← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 302 OF 313

Sashe 302

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mayraah na bude kofar dakin taga mai aikin Ceo a tsaye, da ladabi matar tace "Hajiya dama MD ne yace za a amso wayarsa a wajen ki" Mayraah ta sauke idonta ta juya ta koma dakin ta dauko wayar ta dawo ta ba matar sannan ta kulle kofar ta koma tana tafiya a hankali ta kwanta gefen gado maganganun Musharraf na ci gaba da yi mata zarya a kai, ɗan murmushin takaici tayi tana goge hawayen da ya gangaro mata fuska. MD na zaune compound din gidan Ceo bayan ya raka Dr Khalil ya tafi, Number Musharraf yayi dialing a wayarsa don tun da worker din Ceo ta kawo masa wayar bai samu kiransa ba sai yanzu da ya dawo daga rakiyar Khalil, yana fara ringing Musharraf ya daga, Calmly MD yace "How r you doing?" Musharraf yace "Alhmdlh, good afternoon" MD yace "You know what i want to tell you...." Musharraf ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "Ina ji" MD yace "Ina son a yanzu ka ajiye wani batun ka hakura da kake cewa, let wait and see what they are up to on Thursday" Musharraf yace "Me yasa ku ke son in ci gaba da deceiving kaina ne ina kara sa ma kaina damuwa pls?" MD yace "Matsalata da kai kenan baka jin magana, when is this Thursday? Why not be patient till then, or is it too far?" Musharraf ya dakatar da shi yace "Look Bro, my heart is tired, with reckless abandon my emotions have been tampered with, and i pray this is just the best for me, on that very Thursday kamar yanda nace maku bazan je ba because it's not going to favor me" MD yace "Kamar son nata a bakin ka kawai ya tsaya fa, in ko ba haka ba bai kamata kayi give up just like that ba, come to think of it, shekaru nawa ka ɓata a kanta? kai a soyayyan ma matsoraci ne" Musharraf yace "I pray u won't get carried away in love just like it happened to me, i pray u don't fall victim, it's not funny" Tun daga nisa MD ke kallon Ceo that is coming toward him, hakan yasa ya katse wayar kawai ya ajiye saman table din gabansa, ta karaso ta ja kujera ta zauna tana kallonsa speaking calmly tace "Aliyu i am not accepting you resignation letter! Kana ganin ko don abinda kawunka ya min baka yi deserving aiki a karkashina ba ne kuma? Paternal Relatives dinka ne suka yi min ai ba kai ba" Kallonta ya dinga yi, can ya girgiza kai yace "Not at all Ma'am, ba haka bane wallahi, kawai dai ina son..." Ceo ta dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu tace "You will work with me har zuwa sanda zaka mallaki naka hospital din Aliyu, it's something da ni da kaina zan maka planning dinsa, ba wai zaka yi ta zama ka dawwama a karkashina bane, Sannan have you pondered over what i told u about Mary Ann yesterday?" MD ya daga kai yana kallonta, can ya ɗan yi murmushi yace "Ma, i am sorry but bazan iya cewa zan auri Ex din brotherna ba ko da da gasken har cikin ransa ya hakura da ita, it's something that will never be possible, instead kamata yayi i should go to any extent na ganin ya mallaki heart desire dinsa, tun jiyan ina ta nazari da tunanin how I will arrive at that, at the end na fahimci abu daya kawai zan yi amma kuma ban san outcome din da hakan zai haifar ba, shi yasa still nake contemplating, but i will love to see my brother marry his love" Ceo tayi shiru while looking at him alamar ba haka ta so ba, a hankali tace "But da bakinsa yace ya hakura ai ko?" MD yace "He is frustrated Ma'am, amma nasan yana sonta har yanzu kawai ya rasa yanda zai yi ne, it's now left for her and her parent to do him justice" Ceo tace "To kudin aurensa da kace za a kai fa?" Yace "Ma'am that is a decision between our mother and him, uncle dinmu ai shi yanzu jiran feedback din iyayen nata yake idan sun zo ranan alhamis" Ceo na gyada kai a hankali duk da ita fa ba haka ta so ba, tace "Ohk then, i will speak to her about him, kai kuma zaka iya zuwa Canada ko wata biyu ne kayi since that is what you want, Dr Wale and Dr Ajay suna nan ai, either of them will take ur Seat kafin ka dawo" Shi dai kansa na kasa, can ya dago ya kalleta a hankali yace "Thank you Ma'am" Tace "You are welcome" Daga haka ta mike ta bar wajen ta koma cikin gida. Da daddare Ceo ta shigo dakin Aaria, da mamaki take kallonsu Mayraah na mata kalaba da dogon gashinta wanda yake har kusan bayanta, Aaria da bazaka taɓa convincing dinta ka mata kitso ba wai sai ga Mayraah na mata kitso, Ceo ta karasa tace "Kitso ku ke ta yi