Sashe 271
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*_SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA_*👌🏽👌🏽👌🏽 Ammi ta ajiye abincin da ta kawo ma Mayraah har bedroom dinta da farfesun hanta tana kallonta tace "Ko zaki sha shayi?" Mayraah ta girgiza kai tace "A'a abincin ya isa Ammi" Ammi ta nufi kofa, Mayraah dai ta bi ta da kallo har ta fita ta kullo mata kofar, a hankali ta rufe abincin ta matsar gefe daya sannan ta mike ta dau hularta ta saka ta nufi kofar dakin ta bude a hankali tana leka corridor, sai da ta daina hango Ammi sannan ta fito ta kulle kofar dakinta ta sauka downstairs, dakin Maheer ta tafi ta kwankwasa kofar gently sannan ta murda handle din ta bude kofar, a tare suka juya shi da Usman suna kallon kofar, ta ɗan wara ido ta karasa ciki da sauri tana kallon Maheer da damuwa ta durkusa gabansa tace "Yaya baka san na dawo ba ne?" Sai kuma ta kalli Cannula din hannunsa kafin tace komai yace "Yanzu drip din ya kare zan yi sallah sai in je inyi welcoming dinki Mimi" Ta mike tana kallonsa cike da damuwa tace "Me ya sameka yaya? Since when were u sick?" a hankali yace "Naji sauki ai, Alhamdulillah" Ta kai hannu forehead dinsa gently taji temperature dinsa is normal, cikin sanyin murya tace "Allah ya sauwake yaya" Ya sauke idonsa yace "Ameen Mimi, ya naki jikin?" Tace "Ai naji sauki tuntuni" Ta kalli abincin dake kasa cikin warmer, ta durkusa ta bude tace "In zuba maka abincin?" Yace "Lokacin sallah yayi ai, sallah zan yi first" Zaunawa tayi saman carpet din tace "Ohk i will wait, idan kayi sai in zuba maka" Murmushi yayi yace "Ke baza kiyi sallan bane?" Sai a sannan ta daga kai ta kalli Usman dake kallonsu, sai taki cewa komai kawai ta sunkuyar da kanta ta tallabi chin dinta tana murmushi, shi dai Usman wayarsa kawai yake dannawa, Mikewa tayi tace "Idan an idar da sallah zan dawo Yaya" Yace "Ohk" Usman ya dau wayar Aunty Mariya ya mika mata yace "Ki kai ma Aunty wayarta" Amsan wayar tayi sannan ta fita daga dakin, Usman na kallon Maheer yace "Za ka iya zuwa masallacin ne?" Maheer yace "Let's pray here" Mayraah na komawa daki ta debi abincin da Ammi ta kawo mata dakin, a hankali take cin abincin, lkci daya jikinta yayi sanyi bayan ta tuna incident din da ya sa tayi kusan sati uku a asibiti, duk son ta da abincin sai ta kasa cin da yawa don nan da nan ya fita ranta, daga karshe ta rufe kawai ta mike a hankali ta koma saman gado ta kwanta incident din na dawo mata a kai vividly, bayan minti ashirin taji an bude kofar dakin, juyawa tayi da sauri taga Usman tsaye bakin kofar dakin ta mike zaune kafin tace komai yace "Ya idar da sallahn, ki je ki zuba masa abincin" Ta sauko daga saman gadon tace "Toh" Sai kuma da sauri tace "Yaya kai ka ci abincin?" Yace "Sai anjima" Daga haka ya bar bakin kofar ta fita zuwa dakin Maheer, yana zaune saman darduma ta samesa da counter a hannunsa, ta kulle kofa ta karaso ta durkusa kusa da shi tace "Ka gama yaya?" Yace "Na gama" kallonsa ta dinga yi ganin yanda ya rame, da damuwa tace "Yaya for how long were u sick?" Da fingers dinsa ya nuna mata alamar 2 days, bata sake cewa komai ba ta bude warmer din, same food ne da wanda ta ci dazu a dakinta, ta debar masa ta sa cokali sannan ta koma gefe ta zauna tana kallonsa, sauke idonsa yayi ya dau spoon din ya fara cin abincin a hankali, bayan few minutes yayi breaking silence din dakin yace "I heard MD yayan Musharraf ne ko...." Mayraah ta wara ido tace "Yaya i was very very shock, it was the least thing I expected yaya.... Kuma fa basa kama, kawai dai suna da same thick eye brow with fingers, apart from that i see no resemblance, or may be their noses look alike also, sannan yanayin halinsu ma iri daya wallahi, at times fa idan MD din yayi wani abu sai Musharraf ya fado min, attitude dinsu is almost same, just that Musharraf baya ba irrelevant issues relevant kamar MD, ashe shi MD da Maminsu yake kama, yaya that very day kawai sai nake ganin abun kamar a mafarki wallahi, what a coincidence...." Murmushi kawai Maheer yake yana cin abincin gabansa yana sauraronta, don kanta tayi shiru, ya daga kai ya kalleta yace "Kamar dama kina jiran wannan tambayar ki fara amayar da abinda ke ranki?" Mayraah tayi er dariya tace "Wallahi na rasa da wanda zanyi labarin, i was so shock and confused at the same time, sai nayi regretting abubuwan da na dinga masa a asibitin" a hankali ta karasa maganar, Maheer na kallonta yace "Wasu abubuwa kika dinga yi masa?" Mayraah ta ɗan langwabar da kai tace "Ko da yake shine ai ya janyo duk abinda nayi masa" Maheer yace "Gaya min abinda kika masa" Zata yi magana aka bude kofar dakin, duk suka daga kai, Ammi ce tsaye bakin kofar dakin, mamakin abincin da Maheer yake ci tayi, don for the pass 5 days sai dai ya sha tea kadan ko kuma ya sha fruits amma ba dai abinci ba, ko da ta tilasta sa ya ci abincin to cokali biyu zai yi da kyar, yanzu kuma taga ya ci da ɗan yawa, Mayraah zata mike Ammi tace "Yi zaman ki, ke kin ci abincin ne?