← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 313

Sashe 1

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 9 min read

[5/26, 4:11 PM] Khaleesat Haiydar💖: *If you should come across this post plss say a prayer for my late Father, Allah Ubangiji ya ji ƙan sa ya gafarta masa da duk musulman da suka riga mu gidan gaskiya, Allah ya sa mutuwa hutu ce a garesu, Allah ya yafe masu kurakuransu, Allah ya sa idan tamu ta zo mu cika da imani...*😓

*Greetings to my Lovely Mom, continue being the strong woman you are now and always, Allah Ubangiji ya iya maki Maman Papi*💖

_Here is MAYRAAH lovely fans, i assure u it's gonna be a whole banger, shey you trust my pen_

Bani da intention din fara rubutu a wannan watan, Cause i had july in mind, but the pressure from my lovely fans is something else day by day, so let enjoy ourselves and refresh our brain with Mayraah...

💖💖 _MAYRAAH_💖💖

By _Khaleesat Haiydar_📚✍🏻

"Maheer ga wannan ka ajiye a account dinka...." Cewar Alhaji Mahmud kenan yana mika ma matashin dake zaune parlon bundle din kudin dake hannunsa, Maheer ya mike ya karasa ya amshi kudin daga hannun mahaifinsa yana jujjuyawa ya koma ya zauna, sai kuma ya ɗan sosa keya yana murmurshi yace "Toh Allah ya sa kar in hada da su wajen tawa hidimar" Hajiya Hajarah ta girgiza kai tana ɗan murmushi cikin sanyayyen muryarta tace "To ai kun fi kusa da ita...." Alhaji Mahmud na kallon budurwar dake zaune kasan carpet warce bazata wuce shekara ashirin da biyu ba yace "Allah Ubangiji ya sanya alkhairi My Daughter" Ita dai kanta na kasa tana wasa da gefen karamin mayafin dake kanta bata ce komai ba, Hajiya Hajarah tace "Toh tashi ki tafi ki kwanta...." Sai a sannan ta dago manyan idonta tana kallon iyayen nata tace "Sai da safe" Alhaji Mahmud da Hajiya Hajarah suka amsa tare wajen cewa "Allah ya tashe mu lafiya" ta kalli sauran yayyinta maza dake babban parlon su ma tayi masu sai da safe daga haka ta mike ta nufi kofa ta fita daga parlon, Hajiya Hajarah ta sauke ajiyar zuciya, a hankali tace "Alhamdulillah, Allah Ubangiji ya nuna mana wannan lokaci lafiya, Allah ya rufa mana asiri, ya hore mana ta yanda bama tunani..." Cike da mamaki Maheer ke kallonta amma dai bai ce komai ba, Tayi murmushi tana kallonsa don ta gane nufinsa, tace "To kai wa ke ta kai zan aurar da auta and only daughter" Alhaji Mahmud yace "Rana daya aka sa da naka ai bawan Allah" Maheer was a bit surprise yace "Ohh ai ban sani ba, to Allah ya kai mu da rai da lafiya" Usman da Umar dake zaune parlon suka amsa da "Ameen ya Allah" Mikewa Maheer yayi, yayi ma parent din nasa sai da safe ya tafi sama, sauran kannensa duk suka bi bayansa, Umar ya shige Bedroom dinsa dake nan downstairs... Tana tsaye walk way da zai yi leading zuwa Bedroom ta jingina da bango, Maheer ya karaso yana kallonta ganin hawaye idonta da mamaki yace "What happened?" Kamar jira take ta fashe da kuka ta durkushe nan kasa, Usman ya karaso wajen yana kallonta yace "Me ya faru?" Cikin rawar murya take kallonsa tace "To ni yanzu aure za a min er yarinya da ni yaya?" Usman ya bi gefen Maheer yayi wucewarsa dakinsa, Maheer ya duka yana facing dinta yace "Wa yace maki aure za a maki, hutu kawai za ki je na ɗan lokaci ki dawo, ai we can't do without ur food in this house" Ta fara goge hawayenta a hankali tana kallonsa, Maheer na murmushi yace "Toh amma dai naga ke kika