kenan" Mayraah na murmushi tace "Mun ma gama ai" Ceo tace "Good, in kin karasa ki zo zan sa ki wani aikin a parlor na" Mayraah tace "To" Daga haka Ceo ta fita, Bayan Mayraah ta gama tana kallon Mahaifiyarta da kyawunta ya kara fitowa tana murmushi tace "You look cute Mom" Murmushi Aaria ma tayi tana kallonta a hankali tace "Thank you my love" Mayraah ta tafi bandaki ta wanke hannunta sannan ta dawo dakin, Aaria dai sai bin ta take da kallo, ta dauko mata magungunanta da ruwan gora ta bata, sannan ta gyara mata shimfidarta, har bayan minti ashirin Mayraah bata bar dakin ba sai da taga uwarta ta fara bacci sannan ta fita zuwa gun Ceo, kujera CEO ta nuna mata, Mayraah ta zauna tana kallonta tana jiran jin aikin da zata sa ta, Ceo tace "Tell me the truth Mary Ann, har yanzu a ranki kina jin zaki iya auren brother din Aliyu that was ur fiance before?" Mayraah ta ɗan yi murmushi ta sunkuyar da kanta cikin sanyin murya tace "Ma'am mun yi waya da shi dazu yace min shi ya riga ya hakura da ni, beside yayansa ai yace mana za a kai kudin aurensa" Tana magana amma bata san har hawaye ya cika idonta ba, Ceo dai sai kallonta take, Mayraah tayi karfin halin cewa "Saboda haka nima na hakura da shi, he told me in my ears we shouldn't deceive our selves anymore, kilan ya riga ya samu wata warce yake son aure tunda gashi har za a kai kudi don haka nima i am not interested any longer, Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi" Ceo ta girgiza kai calmly tace "You are not saying this from ur heart Mary Ann, i can see it, kina sonsa har yanzu" Mayraah ta goge idonta tace "Da gaske nake Ma, ni na hakura da shi wallahi, i am not getting married to him, i assume don yana da wata ne yanzu shi yasa ya gaya min haka, if not ai bai jira ranan da aka ce za su zo ba yaga ko zan yi denying dinsa kawai ya yanke hukunci, since he isn't patient enough to wait for that day it's fine dama yana da wata da ya saka rai zai aura bayan mun rabu, i believe haka ne, Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi gare mu baki daya" Ceo dai kallonta kawai take don bata san haka take da bakin magana ba, bayan few seconds ta sauke ajiyar zuciya tace "Me yasa baza ki masa uxuri ba?" Mayraah tace "He didn't even give me a listening ear Ma, kawai ya riga ya gama deciding and he was eager to cut off the call a lokacin, beside Ma'am yayi blocking dina fa ta wayana, ta wayar brother dinsa na samu muka yi magana, kinga assuming he is still interested bazai yi blocking dina ba" Da mamaki Ceo tace "Blocking dinki kuma?" Mayraah ta gyada mata kai a hankali, Ceo tace "To ki kyalesa, ki rabu da shi kawai, may be kamar yanda kika fada ya samu wata ne if not da sai ya jira yaga ko zaki amince da auren nasa ko baza ki amince ba, just leave him" Mayraah dai ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba wasu sabbin hawayen na taruwa idonta, Ceo tace "I think kamata yayi a bar zancen auren nan haka gaba daya har Allah ya kawo maki wani zuwa wani lokaci, duka duka shekarunki nawa, marriage is not something to rush about, you are still young, probably idan Parent dinki suka ji stand din Brother din Aliyu su ma za su bar zancen auren" Mayraah ta daga kai tana kallonta a ranta kuwa taji dadin wannan maganar da tayi, don ita kanta zata zo a bar zancen auren nan zuwa wani ɗan lokaci zuciyarta ya huta from all this stress of few days ago, she need rest, yanzu kawai jira zata yi taga abinda zai faru idan Uncle din su Musharraf suka zo, Ceo bata sake cewa komai ba nan kuwa ita ma wani tunanin ne daban a ranta, Bayan wani ɗan lokaci Ceo ta sauke ajiyar zuciya tace "Zaki iya tafiya ki kwanta, do not stress u self anymore pls, ki kwantar da hankalinki kin ji?" Mayraah ta gyada mata kai a hankali tace "Thank you Ma'am" Daga haka ta mike ta nufi kofa, Ceo ta bi ta da kallo har ta fita ta kullo mata kofar. Kamar yanda Ceo tace ma Mayraah ta kwantar da hankalinta haka ta kwantar da hankalinta sosai ta cire duk wani damuwa a ranta tana harkokin gabanta, ta maida attention dinta gaba daya kan uwarta tana kula da ita tayi mata girki ta gyara mata daki ta hada mata ruwan wanka, duk wani abu dai da Farida ke ma uwarta duk ta dauke mata ita ke yi, yini take tare da mahaifiyarta a dakinta tana mata hira ko kuma su fito parlon dake sama, ita kanta bata san zata yi saurin sakewa da mahaifiyarta haka ba ta dinga jin ta har ranta don at times sai Ammi ta fado mata zata
Chapter 302 · 0% Book details