Sashe 145
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
da kansa ya kirani tun jiya da daddare, shine naga kema ya kamata kije ki dubota idan ya so sai ki bar ni a can kawai ki dawo gida, babu wanda dae zai ce baki je ba, yace yan uwanta kawai ke zuwa dubata kuma hakan ba dadi, ki tashi kawai mu wuce ban sallami me adaidaita sahun ba yana jiranmu" Hajja tace "Subhanallahi, to yanzu asibitin da aka kwantar da ita za mu je kenan?" Mama Ladi tace "Aa yace a nan gida aka sa mata ruwa, ni dama ba sanin gidan nayi ba ke kwanaki naji kina cewa za ki gane gidan, Hajja lokaci na ta wucewa kada yaga kamar ban damu da damuwarsa ba ki tashi mu je don Allah tunda tun jiya ya kirani ya sanar min" Hajja tace "To bari in tashi, to ko laulayi take Haseenar?" Mama Ladi tace "Ni ma nafi tunanin hakan gaskiya" Haka nan Mama Ladi ta ja Hajja suka kama hanyar gidan Maheer a daidaita sahu, Mama Ladi sai girgiza kafa take a adaidaita sahun, abu biyu yasa ta zo ta tafi da Hajja, na farko so take duk tonan sili da zata tayi ma Haseenah a gidan da turaren da zata kunna ace a gaban Hajja za ayi komai taji yanda Haseenah zata tona ma kanta asiri da kanta, na biyu kuma dama ita bata san gidan ba dole sae ta samu mai kai ta wannan yasa ta zo ta tattago Hajja ta lafta mata karya wai Haseenah ba lafiya inji Mashir, Hajja ta kalli Mama Ladi tace "Duk na samu labarin abinda Mamuda yayi Ladi, ke kuma don baki da zuciya baki san inda ke maki ciwo ba kin je kin sake mike kafa a gidansa kin zauna, to in na isa dake Ladi daga gidan Maheer gida za mu komo tare baza ki sake komawa gidan Mamuda ba, sannan zaman da Ammi take yi yanzu haka a gidan bai san albarkacina bane don da ba don ni din ba da tun a jiya Ammin bazata kwana gidansa ba ni nayi mata magana ta waya, dama can yana da niyyar aurensa ya fake da wannan matsala amma babu komai, jiya na hana idona bacci ina me yi ma Ammi addu'an Allah yayi mata abinda yafi alkhairi a rayuwarta kuma Allah ya saka mata wannan zalunci da Mamuda yayi mata cikin gaggawa, kuma albarkacin wannan hawayen nawa da na zubar wllhi Ammi zata ga sakayyan abin nan da Mamuda yayi mata babu dadewa, ita kuma Mayraah idan har mu muka cuceta Allah ya saka mata duniya da lahira, idan kuwa ita ce ta cuce mu ta rikita mana zuri'ar ta lalata zumuncin mu to Allah Ubangiji ya saka mana cikin gaggawa wallahi, da Ammi tasan ta dalilinta Mamuda zai mata wannan walakancin wataran me zai kai ta rikonta? Ai sanin gaibu sai Allah" Mama Ladi dai ko kallon Hajja bata yi ba balle ta bata amsa, Allah Allah kawai take taga sun isa gidan Maheer. Haseenah ta fito daga dakinta kamar mahaukaciya tana bubbuga kofar dakin Badiyyah, Badiyyah dake bacci ta tashi da sauri ta bude kofar da mamaki tace "Waye haka?" Haseenah na huci tace "Badiyyah kin san ni, na sanki, tun wuri kada ma third party ya jiyo mu ki fiddo min atamfofina set bakwai da lace uku da shadda daya da mayafi kala uku, da jaka da takalmin su ma set biyu da kika dauka a cikin akwatin lefena, daga ni sai ke a gidan nan sannan kin san nafi kowa sanin halin ki ciki da bai, kin zata duk ban san kan