Sashe 255
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ceo ta karaso kusa da gadon tana kallon Mayraah tace "Akwai advancement Aliyu?" MD ya gyada kai da sauri yace "She just moved her head now, shine nake duba oxygen saturation level...." Ceo ta ɗan yi murmushi tace "Glory be to God, this is what we've been waiting for, ka je office dina ka sanar ma Dr George...." MD yace "Ohk Ma'am" Juyawa yayi da sauri ya fita daga Unit din, Ceo ta dinga kallon Mayraah babu ko kiftawa, bayan few seconds ta sauke ajiyar zuciya ta juya ta kalli kofar ICU din sannan ta karasa kusa da ita ta kamo hannunta a hankali tace "Mary Ann, can you hear me?" Pecking hannunta dake ta kamshin turaren MD tayi tace "Quickest recovery dear" MD na fitowa Unit din Maheer ya mike yana kallonsa yace "Doctor is there any progress now? Zuwa yanzu ya kamata a samu wani progress" MD na kallonsa yace "Sure there is, in sha Allah" Daga haka ya bar wajen Maheer ya bi sa da kallo. Ceo na tsaye kan Mayraah har MD ya dawo tare da Dr George, sannan ta juya ta fita daga Unit din. Bayan isha Dr George yayi decreasing degree na ventilator support din so as she won't be depending fully on the machine, MD da Dr Khalil dai na tsaye suna kallon baturen, har ya gama ya fita after checking her for the last time, Dr Khalil ya kalli MD yace "Kai baka jin yunwa ne tun jiya bawan Allah?" MD ya shafa kansa a hankali yace "I took tea da safe ko ka manta" Bai jira cewar Dr Khalil ba ya karasa kusa da Mayraah yana kallonta, can ya juya ya kalli Dr Khalil dake kallonsu, yace "I think da safe relatives dinta can come in one at a time to check on her..." Dr Khalil ya gyada kai yace "Haka ne, Allah ya kai mu goben, Allah kuma yasa kafin goben improvement din yafi haka...." Daga haka ya juya ya fita, MD ya bi sa da kallo, a hankali ya juya ya kalleta, sai kuma ya duka ya kamo hannunta yayi kasa da murya yace "Can you hear me Mayraah?" A hankali ta bude lumsassun idonta, he was astonished seeing her open her eyes, Bai san sanda yayi mata murmushi ba, murya can kasa yana massaging hannunta yace "You will get well sooner, you are already doing great, be strong...." Rufe ido ta sake yi, tun kafin magrib ta ke making different movement of discomfort as a result of the breathing tube and that's a very good sign of recovering slowly, amma duk bata bude ido ba sai a yanzu, murza hannunta ya sake yi therapeutically, ta bude ido a hankali, yayi kasa da murya yace "Can you hear me...." Kallonsa kawai take looking so pale and weak, ya sauke idonsa daga kallonta, bai sake ce mata komai ba ya mike ya nufi kofa, har a sannan Maheer na zaune bakin ICU, MD na kallonsa yace "You can check on her, speak to her" Mikewa Maheer yayi yace "Thank you Dr" MD ya bar wajen, Maheer ya shiga unit din, yana isa bakin gadon ya duka ya kamo hannunta a hankali yace "Mimi..." Bude ido tayi, Maheer couldn't believe that, ya kalli Ventilator Machine din da sauri ya ga an ma rage karfinsa, ya matsa dab da ita yace "Get well pls Mimi, we all miss you, i know you to be a strong baby gal, stay calm and relax... You will get better very soon, we love you Mimi" sweet words haka is also a sedative therapy dake improving mental and psychological well being na patient in ICU, it really helps patient to be relaxed and comforted, bin sa kawai Mayraah take da ido, yana massaging mata hannu gently yana kallonta giving her a warm smile yace "Be strong for me, ur Ammi, Abba and barrister..." Lumshe ido tayi, ya sauke ajiyar zuciya feeling so much relieve now. Karfe tara Usman ya shigo IC unit din tare da Dr Khalil, Dr Khalil na kallonsa yace "Speak calmly to her" daga haka ya juya ya fita, nurse daya ce zaune tana monitoring din Mayraah, Usman ya karasa kusa da gadon, idonta na lumshe, ya zauna kan kujeran dake kusa yana kallonta, kasa ce mata komai yayi ya sunkuyar da kansa, bayan few seconds ya riko hannunta ta bude ido, still bai iya yace mata komai ba yana rike da hannunta for almost 10 mins, sake dago kai yayi ya kalleta, yayi pecking hannunta ya lumshe ido da kyar ya iya cewa "Come back soon Mimi" Daga haka ya mike ya fita waje. Sha daya saura Dr Hamid ya shigo Unit din, da mamaki yake kallon nurse din dake kokarin canza ma Mayraah hospital gown dinta da blanket yace "Madam sau nawa za a canza gown din nan ne?" Nurse din zata basa amsa sai ga MD ya shigo, Dr Hamid ya duba abinda zai duba sannan ya juya ya fita, MD ya kalli nurse din yace "What are you