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Na ci" Rufe kofar Ammi tayi ta bar wajen, Maheer ya kalli wayarsa dake vibrate ya dauka yana kallon screen din, can ya kalli Mayraah yace "Shi yake kirana" Mayraah ta buda ido sosai tace "MD din?" Maheer ya gyada mata kai sannan yayi picking call din ya kai kunne tare da sallama, gaisawa suka yi sannan Maheer yayi shiru yana sauraron sa, can yace "Ohk zuwa yaushe kenan?" Daga karshe dai Maheer yace "Alright, ba damuwa" Katse wayar yayi, Mayraah dai sai kallonsa take eagerly taji abinda MD yace masa, bayan ya ajiye wayar da sauri tace "Yaya me yace maka?" Maheer ya ja hancinta yace "Cewa yayi akwai sauran drip uku da za a saka maki a asibitin da kuma allurai 5, wai a maido ki yanzu" Mayraah bata san sanda ta hade rai ba tace "Aa ko ba drip ba, sai dai ya sa ma kansa, ni dai kowa yasan na warke" Dariya Maheer yayi, tana ganin haka ta marairaice tace "Pls be serious mana yaya, nasan ba haka yace maka ba, don Allah ka gaya min me yace maka?" Maheer ya ajiye spoon din hannunsa a hankali yace "Cewa yayi zai zo gida mu hadu, he wants to discuss an issue with me" Mayraah dai tayi shiru tana kallonsa a ranta kuwa sai nanata issue din take, bude kofa aka yi duk suka juya, Usman ya shigo ya ajiye ma Mayraah leda a kusa da ita yace "Wash the fruits for him" Ta bude ledan tana lekan ciki sai kuma ta kallesa tace "Yaya ni fa?" Yace "Au zaki sha ko?" Ta wani turo baki tana kallonsa, yayi murmushi yace "It's for the both of you" Ta washe baki tace "Toh mun gode yaya" Tare suka fita dakin da shi, ita ta wuce kitchen zata wanko fruits din shi kuma ya haura sama. Bayan isha Maheer ya fito parlor bayan MD ya kirasa ya sanar masa yana waje, Ammi na zaune parlor tare da mai aikinta, Ammi ta bi sa da kallo tace "Ina kuma zaka?" Ya dawo yana kallonta yace "Dr Aliyu ne ya kirani, yace za mu yi discussing wani issue, so yana kofar gida" Da wani expression Ammi tace "Waye kuma Dr Aliyu?" Maheer yace "MD...." Da mamaki Ammi tace "MD kuma? Discussion akan me kenan?" A hankali Maheer yace "Shine zan fita in ji, bayan magrib ya kirani zai zo, so he is around now" Ammi da taji hankalinta ya tashi ta mike, kafin tace komai Maheer yayi saurin cewa "Look Ammi, ni nafi tunanin discussion ne akan abinda ya shafi lafiyar Mayraah ba wai wani abu bane...." Shi kansa bai san sanda ya fada mata haka ba ko hankalinta zai kwanta, bai san furucin nasa kara daga mata hankali yayi ba, cike da damuwa tace "Na shiga uku, kar dai sun ga wani abu ne Maheer, dama wannan farin likitan na ta exaggerating akan liver, wai ko poison din ya taɓa nan..." Maheer ya ɗan yi murmushin karfin hali yace "Ni nasan ba haka bane kar ki wani daga hankalinki, zan je in ji koma menene in dawo yanzu" Daga haka ya fita daga parlon, Bilkisu na kallon Ammi tace "Ki kwantar da hankalinki Ammi in sha Allahu babu komai" Ammi dai bata ce komai ba ta koma ta zauna zuciyarta na bugawa. Maheer was confuse, ya dai kafe ido kan result din DNA test da MD ya basa a cikin motarsa, bayan wasu yan dakikai ya kalli MD yace "I am confuse na meye wannan din, naga sunan Mayraah, and dayan babu suna, ban fahimci komai ba, meye ma'anar hakan?" MD yace "I am also confuse just like you, CEO dinmu ce zata warware mana komai... All i know is that 8-9 days back ta kai ni gidanta da daddare ta sa na dau sample din jinin wata mata, muka dawo asibiti tasa na debi jinin Mayraah, ta kuma umarce ayi Genetic testing, dazu result din ya fito and this is what i am seeing" Kallonsa Maheer yake babu ko kiftawa, MD kamar yasan abinda ke ran Maheer yace "Look da ace bani na dau sample din jinin ba nima it won't make any sense to me, but i am telling u ni na dau jinin nasu da hannuna...." Maheer da kansa ya gama kullewa yace "Then what does this mean? It's showing postive, who is the woman?" MD yace "Shi yasa nace maka Ceo ce zata warware koma menene don matar na gidanta, and from the look of things she is not mentally stable" Maheer ya sake kallon results din hannunsa da mamaki, he was totally speechless, MD yace "Naga