← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 169 OF 313

Sashe 169

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

bata wayar ki kara daga mata hankali tunda in ta mutu ni nayi asara ba ke ba, ki bar mata taji da ɓacewar er ta mana Hajja, duk ke da Badiyyah fa ku ka dinga juya matar nan har ta kora er ta kwaya daya ta shiga duniya saboda son zuciya irin taku, gashi kun ja mata kishiya me diri har Mamuda ya dauke kishiyar sun koma dankareren sabon gidansa da ya gina ya bar ita Ammin a walakance a nan cikin yaku bayi Mashir ke gaya min jiya da daddare, wa ya ja mata banda ke da jikarki da tsinanniyar surkarta, Wallahi ban taɓa ganin uwar da bata son kwanciyar hankalin 'ya yanta ba irin ki Hajja, ko ni da ɓan taɓa haihuwa ba bazan yi wannan abinda kike yi ba Hajja, kuma in baki yi hankali da yarinyar nan Badiyyah ba wallahi zata sa a rataye ki muyi ta koke koke muna nema maki rahama wajen Allah" Hajja da ranta yayi mugun baci tace "Ladi ni kike gaya ma wa ennan maganganun? Ni Ladi?" Mama Ladi tace "Toh me na ce? Ni dai Allah ya gani ba rashin kunya na maki ba gaskiya nake gaya maki, haka kawai in ki gaya maki Allah ya kama ni, aa ba ruwana wallahi" Hajja tace "Ba komai, Nagode Ladi, ni dai kike ci ma mutunci haka ko? Ita Ammin ta sa ki gaggaya min wannan maganganun ko?" Mama Ladi tace "Wacece Ammi? Ammi da yanzu haka gata can Mashir ya sa mata ruwan drif, ni dai ba ruwana sai anjima ba rashin kunya na maki ba gaskiya ce dama ance daci gareta" Daga haka ta karasa gun Ammi da sauri tana mata alamar ta katse, Ammi ta katse wayar tana kallon Mama Ladi babu ko kiftawa don kalmar da tayi wai Mamuda ya dauke kishiya sun koma dankareren sabon gidansa ne kawai ke ta yawo kan Ammi, can a hankali Ammi tace "Sabon gida ya koma da matar?" Mama Ladi dake share zufar goshinta tace "Wa?" Ammi ta kasa cewa komai, Can Mama Ladi ta tuna maganganunta a waya, da sauri tace "Haba duk shirgata nake ko zata dawo hankalinta fa, ba nan Mamudan ya kwana jiya ba? Kawai na gaya mata haka ne don in gigitata ta shiga taitayinta ta kyaleki kiyi zaman aurenki lafiya, amma wannan Amarya ai ina jin tana gidansu yanzu haka tun da gashi daga zuwanta komai ya kara tabarbarewa, ai shi Mamudan ba wawa bane" Ammi dai bata sake cewa komai ba, Mama Ladi ta dau tsintsiyar ta ci gaba da sharan tace "Dama baki yi niyyar yi ba, tafi ki zauna kawai ni da kika mayar boyi boyi saboda daga kauye nake sai in ta yi ai tunda za a ban in ci in koshi" Ammi ta koma ta zauna amma zuciyarta ya kasa kwanciya da maganar sabon gidan da Mama Ladi tayi. Mayraah na zaune parlon Maman Hanan da yamma don ranan aka yi sadakan uku, zuwa sannan ma duk mutane sun watse sai yan uwanta, Sosai mutuwar yarinyar ya girgiza uwar gashi tun ita bata sake haihuwa ba shekarar yarinyar takwas, Mayraah ta kalli wayarta da yayi vibrate taga number Dr Khalil da ta kira dazu da safe ne da bai daga ba sai yanzu ya biyota, tayi silencing wayar tana kallon Maman Hanan tace "Aunty bari in shiga gida, sai gobe idan na shigo in sha Allah, sai ki basu takardan da na rubuta maki maganin a siyo maki ki sha zaki samu bacci in sha Allah" a hankali Maman Hanan tace "To Nagode Ilham, baki debi abincin ba kuma" Mayraah ta ɗan yi murmushi tace "Na koshi wallahi, nima wanda na dafa ban cinye ba" Maman Hanan tace "Toh shikenan sai kin shigo goben" Mikewa Mayraah tayi suka yi sallama da mutanen parlon sannan ta fita ta koma gida, bayan ta kulle gate din ta shiga daki ta yi dialing number Dr Khalil, sai da ya kusa katsewa ya daga tayi sallama ya amsa sannan ta gaishesa, yace "Wa ke magana?" Tace "Ilham ce" Yace "Oh, Ilham sorry u called tun dazu, ina busy ne wllh" Tace "Ba damuwa, ya aiki?" Yace "Alhamdulillah, gobe ki shigo asibitin da safe kawai" A hankali tace "Toh" Yace "Yeah, in kin shigo sai ki kirani" Tace "To Allah ya kai mu Nagode" Sallama suka yi ya katse wayar, haka kawai taji gabanta na faduwa, ta zauna gefen katifa tana tunanin yanda zata fara aiki a babban asibitin nan cikin manyan health workers da suka yi shekara da shekaru