waiting for?" Nurse din tace "Dr Hamid just came in to check on her, yanzu zan canza" Juyawa MD yayi ya fita. Washegari da safe Abba ya shiga ICU din tare da Maheer, sosai hankalin Abba ya kwanta ganin state din Mayraah, don yanzun ma ta bude ido duk tana kallonsu, Maheer dai ya duka gabanta yana rike da hannunta yayi mata murmushi yayi kasa da murya yace "Good morning Mimi" Kallonsa kawai take, mintinsu sha biyar suka fita, Abba ba kallon Maheer yace "To yaushe za su yi disconnecting abubuwan nan da suka sa mata?" Maheer yace "Ana jiran aga ko zata iya numfashi da kanta babu matsala sai a cire in sha Allah, nasan zuwa anjima kilan a cire tunda an rage karfin machine din sosai" Abba yace "Toh Alhamdulillah, mun gode ma Allah, nayi farin ciki da abinda wannan asibitin suka mana na nuna concern dinsu, ko nawa suka bukata a biya nasan they deserve it" Maheer yayi kasa da murya yace "Ammi zata iya shiga ta dubata ita ma?" Abba yace "A dai bari a cire abubuwan nan da aka sa mata tukunna" Maheer yace "Haka ne" Ceo ce ta shigo asibitin leaving her securities outside, MD da ya fita dauko mata laptop dinta da wasu abubuwa yana biye da ita a baya, tana ganin Abba maimakon ta wuce sama sai ta tsaya suka gaisa tace "Ka shiga ka dubata ko Alhaji...." Abba yace "Eh bamu dade da fitowa ba, na kuma ji dadin yanda muka sameta, jiki kam Alhamdulillah" Ceo tayi murmushi tace "Mun gode Allah" Daga haka ta wuce sama MD na biye da ita har zuwa office dinta, ya bude mata ta shiga sannan shi ma ya shiga ya kulle kofar ya kunna AC, ajiye handbag dinta tayi ta zauna tace "I left early yesterday, wani family issue ne ya taso shi ne naje nayi intervening, tun daga gidansu nayi niyyar kiran ka in baka samples din nan...." Tana fadin haka ta warware karamin towel din hannunta ta ajiye kananun bottles biyu dauke da blood samples kan table dinta, sai kananun ziploc nylon biyu each dauke da strand of hair tace "I need genetic testings on this, commence it immediately" MD ya dauka yace "Ohk Ma'am" zai fita tace "Yauwa ya jikin Mary Ann? Zuwa yaushe za ayi disconnecting dinta daga Machine din?" Da ladabi yace "Har yanzu numfashin isn't steady so we are still watching over it" Ceo ta sauke ajiyar zuciya tace "Idan na sha coffee zan sauko in duba ta yanzu" Yace "Ok Ma'am" Daga haka ya juya ya fita, duk da Abba bai so Ammi ta ga Mayraah ba sai an cire mata Ventilator Machine, amma saboda yanda ta mugun daga hankali haka likitocin suka saka a barta ta shiga kawai ta ganta, ai ko ranan kwana Ammi tayi kuka har da karin drip, don ita yanda taga an jojona mata wayoyi a jiki duk da idonta biyu tana kallon kowa gani take kamar fa babu sauki kwata kwata, in da sauki ai baza a makala mata wayoyi ba, haka nan aka ci gaba da kula da Mayraah a asibitin, a duk sanda Maheer ko Usman or Abba wani zai shiga wajen ta ya ganta babu hinderance, tunda Incident din nan ya faru MD ke zaman asibiti 24/7 don dama Bedroom babba garesa a office dinsa, Surkar Dr Khalil da inna da ita kanta Zainab duk sun zo asibitin duba Mayraah, duk da basu shiga ICU ba iyakarsu wajen Ammi. Aunty Mariya na kitchen yau ma kamar kullum tana dafa abincin da za a kai ma Ammi asibiti, kwanansu na shidda kenan a Abuja amma Abba yace ba sai sun je asibitin ba tukunna, hakan na damun Aunty Mariya amma bata masa musu ba duk suna gida sai dai tayi girki ita da Bilkisu Usman ko Maheer ya zo ya dauka ya kai asibiti, Mama Ladi ce ta shigo kitchen din tana yafa gyale tace "Sai na dawo Mariya" Aunty Mariya na kallonta tace "Ina kuma zaki Mama?" A fusace Mama Ladi tace "Ina kuwa zan je banda asibiti? Ko a kasashen waje ban taɓa jin inda aka ce baza a shiga asibiti a duba marasa lafiya ba in ba a tsinannen asibitin can ba, in haka ne meye amfanin zuwana? yau fa kusan kwana shidda mun tare a katon gidan nan sai dai mu ci abinci mu kwanta kamar wasu mayunwata" Aunty Mariya tace "Amma dai Alhajin da kansa yace ba sai mun je ba ka'idar asibitin kenan ko, kuma dazu da muka yi magana da shi yace ko zuwa jibi sai mu je" Mama Ladi tace "Amma ai katuwar matarsa Amina ita dai taje kuma an bar ta har ta shiga, tun da har nan ta zo ta mana jaje, naga ma ta kara narka wani uban kiba matar, kuma kwanan ta uku a garin nan yau, Shi kansa Umar da ya dawo shekaranjiya yayi sintirin zuwa asibitin ya fi a kirga kuma duk ana barin sa ya shiga, to sai mu ne za a raina ma wayo ace baza mu je asibiti ba? Ko dai wari muke ne?" Hajja dai ta tabe baki don ita ma hakan