Sashe 147
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Maheer ya mike ya nufi wani likita da ya fito daga emergency ward kafin yace komai likitan yace "Kai ne mijin nata?" Maheer yace "Eh ni ne" likitan yace "To mu je office" Bin bayan likitan Maheer yayi har suka karasa office dinsa, Mama Ladi da Hajja dai suna tsaye sai zazzare ido suke tun zuwan su asibitin kusan awa biyu da rabi kenan, Mama Ladi ta fashe da kuka bayan sun bi likitan dake tafiya tare da Maheer da kallo, ta rike kanta tace "Rabon ayi kawai, dama kuma ance sanin gaibu sai Allah, banda haka ni in nasan abinda zai faru kenan me zai fito da ni daga gidan Mamuda da sassafe ina cikin rufin asiri na? Wallahi ko koshi ban yi ba na fito ashe wannan fitinar ce ke kirana, Yanzu in yarinyar nan ta mutu ai har mu sai an kai kotu mun bada shaidan abinda ya faru, wai don ma Allah ya so ban karasa shiga ciki ba abun ya faru, da ya zan yi da raina yau ni Ladi, to wallahi da kyar in ba rataye Badiyyah za ayi ba in har wani abu ya samu matar nan, ni dai Allah ya so ban shiga parlorn ba" Hajja ta juya da sauri ta kalli Mama Ladi jin abinda tace, a fusace tace "Ke dai mugun alkaba'in ki yawa garesa Ladi, kuma bakin ki ya sari danyen kashi, ita Badiyyar kike ma fatan a rataye saboda shaidan ya shiga tsakaninta da matar Maheer, kawarta ce fa kowa ya sani, da gangan Badiyyah bazata ji mata wannan rauni haka ba, ko ke baki ga yanda matsiyaciyar matar ta shaketa a wuya ba da farko har sai da Allah ya ba Badiyyan sa'an bugata da bango, ni dama tun da naga Maheer ya daina walwala tun bayan auren sa da yarinyar nasan akwai lauje cikin nadi, har muka yi ta kumfan baki ya saketa akan Mayraah ashe matsiyaciya ce bamu sani ba, to ga dai maganganu tiryan tiryan a bakin Badiyyah kuma wllh ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba Badiyyah bazata mata sharri ba, amma dai bari a gama da asibitin nan tukunna mu san ta kwatanci...." Mama Ladi na girgiza kai tace "Aa ba dai Mera ku ka mayar er iska ba mara galihu saboda bata da uwa bata da uban nunawa a duniya, mu je dai zuwa" Hajja ta mata wani kallo tace "Ke da kike wnn maganar kika san yanda muka reni Mayraan har zuwa yau Ladi? Ina ruwanki da Mayraah? To wallahi kar ki gaya min maganar banza kar ranki ya baci" Mama Ladi ta taɓe baki, ta ja bakinta tayi shiru bata sake ce ma Hajja komai ba tana girgiza kafa. Likitan ya zauna yana kallon Maheer yace "Ana bukatar za a mata karin jini, don tayi loosing blood sosai, but Alhamdulillah Allah ya takaita bai yi affecting inda muke tsoro ba at first da aka kawota, but the wound is so deep gaskiya daga gefen kanta ne sai kuma goshinta da shi ma taji ciwo, mun mata stitching anyi dressing din wound din, gefen fuskarta kawai gurjewa tayi , i think that's all, in sha Allahu muna sa ran zata farfado zuwa nan da yan awanni, yanzu kawai jinin za a kara mata, idan jininka da nata yayi dai dai to sai kaje lab yanzu for test a deba, in kuma bai yi ba za ka siya mata a blood bank din mu" Maheer yace "To in sha Allah Dr, Nagode sosai" Tare suka fita office din da likitan, kafin Maheer ya karasa lab din asibitin ya taho gun su Hajja yace "Za ku iya tafiya gida kawai, jikinta da sauki za a mata karin jini ne yanzu" Hajja tace "Inji babu wani mummunan abun da ya samu kan nata?" Maheer yace "Rauni ne kawai ta ji, amma likitan yace da sauki" Mama Ladi ta rike haɓa tace "Waiii, amma Allah ya hore mata jini, yanda fa kasan an yanka saniya Maheer" Maheer bai tanka ta ba ya tafi zuwa laboratory, Mama Ladi ta mike tace "Kin ga tun da ba mutuwa tayi ba Hajja ki tashi mu tafi gida don ni yunwa nake ji yanzu haka daurewa kawai nake amma tun dazu cikina ke kugi..." Hajja tace "Mu dai babban fatanmu yanzu ta samu lafiya sai a san abun yi" Mama Ladi ta gyara yafin gyalenta ta fita daga asibitin Hajja ta bi bayanta... Karfe sha biyu saura Maheer na zaune dakin da aka kwantar da Haseenah da aka nannade kanta da tulin Bandage bayan an aske kusan rabin gashinta, ledan jini ne a hannunta, shi dai kallonta kawai yake maganganun Badiyyah na yawo a kansa, har a lokacin bai kira kowa a cikin yan uwanta ya gaya masu abinda ke faruwa ba, ya dai kira Ammi ya sanar mata Haseenah na asibiti not long ago, A hankali Haseenah ta bude idonta, Maheer dai sai kallonta yake daga inda yake zaune, suna hada ido tana kokarin mikewa da kyar tace "Maheer wallahi duk sharri Badiyyah ta min babu abinda ta fada da yake gaskiya" Maheer ya