Sashe 116
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake.* [7/5, 9:45 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mayraah ta daga kai a hankali tana kallon wata Coursemate dinta da ta dafa shoulder dinta, Farida ta buda ido tace "Duk karatun ne haka Mayraah, have been talking to u since fa" Mayraah ta kirkiri murmushi ta ajiye handout din hannunta tace "Ayya ban sani ba Farida, ya kwana biyu?" Farida tace "Lafiya lau wllh, ya preparation din exams?" Mayraah tace "Alhamdulillah" project supervisor din su daya da Farida wato Dr Musharraf, dama su biyu kadai ne project student dinsa, Farida tace "Supervisor dinmu na kiranki, wani chapter kike yanzu ne? I submitted my chapter 4 just now" Mayraah tace "Ohk, ni ban yi submitting ba" Farida tace "Ohk yace ki je yana jiran ki" Mayraah tace "Toh" Tun barin Badiyyah wajen for almost an hour Mayraah ke zaune ita kadae a gun don kawayen Badiyyan ma tuni suka bar ta a wajen, bayan Mayraah ta maida handout dinta cikin jaka da wayarta da ta saka a Flight mode tun daxu, ta mike ta wuce sama bayan sun yi sallama da Farida don tace gida zata wuce. Office din Dr Musharraf Mayraah ta nufa, tana tsaye bakin kofa tayi knocking gently, sae da yayi mata permission din shiga sannan ta shiga ta kulle office din, shi kadae ne zaune office din amma ba kan office chair dinsa ba yana danne danne a laptop, ya daga kai yana kallonta, ita dai bata bari sun hada ido ba, kwalban coffee dake kan table dinsa kawai take kallo, ta isa har wajen table din ta tsaya kusa da kujeran dake facing din wanda yake zaune without looking at him tace "Good afternoon" Bai amsa ba ya cire glasses din idonsa yace "Na kira wayarki a kashe, so da ban ce a kiraki ba baxa ki shigo ba kenan, i think ko don saboda project dinki ma ai ba sai kin bari na kira ki ba" Shiru tayi taki cewa komai, Musharraf dai kallonta kawai yake, har sannan kuma bata bari sun hada ido da shi ba, bayan few seconds tace "Ana jirana, za mu tafi gida" Ganin bai bata amsa ba ta juya zata bar office din ya riko hijab dinta, bata san sanda ta warce ba ta juyo tana kallonsa da kyau tace "Kar ka sake pls" Ya mike yana kallonta yace "Are you okay?" Ta gyada masa kai furiously tace "I am very much okay, kawai nayi regretting relationship dina da kai ne tun daga farkonsa har yau, i just realized u are the reason i am going through all this, nayi da na sanin haduwata da kai...." Dr Musharraf ya koma ya zauna yana kallonta yace "Really?" Mayraah was trying so hard to control her self kar ta fashe da kukan dake cin ta tace "I regret everything...." A hankali Musharraf yace "I should be the one regretting Mayraah, ni aka yi ma damage so i should regret not you" Kallonsa kawai take zuciyarta na bugawa, can ta juya ta nufi kofa shi dai bai ce mata komai ba, har ta rike handle din kofar ta juya tana kallonsa with regret tace "I regret trusting you, i hate my self for believing in you har na kusa saɓa ma Allah, i will never forgive u for this...." Musharraf yayi kasa da murya yace "I don't understand, ni na sa kiyi saɓon Allah? How?" Hawaye cike idonta tace "Ae zuwa gidanka ma da abinda ka so yi min saɓon Allah ne" Yace "Na taɓa cewa ki zo gidana? Of course no, kawai ke kika ga ya kamata ki zo but ni ban taɓa ce maki ki zo ki sameni a gida ba...." Kallonsa kawai Mayraah take babu ko kiftawa, lokaci daya ta juya ta fice daga office din ta share hawayen idonta bayan haka kuma bata sake jin hawayen ya taho mata ba, ko minti daya bata kara a makarantar ba ta wuce hostel din da take, tana isa hostel din first abinda ta fara yi shine goge duk numbers din Dr Musharraf a wayarta bayan tayi blocking dinsa, ta shiga WhatsApp ma tayi blocking dinsa ta nan, kwanciya tayi gefen gado taji hawaye me zafi na sauka idonta kamar an bude pampo, kalmominsa na karshe ne kawai suka dinga kai komo a brain dinta, tayi da ta sanin zuwa ta samesa a gidansa, tayi mugun da na sani, she wish she neva did that, ta fashe da kuka sosai, tayi me isarta sannan ta mike ta dau wayarta ta shiga timetable din exams dinsu tana dubawa, don tun fitowar timetable din sau daya kadai ta duba, after checking the timetable ta fiddo complete handouts dinta ta jera su according to the timetable sannan ta shiga bandaki ta dauro alwala ta fito don an kira azahar. Karfe hudu da rabi Mayraah ta fito waje ta dalilin kiranta da Usman yayi, yana tsaye jikin motar ta karasa ta tsaya gefensa ta gaishesa, ya amsa yana kallonta yace "Ya kike?