kayana bane zaki min wannan gagarumin satar?? To wallahi shiga ki fito min da kayana kada in maki abinda baki yi zato ba kuma baza ki taɓa mantawa a rayuwarki ba" Haseenah dake ta mata wani shegen kallo daga sama har kasa tace "Amma ke shashasha ce dabba wllhi, fataran kayan sa wa kika ga ina yi da zaki min sharrin na taɓa maki gantalallun kayan lefenki? In taba maki lefe inyi me da shi, ni za ki yi ma kazafi a gidan ɗan uwana?" Maheer ya bude kofarsa jin hayaniyar tasu ya tsaya nan bakin kofar yana kallonsu hannunsa rike da wayarsa, Haseenah ta nufesa tana huci tace "Maheer tun wuri kace ma barauniyar kanwarka ibilishiya mara tsoron Allah a zuciyarta ta fiddo min kayan lefe na da ta sata, in tana ma wasu sata tana kwana lafiya to ni wallahi bazata min ta kwana yau ba ka dai ji na rantse" Ko rufe baki bata yi ba Badiyyah ta sauke mata wani lafiyayyen mari tace "Don kaza kazanki ni kike ce ma barauniya?" Haseenah ta dafe kuncinta with shock tana kallon Badiyyah baki bude, Badiyyah na tafe hannu tace "Gwara dai ni kowa yasan ba zuwa gidan bokaye da malamai nake yi ba a Zaria, malamin nan naki..." Haseenah bata ba Badiyyah daman karasawa ba ta cakumota nan suka fara dambe a wajen suna kai ma juna duka iya karfinsu, Maheer dai na tsaye yana kallonsu bai ko motsa a inda yake ba, kawai ya juya ya koma dakinsa ya kulle, dai dai nan aka bude kofar parlon da sallama, Hajja da Mama Ladi suka yi tsaye bakin kofar bayan sun shigo jin hayaniya ya cika gida, Mama Ladi ce ta fara hangosu Haseenah dake zabga dambe ta gwalo ido tace "Innalillahi, menene zan gani haka?" da gudu ta nufesu Hajja ta zaro ido ita ma jikinta ya dau rawa ganin yanda Haseenah ta saka kan Badiyyah a hammata kamar zata kasheta tana duka, Hajja ta bi bayan Mama Ladi a gigice tana cewa "Innalillahi kar ta kasheta Ladi" Ihu Badiyyah take tana cewa "Wallahi yau sai na tona maki asiri a gidan, sai na fadi duk mugun abubuwan da kike yi, Mama Ladi wallahi boka da malamai take bi in ma kun ce in kai ku gidan malamin da take zuwa a zaria sai in kai ku har can, don ta kai ni wajensa wai nima yayi min aiki, Malamin har ce min yayi asiri take ma surkarta ya bata wani asirin ta kai dakin Ammi don ta raba Ammi da Mayraah yanzu haka asirin na nan a dakin har yanzu, kuma wallahi gold din akwatin Mayraah ma ita ta sa na sato na kawo mata har yau taki bani kuma taki bani kudin....." Haseenah duk ta gigice da maganganun da Badiyyah ke yi har hakan yasa ta fara loosing stamina, wanda wannan ya ba Badiyyah dama ta dinga hade kanta da bango da mugun karfi sai kace an aikota, kan kace me sai ga jini kamar an buda pampo, Mama Ladi da Hajja ihu suke a tare kamar rubabbu suna salati amma sun kasa matsawa kusa da su, Ciwo ba na wasa ba Badiyyah ta ji ma Haseenah a kai don kan kace me jini ya malale corridor din kamar an yanka rago, Haseenah ta fadi kasa wajen a sume, Badiyyah sai zare ido take ganin kamar kwakwalwan Haseenah fa take hangowa, ihun su Hajja ne ya fito da Maheer daga dakinsa, tuni Badiyyah ta shige daki a guje ta saka hijab dinta ta dau wayarta da handbag ta fice daga gidan da gudu.....