← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 313

Sashe 77

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

yayi picking ganin Maheer ne ke kira, ita dai Mayraah idonta na kan titi, Musharraf yace "Yea sai ka wuce traffic light, i parked in front" Yana fadin haka ya Katse wayar ya juya yana kallon Mayraah da taki cewa komai har sannan, ya kamo hannunta yayi kasa da murya yace "Are you still angry Baby?" Ita dai bata ce masa komai ba, ɗan murmushi yyi caressing her hand a hankali yace "I am sorry Baby, u know i love you" Mayraah ce ta fara ganin motar Maheer, Musharraf na sighting dinsa ya dau wayarsa ya kirasa yace yayi parking kawai, juyawa yayi yana kallonta yace "I told him kina school, and i met u here...." Ta dauke idonta zuwa daya side din, yace "Za ki shigo school gobe?" Juyawa tayi ta kallesa, ta marairaice tace "Are you coming?" Yace "Sure" Tace "Ohk" ganin Maheer yayi parking Musharraf ya sauka daga motarsa, Maheer ya karaso ya basa hannu suka gaisa, ita dai Mayraah taki sauka daga cikin motar, Musharraf ya zaga ya bude mata motar yana kallonta, Tayi kokarin ganin hawayen dake taruwa idonta bai zubo ba ta sauko daga motar, Yoghurt din da ta bude ya dauka da ledan magungunanta ya mika mata, ta amsa ta sunkuyar da kanta cikin sanyin murya tace "Thank you" Musharraf ya kalli Maheer dake kallonsu, yayi feigning smile yace "I will be on my way Dr" Maheer yace "Thank you so much Dr Musharraf" Musharraf na kallon Mayraah yace "Take care of ur self" Daga haka ya zaga ya bude front seat ya shiga ya bar wajen, Maheer ya amshi ledan hannunta da drink yana kallonta yace "Mu je" bata yarda ta kallesa ba ta nufi motarsa tana share hawayen dake sakko mata, back seat ta bude ta shiga, ya shiga motar suka bar wajen, har suka yi nisa Maheer ya rasa me zai ce mata, ita dai sai goge hawayenta take da hijab din jikinta..... Mamaki ne ya cika Mayraah ganin inda ya kawota, bayan yayi parking a compound din gidan ya sakko ya bude mata side dinta yana kallonta, tayi karfin halin cewa "But me yasa zaka kawo ni nan yaya?" Yace "Nobody is at home" Shiru tayi ta kasa cewa komai, She knows he isn't saying the truth, lkci daya maganganun Hajja na dazu da safe ya fara dawo mata, to dama ta yaya Ammi zata zabeta akan Mahaifiyarta, shikenan Hajja ta rabata da Amminta kenan, shkkn bazata sake zama gidan da ta taso take tunanin gidan iyayen da suka haifeta ne ba, ta kalli Maheer dake kallonta shi ma ya kasa cewa komai don yasan ma tunanin da take, lkci daya duk jikinsa yayi sanyi, cikin rawan murya tana girgiza masa kai tace "Yaya bazan iya zama da Aunty Haseenah ba, kai ma kasan bata so na, ko in nemi favor wajen Hamidah in zauna gidansu har in gama exams?" Maheer ya kamo hannunta ya sakko da ita daga motar yace "Haseenah bata isa ta zama obstacle na zamanki a gidana ba Mimi, it's my house not her's, kuma dolenta ta zauna dake in dai tana son zama da ni" Mayraah ta fashe da kuka don yanzu kuma ganin abubuwan take kamar a mafarki, ta yaya ma za ace Ammi da Abba ba su ne suka haifeta ba, anya ba mafarki ma take ba tukun, why will they even say Ammi and Abba are not her parents, or are they pranking her?? Maheer ya kasa ci gaba da jure kukan nata ya rungumeta yana jin kukan nata har ciki ransa yace "Plss stop this Mimi...." Sai da tayi kukanta me isanta sannan ya dago kanta yana kallonta, he is just short of words, ya ma rasa wani kalma zai yi amfani da shi wajen rarrashinta, can dai yayi karfin halin cewa "Kiyi hakuri Mimi, we all never bargained for this...." Kai Kawai ta gyada masa, ya share mata idonta sannan ya kama hannunta suka shiga cikin gidan, ko parlor bai tsaya da ita ba ya tafi da ita dakin da yayi mata furnishing duk a yau, hatta kayanta ya kwaso mata daga can gidan with the help of Usman, Mayraah ta karasa cikin dakin ta zauna gefen gado tana goge idonta, duk ta ma gaji