Sashe 280
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*_SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA_*👌🏽👌🏽👌🏽 Ceo ta share sabon hawayen da ya taru idonta tace "Da na daure a sannan duk tsananin rashin lafiyar da nake naje na dauko kanwata da duk abinda ya faru bazai taɓa faruwa ba, i still blame my self for everything till date, the useless man took advantage of my poor sister, he assault her, don sai ya yi dubara ya fara dropping din cousin sis din tasa a gida, i don't even know if they are cousin, sai washegari ya dawo da Aaria gida, she never told me anything that happened, na dai ga gaba daya yanayinta ya canza and her eyes were swollen, na tambayeta menene ke damunta haka, sai tace min ai last paper dinsu ne take ganin kamar bata yi kokari ba, na dai kwantar mata da hankali nace zata yi passing duk papers din, for one week nayi ta rarrashinta don taki walwala tunda nasan ta da saka abu a rai... that wasn't enough for the useless man, haka ya ci gaba da bibiyar kanwata duk bata gaya min ba saboda tsoro don bayan dawowar ta da yan kwanaki na koma kasuwancina, all my wish was for her to write jamb ita ma ta tafi University, few months later na fara ganin some changes tare da ita tana ta rashin lafiya a tsatstsaye, bata iya cin abinci, ban kawo komai a raina ba don har Chemist na kai ta nace Malaria ke damunta muka siya magani, ana haka Classmate dita Hajiya Amina that turned family ta zo bayan sun yi mid semester break, nan fa ta ankarar da ni Aaria is pregnant" Ceo na girgiza kanta hawaye na sauka idonta ta kasa ci gaba har sai bayan wani lokaci ta dake cikin rawan murya tace "Because we were nobody, ba mu da kowa, ba mu da wanda zai tsaya mana... kawai don nayi kokarin kwatar ma er uwata 'yan cinta akan assaulting dinta da aka yi shine mahaifin wannan mugun mutumi ya sa aka kulleni a prison for good 7 months" Kuka Ceo take sosai, cikin karfin hali tace "Da ba don Hajiya Amina ba, kilan da Aaria mutuwa zata yi, don there is nobody to take care of her, bata da kowa ga rashin lafiya na ciki da take yi, bata zuwa ko ina tana one room din da aka bamu a kwance 24/7, duk da wahalan karatu haka kullum Hajiya Amina ke fitowa daga makarantarsu ta je wajen Aaria kai mata abincin da ko iya ci bata yi, sannan sai tayi mata duk abinda ya kamata kafin ta bar gidan, ga magunguna da take siya mata, she was there for her all through the hard time, tayi bakin kokarinta a kanta sosai wanda iyakaci nima abinda zan mata kenan, my sister was depressed.... A haka na fito daga prison bayan 7 months, nayi bakin cikin ganin Hajiya Amina bata sa Aaria ta zubda cikin nan ba, satina hudu da fitowa daga prison Aaria ta haihu, ta haifi ya mace daga ni sai ita a daki wajen karfe sha dayan dare, ko kuka jaririyar bata yi ba bayan ta haifota, nayi dubara na kai mata ruwan zafi bandakinmu dake cikin dakin sannan na zazzage taliyar mu dake cikin kwali na dauki jaririyar da ko goge mata jiki ban yi ba na nannadeta cikin zani na sakata cikin kwalin, na dau leda na rufeta da shi sannan na kulle kwalin na fita da ita cikin daren, nayi tafiyar da tafi ta minti arba'in ina ratsa unguwanni da lungunan talakawa da ban taɓa sanin da su ba a Adamawa, har daga karshe na iso wannan exact spot din kusa da rijiya, na tabbatar babu wanda ke kallona na ajiyeta sannan na juya da sauri na kama hanyar gida, wanda da kyar na iya gane hanyar gida tsabar lungunan anguwannin" Cikin rawan murya ceo ta nuna Mayraah tace "Genetic testing showed ita ce jaririyar nan da na ajiye shekaru ashirin da biyu da suka wuce......" A hankali Ammi ta kara jan Mayraah jikinta hawaye na sauka idonta, Abba was speechless, haka ma su Maheer da duk jikinsu yayi sanyi don duk ba haka suka so jin labarin ba, shi dai MD sunkuyar da kansa kawai yayi wishing it was never like this too, Ceo na goge idonta a hankali tace "Tun da na raba Aaria da jaririyarta ta hadu da post traumatic stress disorder, Hajiya Amina was mad at what i did to the innocent Baby, kuma babu yanda bata yi da ni akan mu koma inda nayi deserting jaririyar ba nace mata nima ban san unguwan ba don tafiya kawai nake cikin duhu bazan gane inda na dinga bi ba, ban taɓa tunanin trauma da kanwata ta shiga will be a forever trauma.... da bazan ma fara rabata da er ta ba, ina ta zaton bayan yan watanni zata dawo dai dai amma abun sai gaba yake, sallah da bata wasa da shi tun shiganta boarding school ta dawo bata yi ma kwata kwata and i was a bit happy with just that