kawo mana mutumin nan gidan nan ba wani ya kawosa ba ko?" Ta kalli kudin hannunsa sai kuma ta mike tace "To amma dai ka bani kudin nan in sa a account dina kar kaje ka kashe min, i don't trust you with money...." Buda baki yayi yana kallonta da mamaki, da sauri ta bar wajen tana dariya, ya gyada kai yayi hanyar dakinsa..... Ta gama shirin kwanciya kenan wayarta dake gaban mirror dinta ya fara ring, karasawa tayi ta dauka tana kallon screen din, ganin me kiranta tayi picking ta kai kunne tare da sallama can ciki, cikin cool voice dinsa ya amsa, a hankali tace "Good evening sir...." Calmly yace "Evening Mayraah" kamar yana ganinta ta sunkuyar da kai don sai da gabanta ya fadi jin yanda ya kira sunanta, yace "Are you done with ur Defense slide?" Tace "A'a ina son ka fara duba min ne sai in ci gaba" yace "Ohk, that is thoughtful of you...." Shiru duk suka yi, bayan few seconds yace "Ya su Ammi?" Tace "Suna nan lafiya" Yace "Maa sha Allah, zan yi tafiya gobe, so zan kwanta da wuri, ko akwai maganar da za ki min" ta girgiza kai a hankali tace "Aa... Allah ya tashe mu lafiya" Yace "Ameen, good night" Daga haka ya katse wayar, ta kalli screen din nata wayar, tabdii... wato nufinsa ita zata fara masa maganar kudin da aka kawo shi bazai mata ba, ta langwabar da kai ta ajiye wayar tayi addu'a ta shige cikin duvet ta kwanta. Washegari da safe karfe takwas Mayraah ta shigo parlor, Ya Usman ne kadai zaune dining area yana breakfast, ta karasa tana tsaye bayan daya daga kujerun dinning din ta gaishesa, yayi mata kallo daya ya amsa yace "How was ur night?" Tace "Alhamdulillah" Shiru duk suka yi, yana ci gaba da shan shayin gabansa, can tace "Me yasa naga kake breakfast da wuri bayan ba kotu zaka ba yau" Ba tare da ya kalleta ba yace "Zan yi tafiya ne" Ta gyada kai, a hankali tace "You look cute" Ya daga ido ya kalleta babu yabo babu fallasa, ta wara masa ido tace "Yes" Ammi ce ta fito daga kitchen ganin Mayraah tsaye dining area tace "Baki da lectures ne yau Mayraah?" Mayraah tace "Ai yau asabar Ammi" Tana fadin haka ta zauna daya daga kujeran dining din tana kallon Usman tace "Yaya can i join you?" Ya matsar mata da flask din kusa da shi zuwa gabanta da kayan shayin, Kafin karfe sha daya na safiyar ranan makota suka dinga tururuwan shigowa gidan yi ma Ammi Allah ya sanya alkhairin an kawo kudin auren Only and last daughter dinta.... Duk da arzki irin na Alhaji Mahmud bai yarda yayi nesa da anguwan da aka haifesa ba, don bayan haifarsa da aka yi a nan, nan din dai kuma ya fara rayuwa da Ammi bayan sun yi aure duk da locality din anguwan don duk yaku bayi irinsa ne dwellers din area din, a nan anguwan Allah yayi ma iyayensa rasuwa Mayraah na da shekara biyu, wanda kusan samun Mayraah ne ya bude ma Alhaji Mahmud kofofin arzkinsa bayan wani bulaguro da suka yi zuwa Yola garinsu Ammi sakamakon yanayi na rayuwa gashi babu me taimako kowa na fama da kansa, a lokacin Maheer is just 10 years Usman kuma 8, Ammi na goyon Umar that was almost 3 years sannan, basu tafi da yaran ba gudun kada suje su sha wahala a yola tunda babu takamaiman abun yi, Aka bar Maheer wajen Mahaifiyar Alhaji Mahmud a sannan da ranta, Usman kuma wajen Hajja Mahaifiyar Ammi warce ita ma ke garin kano, suka tafi da Umar kawai, watansu goma a Yola kwatsam sai ga Mayraah, daga nan kuma wani ikon Allah cikin kankanin lokaci kasuwancin da Alhaji