, guda goma ya isa, Ita dai Mami bata sake sakkowa downstairs ba don ma kada zuciyarta ya kasa hakuri ta biyesu, Mama Harira tace "To yanzu kayan nan da aka rage ya za ayi da su, nan din za a bar su?" Hajiya Halima tace "A bar su suyi me a nan Mama, shi me yan uwa mata barkatai a family, tafiya za ayi da shi a ba kowa hakkinsa" Kawayen Mami babu wanda yace masu komai, kowa dai ya zuba masu ido, suka gama abinda za su yi sannan aka kira drivers su shigo su dau akwatunan su saka su a mota... Mami na kallon Aunty Fatima da tace baxata je kai lefen ba tace "Ki yi hakuri ku je Fatima, ai ba don su za ku yi ba, in don ta su ne ai baza a kai kayan ba" Aunty Fatima tace "Wallahi yaya yanzu yawanci maza ne ma ke kai kayan ba mata ba" Mami tace "To sun ce su za su kai ya za mu yi masu, kawai kiyi hakuri ku tafi, kowa yayi da kyau ai don kansa, abinda su ma suna da baya" Aunty Fatima ta sauke ajiyar zuciya bata sake ma yayar tata musu ba ta dau gyalenta da handbag ta fita, su Goma sha uku suka tafi kai kayan a motoci hudu, wanda kusan tara duk dangin Abbansu Musharraf ne, Hajiya Halima da Cousin sis dinta me suna Murja sai kyabe baki suke a mota ganin hanyar da aka nufa, Murja ta rike haɓa tace "Yanzu duk fadin garin kano yaron nan ya rasa inda zai je neman aure sai outskirt din kano, ashe girman kansa duk na banza ne, ai ko na raina ajinsa yanzu" Aunty Halima dake taunar cingam tace "Atoh, ba uwar ce me mara masa baya yake abinda ya ga dama ba, ga su ga yar kauye ai sai mu ga yanda za ayi zaman" Ruma'isa dake gaban mota a zaune tace "Kuma ina me tabbatar maku auren nan bazai je ko ina ba tunda ba class dinsa zai aura ba, shi da yake nuna yana da taste ashe duk na banza, balle ma yanzu fa an daina auren mai kudi da talaka, kowa lane dinsa yake tsayawa, kwarya tabi kwarya, ina me kudi ina talaka a wannan zamanin?" Murja tace "Toh wai ma ina ya hadu da yarinyar nan tukun? Zan so in ganta kuwa" Aunty Halima tace "Har yau nima abinda nake son sani kenan, me ya kai sa kurna har ya ga yarinyar yace yana so" Ruma'isa tace "Can ta matse masa dai, mu dai za mu zuba ido mu ga yanda abun nan zai yiwu" Motar su Aunty Fatima da frnds din Mami biyu ne ke leading sauran motocin zuwa gidansu Mayraah don shi yaje kwaso kayan lefen daga can, bayan tafiyar kusan 40mins suka iso anguwan, Aunty Halima tace "Ikon Allah, nan ne fa anguwan Murja, cabb ko a mafarki ban taɓa tunanin da abinda zai kawo ni area din nan ba" Duk suka yi shiru ana bin ko ina da kallo cike da takaici, har dai suka ga motarsu ta tsaya kamar yanda sauran motocin ma suka tsaya, Hajiya Halima na kallon wani lafiyayyen gidan dake gefensu tace "Wannan kuma wani hau ya fada masa duk girman kano ya rasa inda zai gina tanfatsetsen gidan nan sai a nan.... Ikon Allah" Murja dake kallon gidan ita ma tace "Nima shi na saki baki nake kallo, wannan ai bai yi dubara ba dubi almajirai sun masa cirko cirko a kofar gidan, to yanzu dai ina gidan da za a kai lefen?" Sauka duk suka yi daga motar ganin sauran ma duk sun sauko, Mama Harira dake toshe hanci tace "Wai ina dreban da aka ce yasan gidan ne an bar mu tsaye a walakance duk sai doyi ya bade mu cikinmu ya kumbura daga kawo kayan aure" Dreban ya taho da sauri yana nuna gidan da su Hajiya Halima suka gama magana a kai yace "Nan ne gidan ai Hajiya" Bai rufe baki ba aka bude gate din gidan sai ga wakeken compound gari guda na kallonsu, Hajiya Halima ta kalli Murja sannan ta kalli Rumaisa, ko wannensu na zare ido, Mai gadin