da kukan she's exhausted with crying, durkusawa yayi gabanta yace "Me zan siyo maki ki ci Mimi?" Tayi shiru tana kallonsa ko kiftawa babu, yace "Anything?" Ta gyada masa kai kawai, mikewa yayi yace "Toh kiyi wanka kiyi alwala kiyi sallah, i will be right back" Bata san sanda tace "Are you leaving me all alone with her?" Maheer ya girgiza kai yace "Ae bata nan, kuma ko tana nan babu abinda zai faru" Daga haka ya mike ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita.... Tun safe sai yanzu hankalin Maheer ya kwanta, don ko da suka fara waya da Musharraf ya sanar masa suna tare da Mayraah bai samu rest of mind ba har sai da ya ganta, yana driving zuwa inda zai samo mata abinci kiran Usman ya shigo wayarsa.... Mayraah ta gaji da zama ta mike a hankali tana kallon akwatunan kayanta dake dakin, bathroom ta shiga taga duk wani abu da zata bukata yana cikin bandakin, tayi wanka tayi alwala sannan ta fito daga bandakin, akwati daya ta bude ta ciro wani kayan da zata sa da hijab, sannan tayi sallan Isha.... Maheer na dawowa gida bayan yayi parking a parking lot wayarsa ya fara ringing, yana dubawa yaga Haseenah ce ke kiransa tun dazu take kiransa yaki dagawa, yayi ta kallon wayar daga karshe ya daga ya kai kunne, tun ranan da ya kai ta gida sai yau ya daga kiranta duk da kusan kullum sai ta kirasa yafi sau goma amma baya dagawa, daga daya bangaren Haseenah ta fashe da kuka cikin tashin hankali tace "Maheer yanzu zuwa gidanmu kayi ka tona min asiri akan abinda ni nasan ban taɓa aikatawa ba a rayuwata ta duniya? Maheer me kaje kace ma iyayena da suke ta kirana haka tun safe?" Maheer dake sauraronta yace "Haseenah dama da na ajiye ki kofar gidanku nace ki tafi wani waje daban ne?" Cikin kuka tace "Ta yaya kake tunanin zan iya shiga gida Maheer? Me zance masu idan na shiga? Did u even know who my mum is??" Maheer yace "Ina kika tafi?" Ta marairaice tace "I was confuse kawai na tafi gidan kawata, idan na shiga gida ban san me zan ce masu ba" Maheer yace "Bani address din gidan kawar taki in zo yanzu" Ta zaro ido gabanta na faduwa sosai, da sauri ta kauda zancen tana shesshekan kuka tace "Maheer ka gaya min me kaje kace ma iyayena ko hankalina zai kwanta? Wllh na kasa sukuni tun dazu, gashi na ki daga kiransu, what did u say to them?" Yace "Ohk, zuwa nayi nace masu ina neman alfarman su sanar maki kanwata Mayraah zata dawo gidana da zama saboda final exams dinta.... Na maki magana kin nuna ke baki amince ba, don haka shi yasa na zo har gida na sanar masu su da suka isa da ke, domin akan haka za mu iya samun issues a zaman aurenmu da ke wanda bai kamata ba, don kuwa yanxu haka bakya gidana" Shiru Haseenah tayi tana sauraronsa da mugun mamaki trying to understand what he is trying to say, can dai tace "Ban gane Mayraah zata dawo gidanka ba Maheer? Wace Mayraah din? Da can daga gidanka Mayraah ke zuwa makaranta?" Yace "Look Haseenah, i am not forcing you to stay under same roof with Mayraah, kawai dai nasan ke zan iya canza ki at anytime amma ita bazan iya canzata ba tunda jinina ce ita, kuma in har kina so na da gaske dole ki so jinina, don haka ni ba da gadara nake ce maki Mayraah zata dawo gidana ba, Aa alfarma nake nema a wajenki kanwata ta dawo gidana for sometimes don zata fara final exams dinta, in kuma kina ganin baza ki iya ba to bana jin zan iya ci gaba da rayuwa da warce bata son jinina, it's now left for u to decide, though it's request not command...." Haseenah da taji zuciyarta na tafarfasa amma tunda dai neman hanyan komawa dakinta take asirinta a rufe, ta dake tace "Atohh tunda ba kaina zata zauna ba ina ruwana da ita Maheer, ba fa kaina zata zauna ba" Yace "Glad u reason dat..." Ita dai tayi shiru tunani iri iri na yawo a ranta, Maheer yace "Kina ina in zo in dauke ki yanzu?" Tace "Gaskiya ban shirya ba, sai dai gobe" Yace "Allah ya kai mu"
Chapter 77 · 0% Book details