Mahmud ke yi na kai kaya kasar Cameroon ya fara bunkasa kamar wasa, kan kace me ya zama millionaire a yan watanni kadan... Shekaran Mayraah biyu suka sake dawowa garin kano don zuwa sannan Naira ta zauna sosai, A nan kano cikin unguwan da aka haifi Alhaji Mahmud ya gina dankareren gidansa da na iyayensa, wanda kaf area din babu gidan da ya kama kafar tasa, a ko da yaushe zaka tarar da almajirai, yara, maza har da mata masu deban ruwa don famfo kusan biyar Alhaji Mahmud yayi a kofar gidan don kowa da kowa su amfana tunda ana wahalan ruwa sosai a area din, ga sadaka da yake yi duk ranan laraba da Juma'a, wannan dalili yasa kofar gidan baya rabo da jama'a a ko da yaushe, Mayraah na da shekara 6 kakanninta na wajen uba duk suka rasu a shekara daya. Mayraah na kitchen tana wanke utensils da aka yi amfani da su wajen yin breakfast ta jiyo wato makociyarsu Maman Shafa tana cewa "Ikon Allah, sati biyar aka sa kenan, ki ce dai rana daya da na Maheer...." Ammi tace "Ehh hadawa kawai aka yi ayi taron lokaci daya" Maman Shafa tace "Kai abu yayi kyau wllh, to Allah Ubangiji ya sa ayi da mu, Allah ya kai mu lokacin lafiya..." Ammi tace "Ameen Ya Allah" A sanyaye Mayraah ke wanke wanken don ita bata san date din da aka sa ba banda yanzu da take ji a bakin Maman Shafa, haka kawai taji dama a fasa auren nata yanzu a bar shi next year ko upper year, by then she will be 23. Bayan ta gama wanke wanken ta tafi dakinta, kwanciya tayi gefen gado ta rasa me ke mata dadi. Bayan magrib duk suna dinning da Abba da Ammi sai Ya Usman da Umar suna cin abinci, Maheer ne kawai baya nan, Ammi na kallon Mayraah dake ta juya abincin gabanta ganin ta ki ci, tace "Meye haka kike yi da abincin nan Mimi?" Mayraah ta daga kai ta kalleta, Abba ya maida attention dinsa kanta shi ma, Mayraah ta ɗan yi murmushi a hankali tace "Ammi kinsan dazu da yamma na ci abinci, kawai na ji yanzu bana jin yunwa" Ammi tace "Toh idan baza ki ci ba ki rufe za a ba almajirai" Mayraah ta dau wani plate ta rufe abincin ta mike ta bar dinning area din tana tafiya a hankali, dakin Yaya Maheer ta nufa, ta samesa kwance yana waya da fiancee dinsa, Mayraah ta zauna saman wani single chair dake dakin tana kallonsa, ya mike zaune yace "I will call u back dear" bayan ya katse wayar ya kalleta yace "Ya aka yi?" Ta sauke idonta daga kallonsa, a hankali tace "Yaya na ji kamar bana son inyi auren kuma" Lokaci daya hawaye ya kawo idonta ta ci gaba tace "Sai gabana yayi ta faduwa, may be ba yanzu ya kamata inyi auren ba, i am still little...." Yace "Addu'a za kiyi ta yi, it's always like that Mimi, fargaban barin su Ammi kawai kike, but this is the right time da ya kamata kiyi aure, u are in ur final year in school" Ta kallesa cikin rawan murya tace "Toh ni dai kawai a bar ni in fara gama karatun gaba daya since i am almost done" Maheer ya kalli wayarsa da ya fara ring yace "Mayraah, za mu yi magana gobe kin ga waya nake" Mikewa tayi a hankali ta nufi kofa ta fita daga dakin... Bayan ta gama shirin kwanciya wajen karfe tara na dare wayarta ya fara ring ta jawo wayar tana kallo, sai kuma ta daga ta kai kunne tayi shiru, sallama yayi mata ta amsa tace "Ina yini" Yace "I told you i was traveling today, but u chose not to call all through..." Zaro ido tayi, sai kuma ta marairaice tace "Kayi hakuri sir, na manta ne...." Yace "To kinyi kokari!"
Chapter 1 · 0% Book details