gidan yace "Motocin duk za su shigo, bismillahn ku sannunku da zuwa" Duka drivers din suka koma cikin motocin da nufin shiga compound din gidan, Hajiya Halima dai ta koma gefe ta tsaya, sai kuma ta kyabe baki tana gyara yafin gyalenta dake wuya, Aunty Fatima da kawayen Mami sai satan kallon reaction din dangin mahaifin Musharraf suke, bayan motocin sun shiga da kafarsu suka karasa cikin gidan, sister din Ammi da yan uwanta na kusa da nesa da kawayenta sannan ga neighbors ne cike gidan suna jiran isowar family din Musharraf, yanda gidan yake a cike kai kace taron biki aka yi, Tarba irinta girma da karamci aka ma dangin Musharraf a gidansu Mayraah, Hajiya Halima dai na zaune babu yabo babu fallasa tana taunar cingam ga akwatuna an zubesu a tsakiyar parlon, sai bin ko ina take da kallo don kam kana gani kasan Naira ta zauna daram, familyn Mayraah sai duba kayan suke sama sama ana yabawa, Hajiya Hafsah frnd din Mami ta bude jakarta ta ciro set din sarka da dankunne na gold har da zobensa, Aunty Halima da mukarrabanta suka saki baki suna kallon ikon Allah don basu san da shi ba, kuma ba a nuna masu ba, they were shock, Hajiya Hafsah ta ajiye set din gold din saman akwatin jewelries, makotan Ammi suka dinga maa sha Allah ana guda cike da farin ciki, sai cewa suke yarinya tayi goshi, Alhamdulillah, Aunty Fatima ta fiddo 300k a cikin jakarta ta daura kan akwatin zannuwa tace "Wannan kudin dinki ne, duk da an dinka mata duk kayan fitan biki suna cikin akwatin, sannan a duba abinda babu a wannan kayan a sanar mana" Hajiya Halima ta wani maka mata kallo, Mama Harira tayi caraf tace "Ai mu babu abinda bamu zuba a kayan nan ba, sai dai son rai...." Aunty Rumaisa tace "Lallai kam son rai, ina ganin in dai babu wani abu to mu za mu koma don daga GRA muke gaskiya" Aunty Halima ta mike tace "Shine kam, kar dare yayi mana a hanya cikin tsukakken lokon nan, ni sai naji kamar barin kanon ma muka yi gaba daya wannan uban tafiya haka" Babu dai wanda yace masu komai a parlon sai Maman Shafa makociyar Ammi da tace "Ai ko dai, dama idan mutum bai saba fita ba sai yaga nisar zuwa nan din, amma a jirgi ma ai ana tafiyar awa da awanni, loko kuma a haka muke zaune cikin kwanciyar hankali babu karya ba komai" Hajiya Halima ta jefa mata wani kallo ita kuwa bata ma san tana yi ba don yaba kyan wani tsadadden lace dake cikin akwati ta hau yi, Small Chop da snacks iri iri da pepper chicken da aka ajiye ma yan kawo kayan nan wani sai yace na gidan biki ne, ga manyan coolers din abinci iri iri da yaji naman rago, ruwa da lemo kuwa yayi park 150 da aka jera masu waje daya abu dai irin na girma, aka kuma dau 300k aka basu tukuicin kayan da suka kawo, Su Aunty Halima basu taɓa zaton haka ba, kuma kana ganin reaction dinsu kasan hakan bai masu dadi ba ko kadan, kamar ana cunkulinsu suka fita daga parlon drebobin da suka zo tare suka dinga fitar da kayan abincin ana sakawa a motoci, aka rakosu har bakin gate cike da mutuntawa har suka shiga mota suka bar anguwan.... Ruma'isa na kallon Aunty Halima dake gefenta tace "Ikon Allah, ashe dai ba er matsiyata bace" Ko kulata Aunty Halima bata yi ba, Mama Harira tace "Amma duk yanda aka yi ubanta kasungumin ɗan kauye ne wanda yayi aziki sama ta ka, banda haka bazai shigo wannan anguwa haka ya kera gidan nan ba kamar ance masa jeka ka gani" Rumaisa tace "Dama mana, irin yan kauyen nan ne fa da suka fito birni suka yi kudi babu zato babu tsammani, to ko wacece uwarta a cikin matan parlon oho...."