← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 163 OF 313

Sashe 163

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 1 min read

yayi shiru bai ce komai ba, Cikin lallami Mama Ladi tace "Nasan ka da hakuri da kauda kai Mamuda, kayi hakuri yanzu ka tafi sama ka duba halin da take ciki sai ka ga ta samu nutsuwa a ranta, babu bawan da ke wuce kaddararsa wllhi, babu tsimi fa babu dubara sai wannan abu ya faru Mamuda" Abba yace "Shikenan Mama, zan duba ta" Mama Ladi tace "Yauwa ko kai fa ɗan albarka, ai haka ake son babba ya gaya ma yaro magana ya ji, ni wallahi ka gama min komai wannan mutunta ni da kake yi" Mama Ladi tace "Yanzu sai ka tashi ka tafi sama ka dubata, ni kuma zan je kitchen in nemi abinda zan ci kar yunwa ta kasheni" Mikewa Abba yayi ya wuce sama zuwa bangaren Ammi.
Chapter 163 · 0% Book details