mike ya dakatar da ita yace "Na sani, you don't need to stress ur self koma ki kwanta" cikin rawan murya tace "Kasan halinta ae ko, wallahi karya kawai take min dama ta saba sharri iri iri, dubi sharrin da ta dinga bin Mayraah da shi, wallahi karya take min Maheer" Maheer ya mayar da ita ta kwanta yace "Duk na sani, do not worry ur self, u need rest" Haseenah tayi shiru tana jin kanta kamar ana buga mata guduma, Maheer yace "Bari in kira likita" Daga haka ya fita daga ward din, yana fita bayan few minutes sai ga wata nurse ta shigo ta karasa har kusa da Haseenah tana mata sannu, cike da karfin hali Haseenah tace "Nurse ji nake kan kamar ba nawa ba, yayi min nauyi nurse, ko dai bandage din da aka sa min ne?" Nurse din tace "Kiyi hakuri, zai maki sauki in sha Allah, sai a hankali zaki ji ya dawo dai dai, ki daina yawan magana kin ji" Haseenah dai sai hawaye take, Nurse din tace "Bari in dauko alluran da za a maki yanzu, mai gidanki ya fita samar maki abinda za ki ci kafin a maki alluran" Haseenah na son gyada mata kai amma ba dama saboda ya mata nauyi kan, cike da karfin hali tace "Ki ɗan ara min wayarki zan yi kira nurse" Nurse din tace "To ba damuwa" A aljihun uniform dinta ta saka hannu ta ciro wayarta ta mika ma Haseenah sannan ta juya zata fita, Haseenah tace "Don Allah ya sunan asibitin nan?" Nurse din ta gaya mata, bayan ta fita Haseenah tayi dialing number kanwar mum dinta Aunty Fauziyya, yana fara ringing Aunty Fauziyya ta daga, Haseenah ta fashe da kuka da kyar tace "Aunty ina asibiti" Aunty Fauziyya tace "Asibiti kuma? Subhanallahi, me ya sameki Haseenah? Wani asibitin kuma?" Nan Haseenah ta koro mata duk abinda ya faru tana kuka da kyar sbda azaban ciwon kai, Aunty Fauziyya ta mike tsaye daga zaunen da take tace "Kan bala'i, ita Badiyyar ce ta fasa maki kai? Kuma matsiyaciyin mijin naki ya kasa bugowa ya sanar mana abinda ke faruwa, wato ta fasa ma banza kai kenan? Wani asibitin kike yanzu?" Haseenah na gaya mata asibitin Aunty Fauziyya ta katse wayar, Haseenah tayi dialing number Aunty Farida ita ma sis din Mum dinta ce amma ta ji tana on another call, Cousin sis dinta Salma ta kira ita ma tana dagawa ta gaya mata abinda ya faru da asibitin da take, bayan ta gama sanar ma Salma sai ga kiran Aunty Farida ya shigo, Haseenah ta daga da sauri cikin kuka zata fara mata bayani cikin daga murya Aunty Farida tace "Fauziyya ta kirani ai ta gaya min komai, ga mu nan zuwa asibitin yanzun nan za mu ga uban da ya tsaya ma Badiyyah har ta maki haka" Daga haka Aunty Farida ta katse wayar. Ammi ta fito daga bangarenta bayan Maheer ya kirata ya sanar mata abinda ya faru, har zata sauka downstairs ta tsaya for few seconds, Mama Ladi dama ta gaya mata a dakin Maheer Mayraah take yanzu, kawai ta buda kofar dakin taga babu kowa ciki, hakan yasa ta sauka ta fita zuwa asibitin da Maheer yace mata aka kwantar da Haseenah, Ammi na isa asibitin ta kira Maheer ya fito ya shigo da ita ward din da Haseenah take, ko da wasa bai yarda sun hada ido da Ammi ba, ita dai Ammi na tsaye kan Haseenah dake ta juye juye tana wayyo Allah don Anaesthesia ya fara sakinta, gaba daya Ammi ta ma rasa me zata ce jikinta duk yayi sanyi ganin ashe ciwon ba na wasa bane ganin yanda aka nannade kan Haseenah da bandage wanda har ya fara staining sosai da jini, Bude kofar ward din aka yi sai ga Aunty Farida da Fauziyya da Aunty Murja warce cousin dinsu ce, sai kawar Aunty Farida sun shigo babu ko sallama fuska a murtuke basu ko bi ta kan Ammi da Maheer ba suka nufu gun Haseenah kamar wasu sojoji, Aunty Farida na huci tace "Kan bala'i, ita Badiyyar ce ta maki wanna aika aikan? Ita Badiyyar? To wallahi wallahi sai mun yi shari'a da ita, sai naga uban da zai tsaya mata a kano" cikin bacin rai Aunty Fauziyya tace "Wato ba don ke kin kira mu ba so suka yi sai kin mutu su kira mu su sanar mana mu xo mu dauki gawarki ko? Saboda 'yar su ce shine suke neman rufe abun ko? to wallahi sai mun ga uban da ya tsaya mata a kaf garin kano, mu je Farida, wallahi ko guduwa tayi ta bar kano sai mun sa an daure uwarta tayi mana providing dinta, ai ba kowa ake taɓawa a kwana lafiya ba" Aunty Murja ta kankance ido tace "Wallahi kasheta kawai tayi niyyar yi ko ince suka yi niyyar yi, uban me ta masu haka? wani irin family Haseenah ta fada haka?? Duka duka yau wata nawa da auren aka mata haka?" Ammi ta kasa cewa komai ta saki baki tana kallonsu da mugun mamaki, Shi kansa Maheer na tsaye jikin