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Kina karatun sosai?" Ta daga kai ta kallesa tace "Ina yi" Ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "Zan yi tafiya gobe zan je wani aiki, so i don't know how long zan tsaya a can kafin in dawo...." Mayraah tace "Toh Allah ya tsare, i will be fine in sha Allah" Yace "Sure?" Ta ɗan yi murmushi tace "In sha Allah" Usman bai wuce 30 minutes ba ya wuce, Mayraah ta koma cikin hostel, har ranta dama taji bata ma son kowa ya dinga zuwa wajenta daga yanzu she just want to be left alone, and she is happy Usman is traveling tunda shi bazata iya gaya masa she wants to be left alone ba, Maheer kuma dama zata iya masa magana without any fear zata ce masa tana son ta dinga karatun ta without distraction..... Daren ranan Maheer ya zo, Mayraah ta gaya masa abinda ke ranta, bai iya ya ce mata komai ba at first, ita dai tana ta jiran abinda zai ce, bayan wani lokaci yace "Haka kike so Mimi?" Ta gyada masa kai tace "Yea, i want to concentrate fully, za mu dinga shiga school tare da Ummi from morning till evening don inyi karatu sosai" Maheer ya sauke ajiyar zuciya, yau kam yaji da confidence dinta take magana kamar ta samu motivation from somewhere, a hankali yace "Shikenan, if that is what u want Mimi...." Bata ce masa komai ba and she was expecting taga ya tashi ya tafi, can ya juya ya kalleta yace "Amma ai zan iya dinga zuwa sau daya in ganki?" Ta girgiza kai tace "Aa yaya, i said i can take care of my self, even Ummi that is in level 2 babu wanda yake zuwa nan dubata kullum, and i am not a kid" Maheer dai kallonta kawai yake, can ya ɗan yi murmushi yace "To shikenan, nasan zaki kula da kanki Mimi, today is Monday, in sha Allah Wednesday zan zo in ganki, hakan yayi ko?" Ta ɗan hade rai tace "Aa yaya, i said i can take care of my self, I am not a kid" Bai kuma ce mata komai ba, ita ma haka, a ranta kuwa ta kagu ya tashi ya tafi ta wuce ciki abunta, she just hate the sight of everyone har cikin ranta, bayan few minutes yace "Shikenan zan tafi, i will be calling u Mimi" Tace "Thank you" Daga haka ta mike ta shige cikin hostel din ya bi ta da kallo.... Har ya koma gida jikinsa a sanyaye yake, kullum addu'ansa Allah ya kawo karshen wannan abun ko zai samu rest of mind, a kofar gida yayi parking don yana son zai je wajen Ammi bayan magrib, yana shiga cikin gidan ya zauna parlor, kamshin girki ne ya cika gidan alamar ana girki a kitchen, can dai ya mike ya nufi corridor, dai dai nan Badiyyah ta fito daga dakin Haseenah kusan a guje rike da turmin atamfa uku ta cusa a cikin leda, sosai ta tsorata ganinsa ta koma gefe tana gwale ido sai rufe bakin ledan take kar ya ga meye a ciki, da kamar bazai ce mata komai ba sai kuma yace "Kin dawo" Tana kame kame tace "Eh, dama, eh dama yanzun nan nima na dawo, ajiya na bata shine na dauko yanzu" Yace "Ohk" Daga haka ya bude dakinsa da yake kullewa da makulli ya shiga ya rufe, Badiyyah tayi saurin shigewa dakin da take ta bude jakarta ta saka turamen atamfar ta kulle jakar, ta zauna gefen gado tana sauke ajiyar zuciya. Haseenah ta gama tuwo da miyar vegetable da take ta juye komai a cooler ta fito daga kitchen din, zaune taga Badiyyah a parlor, ko sanin Badiyyar ta dawo bata yi ba don tun karfe uku take kitchen kamar me girka abincin mutane goma, sai yanzu biyar da rabi ta fito, Haseenah ta dake tace "Aa kin dawo ashe" Tun da Badiyyah tayi mata maganar kudin gold few days back ta ɗan fara sake mata sama sama tana kauda kai a abubuwa da yawa sai dai ita kadai tasan plan din da suka yi ma Badiyyah ita da Cousin sister dinta Ramlah, Badiyyah na tauna chewing gum tace "Yanzun nan na shigo ae ko daki ban karasa ba" Haseenah tace "Ko zaki dafa Indomie don tuwo ne malmala biyu ya sa in masa, nasan ke baki cin tuwo" Badiyyah ta hade rai tace "Ni nasan yanda ake wani dafa Indomie, kuma yaushe nace maki bana cin tuwo" Haseenah tayi wucewarta ta bar ta a wajen, bata so Badiyya ta dawo gidan bata gama girki ba, so tayi ace kafin ta dawo ta gama tayi maza ta shige daki da shi ai dai bazata ce tayi girki ta hanata ba, duk saurin da take wai ashe har Badiyyar ta dawo.... Haseenah tayi wanka sharp sharp ta fito daga dakinta wajen karfe shidda,