because i was against her practicing Islam Hajiya Amina ce ta ce in rabu da ita tayi addinin da take so, ranan farkon da naga tayi sallah bayan ta dawo wani hutu da suka yi i was so angry at her for trying to practice islam ashe makarantar ma a musulma suka san ta she was bearing Maryam Ibrahim that was our fathers name, duk da ni da sunanta na Christain nayi registering dinta, sai nake ga kamar kawaye ne suka ja ra'ayinta na yin addinin musulunci whereas ba haka bane don kanta ta zabi addinin, ta bi religion din mahaifinmu ne don sanda yake da rai she was his favourite, bayan yan watanni nayi jamb na shiga jami'a still with Amina's assistant, all this while kuma muna zaune gidan bawan Allahn nan Alhaji Ayuba, gradually kanwata ta zama mara cikakken lafiya don in zan fita makaranta ma kulleta nake a daki in na dawo in bude" Ceo ta goge idonta cikin sanyin murya tace "Hajiya Amina is the reason i am where i am today, sai dai Allah yayi mata rasuwa yau shekara bakwai kenan kuma bata taɓa haihuwan rayayyu 'ya ya ba, ranan da na fara ganin Mary Ann, kawai gani nayi tana min kama da wannan Hajiya Aminar, amma ni dai nasan Hajiya Amina bata taɓa haihuwa ba ta dai yi adopting yara uku a orphanage kuma duk tayi sponsoring dinsu kamar yanda nima ta min tun ma bata san zata auri me kudi danginsa su sa ta gaba ba, wanda bakin cikinsu ne ma ya kasheta, da farko saboda yanayin da take min da Hajiya Amina yasa naji ta shigar min rai, ina kuma sonta har cikin zuciyata, sau tari sai in shigo asibiti duk don in ganta, i usually have a feeling that i cannot even explain akan Mary Ann, even after i left for UK tana rai na, rana daddaya ne idan muka yi magana da Aliyu bazan tambayesa ita ba, she wasn't suppose to go for that UK conference but saboda kawai ina son ganinta na sa a taho da ita, sannan babu staff da ya taɓa sauka gidana amma ita na sauketa gidana, zamanta gidana na just 2 days din nan ne nayi noticing wasu abubuwan da suka girgiza ni game da ita, first nayi noticing yanda take kwanciya bacci just exactly like my sister Aaria, kafin nan ma i notice how she behaves when sick, don da suka sauka bata jin dadi har cikin dare, and all through the night ina shigowa dubata, in the morning i noticed the way she eats, muna dining din still sai na lura da irin kallon da ta ma Aliyu sak na kanwata, i was tensed and confused at the same time, bayan ta gama cin abincin ta bar dinning area, her walking steps took my attention.... Haka nan dai na kawar da komai a raina na ci gaba da harkokin gabana su kuma suka koma Nigeria tare da Aliyu, sun koma da kwana hudu aka yi poisoning dinta, ban yi tunanin hankalina zai yi irin tashin da yayi ba bayan Aliyu ya kirani ya sanar min abinda ya faru, and immediately nayi communicating da wasu Dr which were my colleagues muka taho Nigeria babu bata lokaci tare da su, bayan ta fara farfadowa ne na debi jininta da gashin kanta just to clear my unnecessary doubt that i my self don't understand, ban ma san menene damuwata game da ita in particular ba, ni dai har cikin raina ban taɓa tunanin ita din yarinyar kanwata ce da nayi deserting ba, amma na kasa samun sukuni a kanta, na rasa inda matsalar take, result din DNA test da na bada ayi na fitowa kuma i got the shock of my life, still na sake kawo Aliyu gidan nan ya debi jinin kanwata da kansa muka koma hospital ya debi na Mary Ann, and behold the result was still the same....." Shiru Ceo tayi tana share idonta tana kallonsu, su Abba dai kallonta kawai suke su ma, kuma babu wanda ya iya cewa komai, Maheer dai sai kallon Mayraah da ta rufe fuskarta jikin Ammi yake, he was soo heartbroken, he wish ba da ita aka zo gidan ba, Bayan some minutes Ceo ta mike da kyar tace "Aaria is upstairs, za ku iya bi na yanzu mu je wajenta, wani lokacin tana magana sama sama, though ni kadai ma take yi ma maganar, wani lokacin kuma sai dai ta bi ka da ido kawai, babu kasar da ban fita da ita ba don nema mata lafiya but all my effort prove abortive, babu wani improvement, kuma a haka yanda take har sallah tana yi, masu kula da ita da na dauka ma duk musulmai ne...." Abba ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya ya mike, sauran ma duk suka mike tsaye, Ammi ta dago Mayraah a hankali tana kallonta, hawaye ta gani kwance fuskarta, Ammi ta goge mata hawayen murya can kasa tace "Kar ki sake kuka daughter" Mayraah ta gyada mata kai, duk kallonsu ake a parlon, Ammi ta dagota suka mike, Ceo na gaba suka bi ta har sama zuwa