a aikin, za ma ta iya kuwa? Anya ma zata iya tuna abubuwa yanzu don gani take kamar kanta baya ja, haka nan ta kwana cikin zulumi da tunani iri iri a ranta, gari na wayewa bayan ta shirya cikin doguwar riga ta saka hijab dinta har kasa da tayi iron, shayi kawai ta iya sha don duk a tsorace take, bayan ta gama ta dau nose mask dinta ta saka sannan ta dauki handbag dinta ta fita ta kulle gidan, sai da ta fara lekawa gidan Maman Hanan ta gaisheta ta tambayeta ko ta samu bacci, Maman Hanan tace "Ai kam na samu bacci sosai Ilham, Nagode fita za ki yi ne?" Mayraah tace "Eh zan tafi makaranta" Maman Hanan tace "Toh Allah ya tsare sai kin dawo" Daga haka Mayraah ta fita ta kama hanyar cikin garin Abuja, tana isa asibitin wajen karfe goma saura bugun zuciyarta ya tsananta ita kanta ta rasa me yasa ta zama so tensed haka, sau biyu ta kira Dr Khalil bai daga ba, ta zauna reception bayan ta gaida wasu nurses da ta gani, wata nurse na tambayarta ko tana da appointment da Dr ne, Mayraah ta girgiza kai zata yi magana sai ga Dr Khalil ya shigo Reception din, yana ganin Mayraah yace "Meet me at my office" Daga haka ya wuce sama ta mike ta bi bayansa zuwa office din nasa, bayan ta shigo ta gaishesa ya amsa yace "Zauna mana" Zaunawa tayi kan kujera tana kallonsa, wani leda ya dauko ya ajiye mata kan table yace "Ur Scrubs and shoes, Allah ya sa su maki" Mayraah ta dau ledan, Dr Khalil yace "Ya kamar kina tsoron ledan" Ɗan murmushi tayi tace "Aa" Yace "Zaki fara aikin yau ai?" Mayraah ta rasa abinda zata ce, ya nuna mata wani kofa a office dinsa yace "Ki shiga nan ki gwada scrubs din ko za su maki da shoes din" Ta gyada masa kai sannan ta mike tana rike da ledan ta nufi kofar da ya nuna mata ta bude ta shiga, bayan few minutes ta fito sanye da hijab dinta tana kallonsa tace "Sun yi" Yace "To me yasa baki bari a jikin ki ba kika cire, u are resuming work today" Mayraah dai kawai tayi murmushi ta koma ta zauna tana kallon sa, kwankwasa office din aka yi yayi izinin shigowa wata nurse ce ta shigo warce bazata haura 30 years ba ta gaishesa da ladabi, yace "Morning Hafsat, ga sabon staff dinmu zan damka maki ita yanzu, ki dinga guiding dinta pls, for now she is not working amma komai za ki yi you make sure tana kusa da ke tana gani" Nurse Hafsat ta karaso tana murmushi tace "To ba damuwa sir, in sha Allah i will do so" Yace "Transferring dinta aka yi zuwa nan ko da wani ya tambayeki...." Hafsat tace "In sha Allah sir" Dr Khalil ya kalli Mayraah yace "Nurse Ilham, follow your colleague zata nuna maki inda zaki saka scrub din ki" a hankali Mayraah tace "To Nagode" Daga haka ta mike tana rike da ledan ta bi bayan Nurse Hafsat suka fita, suna sauka reception din few nurses dake wajen suka bi su da kallo, Nurse Hafsat ta kai Mayraah changing room tace "You are welcome to be part of Us in this great hospital Nurse Ilham" Mayraah tana murmushi tace "Thank you" Mayraah na gama saka scrub din ta fito daga bandaki Hafsat tace "Waow kin ga yanda ya maki kyau kuwa kamar sai da aka auna ki kafin a dinka" Mayraah dai ta kirkiri murmushi, Nurse Hafsat tace "You look smart on this scrub" Mayraah was a bit comfortable cikin uniform din saboda me Hijab ne duk da karamin hijab ne, unlike yanda taga wasu nurses babu hijab sai scrub cap amma tana tunanin ba musulmai bane don Hafsat ma nata uniform din da karamin Hijab a kai, Hafsat tace "Wani makarantar kika yi?" A hankali Mayraah ta gaya mata school din da ta gama, Hafsat ta wara ido tace "Da gaske? Wani department?" Mayraah ta gaya mata, Hafsat tace "Lahhh, nima shi nayi ai, mun gama kusan 8 years kenan" Mayraah da bata son zancen tayi saurin cewa "Ayya, ina zan bar jakana yanzu?" Wata nurse ce ta shigo wajen ta kalli Hafsat sannan ta kalli Mayraah, can ta maida dubanta kan Hafsat tace "There is an emergency" Daga haka ta juya ta fita, Hafsat ta amshi jakan Mayraah da sauri ta bude wani safe ta saka ciki da ledan second scrub da takalmin Mayraah sannan ta kulle safe din ta ja Mayraah suka fita daga room din da sauri.
Chapter 169 · 0% Book details